Rufewa
Masu bibiyar mu anan muke muku godiya da fatan alheri bisa ƙoƙarin da kuke wajen karanta labaran da muke wallafa muku.
Rabiatu Kabir Runka ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku rahotanni da bayanai kan zaɓen ƙasar Amurka da aka gudanar a ranar Talata 5 ga watan Nuwamban 2024.
Isiyaku Mohammed, Usman Minjibir, Umar Mikail, Ibrahim Muhammad da Abdullahi Bello Diginza, Rabiatu Kabir Runka
Masu bibiyar mu anan muke muku godiya da fatan alheri bisa ƙoƙarin da kuke wajen karanta labaran da muke wallafa muku.
Rabiatu Kabir Runka ke cewa mu kwana lafiya.
Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer, ya yi waya da Trump bayan samun nasararsa.
Fadar gwamnatin Birtaniya ( Downing Street ) ta tabbatar wa da BBC cewa sun yi magana.
Ana sa ran nan gaba kaɗan ofishin Firaministan zai bada cikakken bayanin tattaunawar ta su.
Fadar White house ta ce shugaba Joe Biden ya taya Donald Trump murnar lashe zaɓe ta wayar tarho.
Biden ya bayyana cewa zai tabbatar da ya miƙa mulki cikin sauƙi, ya kuma gayyaci Trump zuwa Fadar White House domin su tattauna.
Zai kuma yi jawabi ga ƴan ƙasar ranar Alhamis kan sakamakon zaɓen da kuma shirin miƙa mulki, cewar sanarwar.
Biden ya kuma yi wa Kamala murnar kammala yaƙin neman zaɓenta mai cike da "tarihi".
A cikin wata sanarwa da ofishin yaƙin neman zaɓen Donald Trump ya fitar, ya kira nasararsa da wadda ba a taɓa ganin irinta ba a tarihin Amurka.
Ya kuma yi alkawarin zai jajirce wajen gina Amurka, batun da ya sha nanatawa a wajen yaƙin neman zaɓensa.
"Ba zani tsahirta ba, har sai na samar da Amurka mai ƙarfin faɗa a ji kuma amintacciya ga yaranmu da ku," In ji shi.
"A tare za mu samar wa Amurka makoma mai kyau."
"Ina sake gode maku da kuka zaɓe ni da gagarumin rinjaye."
Ba shakka dawowar Trump a shugabancin Amurka abu ne mafi ɗaukar hankali a tarihin ƙasar, kasancewar bayan shekara huɗu da barinsa White House miliyoyin Amurkawa sun sake zaɓensa domin ya koma karo na biyu.
Abubuwan da suka faru a yaƙin neman zaɓen abubuwa ne da za su tabbatu a litattafan tarihi - ya tsira daga yunƙurin kashe shi sai biyu kuma ainahin abokin karawarsa a zaɓen Joe Biden ya fice daga takara 'yan watanni kafin ranar zaɓe.
Nasararsa ta zo ne bayan matsaloli da ya faɗa - ya ki yarda da sakamakon zaɓen 2020, wanda ya faɗi a hannun Biden, da kuma har yanzu ana bincikensa kan rawar da ya taka a ƙoƙarin sauya sakamakon zaɓen.
Saƙonsa a kan tattalin arziƙi ya yi tasiri
Mutane da dama na ɗari-ɗari da shi - yawancin mutanen da na tattauna da su a lokacin yaƙin neman zaɓensa sun ce za su so su ga ya daina magana barkatai - amma duk da haka sun kawar da kai a kan wannan, inda suka mayar da hankali kan tambayar da yake yawan yi a wajen yaƙin neman zaɓensa - “Da rayuwarku ta shekara biyu baya da ta yanzu wacce ce ta fi?”
Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris ta kira Donald Trump a waya domin taya shi murnar lashe zaɓen shugaban ƙasa, a y cewar rahoton kafar yaɗa labarai ta CBS.
Yayin kiran, Kamala ta jaddada batun miƙa mulki cikin lumana, da kuma zama shugaba na kowa da kowa ga Amurkawa, kamar yadda wani mai taimaka mata ya faɗa wa CBS.
