Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Donald Trump zai yi kome a matsayin shugaban Amurka na 47

Wannan shafi na kawo muku rahotanni da bayanai kan zaɓen ƙasar Amurka da aka gudanar a ranar Talata 5 ga watan Nuwamban 2024.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Mohammed, Usman Minjibir, Umar Mikail, Ibrahim Muhammad da Abdullahi Bello Diginza, Rabiatu Kabir Runka

  1. An buɗe rumfunan zaɓe a Alaska da Washington

    Yanzu haka karfe 07:32 na safe ne a Alaska, karfe 08:32 na safe ke nan a birnin Washington, wanda ke nufin yanzu an buɗe rumfunan zaɓe.

    Akwai ƙuri'un wakilan masu zaɓe uku a Alaska, wadda ita ce jiha mafi faɗin ƙasa a Amurka, kuma akwai ƙuri'u 12 a Washington.

    Hawaii - mai ƙuri'un wakilan masu zaɓe huɗu - ita ce jihar ta ƙarshe da ta buɗe rumfunan zaɓe da ƙarfe 7:00 na safe - ƙarfe 5:00 kenan agogon GMT.

  2. An tsawaita lokacin zaɓe a wasu sassan Pennsylvania

    Rahotanni daga masu kaɗa ƙuri'a a gundumar Cambria na bayyana cewa ana fuskantar tangarɗa da na'urar zaɓe.

    Wata mata mai suna Jessenia Anderson ta bayyana cewa na'urorin zaɓe ba su aiki, kuma ba a iya ɗaukar hoton masu kaɗa ƙuri'a.

    A wata sanarwa da hukumar zaɓe ta gundumar Cambria ta fitar, ta ce "lalacewar manhajoji" ta hana wasu masu kaɗa ƙuri'a tantance kuri'unsu.

    Sanarwar ta ƙara da cewa "wannan bai kamata ya kashe wa masu kaɗa ƙuri'a gwiwa ba wurin kaɗa ƙuri'unsu".

    Hukumar ta shigar da buƙata a kotu ta tsawaita lokacin kaɗa ƙuri'a a gundumar - wadda ke kusa da Pittsburgh.

    "Akwai abubuwan da aka tsara don al'amura makamantan haka," in ji mahukunta a gundumar. "Za a karɓi dukkan ƙuri'un da aka kaɗa, za a tantance kuma a kirga su."

  3. An buɗe rumfunan zaɓe a California da wasu jihohi huɗu

    An bude rumfunan zaɓe a jihohin California da Idaho da Nevada da kuma Oregon.

    Jihohin da suka rage su fara kaɗa ƙuri'a yanzu su ne Alaska da Hawaii.

    California tana da ƙuri'un wakilan masu zaɓe 54 - mafi yawa tsakanin jihohin Amurka - amma ana ɗaukar ta a matsayin jihar da jam'iyyar Democrat ke da tasiri, saboda lokaci na karshe da ta zabi ɗantakarar Republican shi ne a 1988.

    Nevada, wadda ke da ƙuri'un wakilan masu zaɓe shida, ita ce ta ƙarshe a cikin jihohi bakwai da ba su da tabbas da za a buɗe rumfunan zaɓe a yau.

    Don tunatarwa - jihohi suna ba da dukkan ƙuri'un wakilan masu zaɓensu ga duk wanda ya samu rinjayen ƙuri'un jihar.

    Misali, idan dantakara ya lashe kashi 50.1% cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a California, ana ba shi dukkan ƙuri'u 54 na jihar.

  4. Ana iya yin rajista da kuma kaɗa ƙuri'a a lokaci ɗaya

    Dokokin yin rajista sun sha bamban a kowace jiha ta Amurka, amma a mafi yawan jihohin har yanzu ana iya yin rajista a ranar zaɓe.

    Kusan rabin jihohin kan ba da damar mutum ya yi rajistar katin zaɓe kuma ya jefa ƙuri'a a lokaci guda - har a yankin District of Columbia.

    A sauran jihohin, tuni lokacin yin rajista ya wuce - ban da jihar North Dakota, wadda ba a buƙatar mutum ya yi rajistar ma gaba ɗaya.

  5. Mataimakin Trump ya kaɗa ƙuri'arsa

    Abokin takarar Donald Trump a jam'iyyar Republican, JD Vance, ya kaɗa ƙuri'arsa ba da jimawa ba da hannunsa a Cincinnati da ke jihar Ohia.

    An ga Vance yana isa rumfar zaɓen tare da matarsa da kuma 'ya'yansu.

  6. Kaɗa ƙuri'a da na'ura

    A wannan zaɓe, Amurkawa na da ikon kaɗa ƙuri'arsu ta na'ura - ma'ana ba sai mutum ya ɓata lokaci wajen cike-ciken takardar kaɗa ƙuri'a ba.

    Kamar yadda aka rubuta a jikin dandamalin na'urar: "Mai zaɓe kawai zai nuna wa allon na'urar ƙuri'arsa ne. Idan an karɓi ƙuri'ar tasa, hoton turar Amurka zai bayyana."

