Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Donald Trump zai yi kome a matsayin shugaban Amurka na 47

Wannan shafi na kawo muku rahotanni da bayanai kan zaɓen ƙasar Amurka da aka gudanar a ranar Talata 5 ga watan Nuwamban 2024.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Mohammed, Usman Minjibir, Umar Mikail, Ibrahim Muhammad da Abdullahi Bello Diginza, Rabiatu Kabir Runka

  1. Yanayi ya sauya a cibiyar jiran sakamakon zaɓe ta Harris

    Yayin da aka gabatar da sakamakon jiha guda daga cikin jihohi bakwai marasa tabbas, yanayi ya fara sauyawa a wajen harabar jima'ar Howard da ke birnin Washington DC.

    Bayan shafe sa'o'i masu yawa ana tiƙa rawa cikin murna da waƙe-waƙe, dubban magoya bayan da suka taru a cibiyar sun fara nuna damuwa.

    "Na sani akwai damuwa a yanzu," in ji Jordan Newsom wani ɗalibin jami'ar Howard, bayan bayyana sakamakon jihar North Carolina da ke nuna cewa Trump ne ke kan gaba.

    Amma Newsom ya ce 'yan'uwansa magoya bayan Harris za su yi duk abin da ya dace don maido wa kansu farin cikin da suke ciki.

    "Babban abin da ya kamata mu yi shi ne haɗa kanmu, cike da fatan nasara ga kawunanmu''.

  2. Hankali ya koma kan jihohi marasa tabbas

    Yayin da ake ci gaba da ƙidaya ƙuri'u a zaɓen shugaban Amurka, a yanzu hankali ya karkata kan jihohi marasa tabbas da za su iya tabatar da wanda ya yi nasara a zaɓen.

    Kawo yanzu dai Donald Trump na jam'iyyar Republican ne ke kan gaba da ƙuri'un wakilan masu zaɓe 230, yayin da Kamala Harris ke da 165.

    An dai bayyana sakamakon jihar North Carolina - wadda ke cikin jihohin bakwai - Inda kuma Donald Trump ya lashe ta.

  3. Labarai da dumi-dumi, Trump ya kama hanyar lashe jihar North Carolina

    Ɗan takarar Republican Donald Trump ya samu nasarar lashe jihar North Carolina.

    Jihar na cikin jihohi bakwai marasa tabbas a zaɓen ƙasar.

    North Carolina na da adadin ƙuri'un wakilan masu zaɓe 16.

    Yanzu saura jihohi shida cikin marasa tabbas domin sanin wnda ya lashe zaɓen ƙasar.

  4. An kammala zaɓe a duka jihohin in banda Hawaii da Alaska

    An kammala kaɗa ƙuri'a a duka jihohin Amurka, in banda Hawaii da Alaska.

    Fiye da rabin jihohin ƙasar sun sanar da sakamakonsu.

    Kawo yanzu sakamakon yana tafiya kamar yadda aka tsammata.

    Turmp ya ci duka jihohin da jam'iyyarsa ke da rinjaye, yayin da ita ma Harris ta lashe jihohin da Demokrats ke da rinjaye.

    Kawo yanzu babu jiha guda cikin marasa tabbas da aka sanar da sakamakonta.

    Jiya ta baya-bayan nan da ka kammala zaɓen ita ce jhar California - mai adadin ƙuri'un wakilan masu zaɓen 54 - wadda jam'iyyar Demokrats ta lashe

  5. Hotunan yadda wasu magoya baya ke jiran sakamakon zaɓe a jihar Minnesota

  6. Har yanzu Trump na kan gaba da tazara mai yawa

    Har yanzu sakamakon da ke fitowa daga jihohin daban-daban na Amurka, na nuna cewa ɗan takarar jam'iyyar Republican, Donald Trump na kan gaba da gagarumin rinjaye.

    Kawo yanzu Mista Trump ya da adadin ƙuri'un wakilanmasu zaɓe 172, yayin da abokiyar takararsa ta jam'iyyar Demokrats ke da 81.

    Ɗan takara na buƙatar samun adadin ƙuri'un wakilan masu zaɓe 270 ko fiye kafin ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.