Ana sa ran za ta yi wa jama'a jawabi a farfajiyar jami'ar Howard University a yau Laraba.
Shugabannin duniya da dama sun yi magana da Donald Trump tun bayan fara sanar da sakamakon zaɓe.
Firaministan Indiya Nerendra Modi ya ce ya yi tattauna "mai daɗi" da abokinsa Trump domin taya shi murnar nasarar da ya yi.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya ce yana sa ran yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Trump domin kyautata alaƙarsu a ɓangaren fasaha, da tsaro, da kuma makamashi.
Firaministan Isra'ila Benjami Netanyahu ya yi magana da Donald Trump ta waya a yau, a cewar sanarwar da ofishin yaɗa labarai na gwamnati ya fitar.
Cikin wata tattaunawa mai mahimmanci da kuma fahimtar juna, Netanyahu ya taya Donald Trump murnar lashe zaɓe, inda "suka amince za su yi aiki tare kan tsaron Isra'ila", in ji sanarwar.
A cewar sanarwar, sun kuma tattauna batun "barazanar Iran".
Tun da farko, Netanyahu ya bayyana nasarar Trump da "babba" a cikin wata sanarwa da Benyamin da Sara Netanyahu suka sanya wa hannu.
Akwai wasu abubuwa da suke tattare da wannan zaɓen na bana da basu taɓa faruwa ba a tarihin Amurka.
Nan gaba a yau ne Kamala Harris za ta yi jawabi a jami'ar Howard. Har yanzu ba ta koma kan sakamakon zaɓen ba.
Ofishin yaƙin neman zaɓen ta ya gayyaci magoya bayanta da su halarci inda za ta yi jawabi ita da mataimakinta, Tim Walz a Washington DC.
Za ta yi jawabin ne da misalin ƙarfe 1pm zuwa 5pm na yamma agogon Amurka, wato ƙarfe 6pm zuwa 10pm, agogon GMT da Ghana.
Daga Ethiopia zuwa Masar, Afirka ta Kudu zuwa Najeriya, shugabannin Afirka sun taya Donald Trump, murnar nasarar cin zaɓen shugaban Amurka a karo na biyu bayan ya bar mulkin shekara huɗu baya.
A lokacin mulkinsa na farko Mista Trump bai ziyarci Afirka ba, abin da ya janyo masa suka kan taƙaitacciyar mu'amulla da nahiyar.
Sai dai masu sharhi na ganin wa'adin mulkinsa na biyu ka iya ba shi damar ƙarfafa manufofin Amurka a kan abubuwan da suka shafi Afirka, kamar lafiya da kasuwanci da kuma tsaro.
Haka kuma ana ganin sai Trump ya yi aiki tuƙuru kafin ya iya kawar da tasirin ƙasashe irin su China da Rasha, wadda ta samu shiga Afirka sosai yayin da Amurka ta kawar da kai a kan nahiyar.
Dukkan manya kafafen watsa labarai ciki har da BBC, sun bayyana cewa Trump na kan gaba a zaɓen shugaban ƙasar Amurka.
Kuma a cikin daren jiya, mun jiyo Donald Trump , ya bayyana samun nasararsa, sai dai har zuwa yanzu, Kamala Harris ba ta taya Trump murna ba ko kuma ta ansa shan kaye a zaɓen.
Kodayake hakan ba wani laifi ba ne,kuma hakan ta sha faruwa a baya.
A shekarar, 2016, tsohuwar ƴar takarar shugabar ƙasa ,Hillary Clinton, ta ansa shan kaye cikin lokaci bayan da Trump ya samu nasara.
An jima ana sa ran Harris za ta yi jawabi a gaban magoya bayanta a jami'ar Howard, inda ake tunanin za ta amsa shan kaye.
Za a rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka a wurin biki ranar Litinin, 20 ga watan Janairun 2025.
Kafin haka, sai an kammala duba ƙuri'un wakilan masu zaɓe wato electoral college. Akan bai wa kowace jiha yawan wakilan ne gwargwadon yawan al'ummarta, sannan su kuma su zaɓi duk ɗantakarar da ya cinye ƙuri'un zaɓen jihar.
Amma za a yi hakan ne yayin ganawa a ranar 17 ga watan Dismaba.