  7. Takardar kaɗa ƙuri'a da kuma yadda ake kaɗa ta a Amurka

    A Amurka, takardar kaɗa ƙuri'a na da tsayi - takan ƙunshi shafi biyu ko uku.

    Ba 'yantakarar shugaban ƙasa ne kawai a jikin ƙuri'ar ba, har da na 'yantakarar majalisar wakilai da ta dattawa, har ma da wasu tsare-tsaren gwamnati kamar kasafin kuɗi na yankuna.

    Idan aka je kaɗ ƙuri'a, mutum zai cike wata da'ira da aka zana a jikin takardar maimakon ɗiga alama a gefen abin da mutum yake so.

    Mutum kan ɗauki kusan minti 10 kafin ya iya kammala kaɗa ƙuri'ar saboda yawan abubuwan da ke jikin takardar.

  8. An buɗe rumfunan zaɓe a jihar Arkansas

    An buɗe rumfunan zaɓe a Arkansas, abin da ke nufin an fara jefa ƙuri'a a jihohin Amurka kusan 30 kenan a yau ɗin nan.

    Jihar na da ƙuri'un wakilan masu zaɓe (electoral college) shida - ba kamar California ba mai 54, da New York ba mai 28.

    Yawan jama'a kowace jiha ne ke fayyace yawan ƙuri'un wakilan masu zaɓen da take da shi.

    Tuni jihohi da dama suka buɗe rumfunan zaɓe, kamar Mississippi da North Dakota.

  9. Yadda zaɓe ke wakana a Amurka

    Ga waɗanda suka shigo shafin a yanzu, wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wainar da ake toyawa a zaɓen Amurka, inda Amurkawa suka fara kaɗa ƙuri'a domin zaɓan sabon shugaban ƙasarsu tsakanin Donald Trump da Kamala Harris.

    Zuwa yanzu dai an fara zaɓe a sama da rabin jihohin ƙasar, kuma an fara da zaɓen ne da misalin ƙarfe 11 a agogon Najeriya da Nijar.

    Akwai wasu jihohi guda bakwai da ake kira swing states, wato jihohi marasa tabbas, waɗanda a lokuta da dama, su ne suke sauya sakamakon zaɓen ƙasar.

    Ku ci gaba da kasancewa tare da mu.

  10. An fara zaɓe a wasu ƙarin jihohi

    Wasu ƙarin jihohin sun fara gudanar da zaɓe, ciki har da jihar Texas, wadda ita ma jiha ce mara tabbas.

    Jihohin da suka fara zaɓen da aka ƙara su ne:

    • Alabama
    • Iowa
    • Kansas
    • Minnesota
    • Mississippi
    • North Dakota
    • Oklahoma
    • South Dakota
    • Texas
    • Wisconsin - jiha mara tabbas mai wakilan zaɓe 10

    Zuwa yanzu dai an fara zaɓe a sama da rabin jihohin ƙasar guda 50.

    Ku ci gaba da kasancewa tare da mu.

  11. Jihohi bakwai da za su iya sauya sakamakon zaɓen shugaban Amurka

    Kimanin mutum miliyan 240 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a a zaɓen Amurka na 2024, amma kaɗan ne daga cikinsu ke iya tabbatar da wanda zai zama shugaban ƙasa.

    Masana sun yi amanna cewa akwai ƴan tsirarun jihohin da ake kira "swings state", wato jihohi marasa tabbas, domin kuwa kowa daga cikin 'yan takarar, Kamala Harris ta Democrats da Donald Trump na Republican.

    Waɗannan jihohi bakwai waɗanda su bakwai, - Arizona da Georgia da Michigan da Nevada da North Carolina da Pennsylvania da kuma Wisconsin - ana ganin kamar su ne ke riƙe da makullan fadar White House (Ofishin shugaban ƙasar Amurka).

    Don haka duka jami'iyyun biyu sun karkata kan farautar ƙuri’un mutane - da ba su yanke shawara kan wanda za su zaɓa ba - a waɗannan jihohin.

    Ga bayanan jihohin da adadin al'umominsu, da adadin ƙuri'un wakilan masu zaɓe (Electoral college) da kowace jiha ke da shi, da kuma mutumin da ya lashe zaɓen jihar a 2020 da tazarar da ya bai wa abokin karawarsa.

  12. An shiga layin zaɓe a Pennsylvania

  13. Yaya ake ƙirga ƙuri'un zaɓen Amurka?

  14. Me zai faru idan aka ƙalubalanci sakamakon zaɓen?

    Ƙarin bayani - https://bbc.com.im/hausa/articles/c0lpnzgnxd8o%3C/a%3E%3C/p%3E%3C/div%3E%3C/div%3E%3C/article%3E%3C/li%3E%3Cli class="css-xxlek1">

    Zuwa yaushe za mu san wanda ya yi nasara tsakanin Harris da Trump?