  7. An rufe rumfunan zaɓe a jihohi fiye da 40

    An rufe rumbunan zaɓe daga jihohin Amurka fiye da 40 (haɗe da gundumar Columbia) daga cikin jihohin ƙasar 50.

    Nan ba da jimawa ba kuma za a samu sakamakon zaɓen wasu jihohin, to amma wasu jihohin za su ɗauki kwanaki suna ƙidaya ƙuri'unsu.

    Alal misali jihar Nevada, za a ɗauki kwanaki ana ƙidaya ƙuri'unta. Da dama an kaɗa ƙuri'un jihar ta hanyar saƙon Email, don haka za a ci gaba da ƙidaya ƙuri'u har zuwa ranar Asabar .

    Haka kuma jihar ba ta fitar da sakamakon ba, har sai an kammala ƙidaya ƙur'ar ƙarshe a zaɓen.

  8. Ana hasashen Trump ya ci Texas da ƙarin jihohi uku

    An kuma yin hasashen ɗan takarar jam'iyyar Repbilcan Donald Trump ya lashe zaɓen a jihar Texas mai ƙuri'un wakilan masu zaɓe 40, da wasu ƙarin jihohin uku.

    Sauran jihohin uku sun haɗa da Wyoming da South Dakota da kuma North Dakota, duka dai jihohin uku na da ƙuri'un wakilan masu zaɓe uku-uku.

  9. An hasashen Harris ta ci jihohin Rhode Island da New York da Illinois

    An hasashen 'yar takarar jam'iyyar Demokrats Kamala Harris ta ci jihohin Rhode Island da New York da kuma jihar illinois.

    Jihar New York - mai ɗimbin jama'a na da ƙuri'un wakilan masu zaɓe 28, yayin da Rhode Island ke da wakilan masu zaɓe huɗu.

    Ita kuwa jihar illinois na da wakilan masu zaɓe 19

  10. Hanyar samun ƙuri'un wakilan masu zaɓe 270: Ta yaya ɗan takara zai yi nasara?

    Akwai jihohi 50 a Amurkakuma mafi yawansu, suka zaɓi jam'iyya guda ne a kowane zaɓe. To amma akwai wasu jihohin masu muhimmanci, da ake yi wa laƙabi da ''marasa tabbas'', wanda kowane ɗan takarar zai iya lashe su.

    Jihohin sun haɗa da Nevada da Arizona da North Carolina da Georgia da Wisconsin da Michigan da kuma Pennsylvania.

    Jihohin da suke da yawan jama'a ne suka fi yawan adadin ƙuri'un masu zaɓe.

    A jimlace akwai ƙuri'un mazu zaɓe 538. Kuma duk wanda zai lashe zaɓen dole ne ya samu ƙuri'a 270 ko fiye.

    Kuma duka 'yan takarar na buƙatar yin nasara a jihohi marasa tabbas aƙalla uku domin samun nasara.

  11. Trump na kan gaba a sakamakon farko da aka fitar

    Sakamakon farko da aka fitar zuwa ya nuna cewa ɗan takarar jam'iyyar Republican, Donald Trump na kan gaba da tazara mai yawa kan abokiyar hamayyarsa, Kamala Harris ta Demokrats.

    Kawo yanzu Mista Trump ya samu ƙuri'un wakilan masu zaɓe 154, yayin da Harris ta samu 30.

    Sai dai komai na iya faruwa, saboda mafi yawan sakamakon da aka samu zuwa yanzu na jihohin da Republican ke da rinjaye ne.

    Dan takara na buƙatar ƙuri'un wakilan masu zaɓe 270 ko sama da haka kafin ya lashe zaɓen shugabancin Amurka.

  12. An samu hasashen ƙarin sakamakon wasu jihohin

    A yanzu mun ƙara samun hasashen ƙarin sakamakon wasu jihohin

    Jihohin da aka ƙiyasta Donald Trump zai lashe:

    • Florida
    • Alabama
    • Missouri
    • Oklahoma
    • Tennessee

    Kamala Harris za ta lashe :

    • District of Columbia
    • Maryland
    • Massachusetts

    Duka waɗanann dama ana sa ran haka, la'akari da tarihin zaben jihohin.