Sai kuma sabuwar majalisar wakilai ta zauna ranar 6 ga watan Janairu, inda za ta ƙirga ƙuri'un a hukumance kuma ta tabbatar da sabon shugaban ƙasa.
Kafin zaɓen, an yi ta tafka muhawara a ƙasar Lebanon kan makomar yaƙin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya, inda wasu ke ganin Biden na da hannu a kashe sama da Falasɗinawa 40,000 a Gaza.
Wasu kuma cewa suke yi Amurka na ci gaba da goyon bayan Isra'ila da makamai da suke amfani da su a Gaza, da ma kan Hezbollah a Lebanon.
"Babu abin da ya shafe mu. Da Trump ɗin da Kamala duk tsarinsu ɗaya ne," in ji Sanaa El Banji. "Dukansu suna goyon bayan Isra'ila, kuma babu ruwansu da yaƙin da ake yi a Lebanon."
Sai dai ta ƙara da cewa, "Trump ya fi zafi, kuma ba ya ɓoye-ɓoye."
Wata tsohuwar ma'aikaciyar gwamnati mai suna Wafa Karameh ta ce, " dukansu ɗaya ne, amma ina fata Trump ya zo da alheri a shekara huɗu masu zuwa."
Shi kuma injiniya Omar Baalbahi cewa ya yi, "abin da muke fata shi ne ya samar mana da zaman lafiya. Mutum ne mai faɗa da cikawa. Mun sha wahala a zamanin jam'iyyar Democrats. Muna fatan samun sauƙi."
Kasuwar hannun jarin Amurka na kamfanoni da dala da Bitcoin sun tashi bayan Donald Trump ya lashe zaɓe.
Alƙawarin rage haraji da ya yi zai sa a samu ƙarin masu zuba jari a ƙasar, amma barazanarsa ta ƙaƙaba ƙarin haraji kan shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje, za ta iya jawo hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.
Haka kuma kasuwar cyrpto ta tashi, inda Bitocin ya kai farashin da bai taba kaiwa ba.
Donald Trump ya lashe Wisconsin da ratar kashi 1, wanda hakan ya ƙara tabbatar da nasararsa a zaɓen.
Har yanzu dai ba a kammala tattara sakamakon zaɓen ba a hukumance, amma dukkan alamu sun nuna Trump ya riga ya lashe zaɓen bayan samun adadin ƙuri'un wakilan zaɓe da aka buƙata domin cin zaɓen,
Tun kafin nan ma, Trump ya riga ya bayyana wa magoya bayansa a Florida cewa ya samu gagarumar nasara a zaɓen.
A daidai lokacin da ake dakon sanar da Donald Trump a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka, ga wasu muhimman abubuwa guda shida da suka faru.
Donald Trump na yawan nanata cewa zai kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe, amma zai gaji manyan yaƙe-yaƙe guda biyu: Yaƙin Rasha a Ukraine da yaƙin Isra'ila a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda wakilin harkokin tsaro, Frank Gardner ya bayyana.
Haka kuma akwai Koriya ta Arewa, wadda ke yunƙurin assasa makamashin nukiliya, da kuma hasashen da ake yi China za ta ƙara mamaye Taiwan, wadda ƙawar Amurka ce.
Yadda Trump zai fuskanci waɗannan yaƙe-yaƙe abu ne da ba za a iya fahimta ba a yanzu, musamman ganin a yanzu ba ya tare da fitattun janarorin soji da suka yi aiki a tare a wancan gwamnatin.
Sai dai kuma barin abokan hamayyarka cikin duhu yana da muhimmanci a irin wannan yanayi.
Shin zai tursasa Putin ya shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da Ukraine? zai iya dawo da Kim Jong-Un teburin sulhu? zai iya hana Beijjing mamaye Taiwan? zai iya tursasa Iran ta dakatar da ƙungiyoyin da take ɗaukar nauyi domin hana Isra'ila, wadda take samun goyon bayan Amurka kai hari a cibiyoyin makamashin nukiliyarta?
Waɗannan amsoshin dai sai an jira lokaci za a gani.
Yanzu da Donald Trump ke gab da zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka, bari mu yi waiwaye kan wasu ƙudurorinsa.