Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Donald Trump zai yi kome a matsayin shugaban Amurka na 47

Wannan shafi na kawo muku rahotanni da bayanai kan zaɓen ƙasar Amurka da aka gudanar a ranar Talata 5 ga watan Nuwamban 2024.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Mohammed, Usman Minjibir, Umar Mikail, Ibrahim Muhammad da Abdullahi Bello Diginza, Rabiatu Kabir Runka

  1. Akwai yiwuwar Trump ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka

    Bisa ga dukkan alamu, Donald Trump ya riga ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka, inda ya yi kome a fadar shugaban ƙasar, bayan Joe Biden ya kayar kayar da shi shekara huɗu da suka gabata, kamar yadda wakilin BBC, Anthony Zurcher ya bayyana a sharhinsa.

    Tun tuni Trump ya yi wa magoya bayansa jawabi, inda a ciki ya bayyana cewa ya samu gagarumar nasara a zaɓen.

    Trump ya fi mayar da akalar yaƙin zaɓensa ne kan farfaɗo da tattalin arziki da yaƙi da kwararowar baƙin haure.

  2. Trump ya samu ƙuri'u 279 na wakilan masu zaɓe

    Donald Trump ya samu ƙuri'un wakilan masu zaɓe da ake kira electoral college guda 279 zuwa yanzu, ita kuma Kamala tana da guda 219.

    Dama ana buƙata ne ɗantakara ya samu ƙuri'u 270 na wakilan masu zaɓe domin lashe zaɓen na shugaban ƙasa. Yanzu ana dakon ƙuri'u wakilan masu zaɓe 46. Ke nan ko da ta lashe sauran ƙuri'un ba za ta kamo shi ba.

    Haka kuma ya wuce ta a yawan ƙuri'un da gama-garin mutane suka kaɗa.

    Yanzu dai saura sakamako guda shida ake jira.

  3. Tinubu ya taya Donald Trump murna

    Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya taya Donald Trump murna, inda ya ce a shirye yake su ci gaba da aiki tare domin inganta alaƙa tsakanin Najeriya da Amurka.

    Ya ce, "idan muka haɗa kai, za mu inganta tattalin arziki da zaman lafiya da magance matsalolin da al'umarmu ke fuskanta," kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya sanar.

    Trump ne dai ya sanar da samun nasararsa a jawabinsa ga magoya bayansa, inda ya ce ya samu gagarumar nasara.

    Tinubu ya kuma yaba wa Amurkawa bisa yadda suka gudanar da zaɓen cikin lumana.

    Tinubu ya ce kasancewar Trump ya taɓa yin mulkin ƙasar, dawowarsa a matsayin shugaban ƙasar na 47 zai zo da gagarumar sauyi a tattalin arziki da ƙarin haɗin kai tsakanin Amurka da ƙasashen Afirka.

  4. Allah ne ya san dalilin da ya tseratar da ni daga yunƙurin kisa - Trump

    Donald Trump ya ce ashe ba a banza ya tsallake yunƙurin kashe shi da aka yi ba.

    Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga ɗimbin magoya bayansa, inda ya bayyana nasararsa.

    A watan Yuli ne aka kai masa hari a wurin yaƙin neman zaɓensa.

    Da yake jawabin, ya ce, "ba a banza rayuwa ta tsira ba."

    Har yanzu dai Trump bai kai adadin wakilan zaɓen da aka buƙata ba domin tabbatar da nasararsa a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

  5. Yadda aka watse a wurin da aka shirya domin Kamala ta yi jawabi

    Da farko an shirya kujeru a jami'ar Howard domin sauraron jawabin Kamala Haris ne, amma da sakamako ya fara fitowa ƙarara, sai aka watse a wurin, aka bar kujeru ba kowa.

  6. Su wane ne wakilan masu zaɓe da ake kira 'electoral college' kuma wace rawa suke takawa?

    A ranar Talata ne miliyoyin Amurkawa suka kaɗa ƙuri'ar zaɓen shugaban ƙasar Amurka. Sai dai akwai yiwuwar ɗan takarar da ya fi yawan kuri'u ba shi ne zai yi nasara ba.

    Domin kuwa ba masu kaɗa ƙuri’a ne ke zaɓar shugaban ƙasa kai tsaye ba, wani tsari ne da ake kira wakilan masu zaɓe ko kuma electoral college a Turance.

    Me ake nufi da wakilan masu zaɓe?

    Mafi yawan masu zaɓe sun kaɗa ƙuri'a ne ga ƴar takarar Democrat Kamala Harris ko ɗan Republican Donald Trump.

    Amma waɗannan ƙuri'un ba su za su tantance wanda ya yi nasara kai tsaye ba. A maimakon zaɓe na ƙasa bai-ɗaya, zaɓen na kasancewa ne a matakin jiha-jiha.

    Samun ɗaya daga cikin jihohi 50 na nufin ɗan takara ya lashe duk ƙuri'un abin da ake kira wakilan zaɓe na wanna jihar. Akwai adadin kuri'u 538 na wakilan zaɓe a Amurka baki ɗaya.

    Ana buƙatar dan takara ya sami rinjayen kuri'u - 270 ko fiye da haka - don lashe zaɓen shugaban ƙasa. Abokin takararsu kuma ya zama mataimakin shugaban ƙasa.

  7. Netanyahu ya taya Donald Trump murna

  8. Wannan nasara ce ga Amurkawa baki ɗaya- Trump

  9. Donald Trump na kan hanyar isa cibiyar dakon sakamakonsa a Florida

  10. Harris ba za ta yi jawabi a daren yau ba