  13. An rufe rumfunan zaɓe a jihohi 16 cikin har da Pennsylvania

    An rufe mafi yawan rumfunan zaɓe a jihar Pennsylvania da wasu jihohi 16.

    Nan da sa'a guda ko fiye ana sa ran fara rufe gomman jihohi da suka haɗa da Wisconsin da Arizona da kuma Michigan.

    Muna sa ran samun sakamakon zaɓen jihohin da aka kammala kaɗa kuri'a.

    Da dama da cikin waɗannan jihohi wurare ne da jam'iyyun Republican da Demokrats suka saba ci, kuma suke da ƙarfi, kodayake an kammala zaben a ɗaya daga cikin jihohi marasa tabbas wato Georgia, wadda kuma muke sa rai da sakamakonta nan ba da jimawa ba.

    Haka kuma za mu fara samun sakamakon ƙuri'ar batun zubar da ciki a jihar Missouri, wadda idan an amince da dokar za ta bayar da damar zubar da ciki, har sai idan ɗan tayin zai iya rayuwa, saɓanin dokar haramci ta yanzu.

    Haka ma a jihar South Dakota, nan ba da jimawa ba za mu ji abin da masu zaɓe suke so kan batun zubar da ciki.

    A halin yanzu dai duka nau'in zubar da ciki haramun ne a jihar, har sai idan ya zama dole don ceto rayuwar uwar.

    Idan masu zaɓen sun amince da batun, to hakan zai soke dokar ta yanzu da ta haramta zubar da ciki.

  14. An rufe rumfuna a ƙarin jihohi uku ciki har da North Carolina

    An samu ƙarin jihohi uku da aka rufe rumfunan zaɓe da suka haɗa da Ohio da West Virginia da kuma North Carolina - wadda ke cikin jihohi masu muhimmanci.

    Tun da farko Donald Trump ya lashe jihohin Indiana da Kentucky, yayin da Kamala Harris ta lashe jihar Vermont.

    Wannan sakamako bai zo da mamaki ba, kasancewar dama waɗannan jihohi sun saba samar da irin wannan sakamako shekaru da dama da suka wuce

    To amma yanzu aka fara, kuma ana sa ran samun ƙarin sakamako nan ba da jimawa ba.

  15. An samu ƙarin barazanar bom a wuraren zaɓe a Georgia

    'Yansanda a gundumar DeKalb da ke jihar Georgia na gudanar da binciken bom rumfunan zaɓe bakwai.

    Gundumar DeKalb, babban yankin baƙaƙen fata ne da suka zaɓi Biden a 2020.

    Tuni dai aka tsawaita zaɓe a rumfuna biyar a gundumar Fulton - da baƙaƙen fata suka fi yawa, bayan da aka samu tsaikon zaɓe sakamakon barazanar samun bom.

    Tun da farko hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI da shugaban hukumar zaɓen jihar Georgia sun ce mafi yawan barazanar an same su ne daga ''saƙonnin ƙarya na Email da Rasha ta ƙirƙira''.

    An kuma samu irin wannan matsala a jihohin Michigan and Wisconsin.

    Wurare ƙalilan ne dai aka samu wannan matsalar, idan aka kwakwanta da yawan ƙasar, inda a sauran wurare zaɓen ya tafi kamar yadda ake buƙata.

  16. An rufe rumfunan zaɓe a wasu ƙarin jihohi ciki har da Georgia - wadda ke cikin marasa tabbas

    An rufe zaɓe a wasu ƙarin jihohi baya ga Kentucky da Indiana, da aka rufe tun ɗazu, a yanzu an rufe rumfunan zaɓen a jihohin South Carolina da Vermont da Virginia, da kuma jihar Georgia mai matuƙar muhimmanci.

    Georgia na ɗaya daga cikin jihohi bakwai da za su iya sauya sakamakon zaɓen.

  17. Hukumomin jihar Philadelphia sun yi watsi da iƙirarin Trump na samun 'gagarumin maguɗi'

    Donald Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta wato 'Truth Social' yana mai cewa ''Jami'an tsaro sun je'' jihar Philadelphia saboda abin da ya kira samun ''gagarumin magudi'' a can.

    A karo na farko da yake zargin samun maguɗin zaɓe a shafinsa na 'Truth Social' a yau, to sai dai bai yi cikakken bayanin hujjjoji kan ikƙirarin nasa ba.

    To sai dai rundunar 'yansandan jihar, sun shaida wa BBC cewa ba su da masaniya game da abin da Trump ɗin ke faɗi.

    Babban alƙalin gundumar Philadelphia, Larry Krasner ya wallafa martani game da wannan iƙirari, yana mai cewa ''babu wata hujja daga jami'an tsaro da ke tabbatar da zargin''.

    Wani kwamishina a jihar wanda ɗan jam'iyyar Republican ne a wallafa a shafinsa na X, cewa ''babu ƙanshin gaskiya kan wanann iƙirari. Zaɓe a jihar Philadelphia na gudanar cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali''.

  18. Labarai da dumi-dumi, An samu sakamakon farko na 'yan majalisar wakilai... a kujerun da babu hamayya

    Duk da cewa wurare ƙalilan ne aka rufe rumfunan zaɓen a jihohin Kentucky da Indiana, amma za mu iya cewa jam'iyyar Repblican ta lashe kujerun majalisar wakilai uku.

    Ta yaya muka gane sun yi nasara?

    'Yan majalisar na jihar Kentukcy - masu ci - Hal Rogers da Thomas Massie sun tsaya takarar ne ba tare da abokan hamayya ba a yankunan da jam'iyyar Republican ke da ƙarfin gaske, inda kuma tuni aka rufe rumfunan zaɓen yankunan.

    Haka shi ma Marlin Stutzman na gundumar a jihar Indiana, ya lashe zaɓen da kashi 61 cikin 100 na ƙuri'un daka kaɗa a gundumar.

  19. Magoya bayan Harris sun taru a wajen jami'ar Howard don bikin sauraron sakamako

    Magoya bayan Kamala Harris a birnin Washington DC, sun taru a wajen jami'ar Howard, inda 'yar takarar Dimokrats ɗin ta yi karatun digirinta, wanda kuma shi ne zai kasance babban ɗakin taron da za a gudanar da bikin jiran sakamakon zaɓenta.

    Daga cikin waɗanda suka halarci wurin har da Cheryl Taylor, wadda ita ma tsohuwar ɗalibar jami'ar Howard ce, wadda ta fara tallata wa Harris shiga ƙungiyar mata masu rajin kare baƙaƙen fata.

    A lokacin tana da shekara 19 Harris ta zama shugabar ƙungiyar, ''ta yi abin da ya kamata.' in ji Taylor, ''Kyakkyawa, mai fikira kuma mai kirki''.

    Taylor ta bayyana matakin Harris na gudanar da bikin a wurin, tana mai cewa an yi hakan ne saboda muhimmancin jami'ar a rayuwarta, a matsayin wurin ya ɗora ta a hanyar jagoranci, tare da ''nuna fikirarta''

  20. An shirya ɗakin taron da Trump zai jira sakamakon zaɓe

    Kafofin yaɗa labarai na shirya kyamarorinsu a babban ɗakin taron da Donald Trump zai gudanar da bikin sauraron sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.

    Tuni aka shirya wurin da zai yi jawabi ga magoya bayansa da kuma ƙasar baƙi ɗaya.

    An maƙala wani makaken ƙyalle ɗauke da rubutun ''Trump zai gyara ta'', wasu kalamai da ya yawaita amfani da su a wajen yaƙin neman zaɓensa.

    Ana ta gwada na'urorin sauti, sannan an girke manya-manyan magiji na manyan gidajen talbijin.

    Nan ba da jimawa ba manyan baƙin da aka gayyata za su halarci babban ɗakin taron domin kallon yadda ake tattara sakamakon tare da Mista Trump.

    A yanzu Trump zai ci abincin dare a Mar-a-Lago, sannan ya kasance da 'yan'uwa da abokai da manyan masu ba shi tallafi, kamar mamallakin shafin X, Elon Musk.