Me kuke son sani kan wasan Man United da Brentford?, Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta karɓi bakuncin Brentford a wasan mako na na 34 a Premier League da za su fafata a Old Trafford ranar Litinin.
A wasan farko a bana ranar 27 ga watan Satumba, Brebtford ce ta yi nasara 3-1 a gidanta.
Ga abinda ya kamata ku sani kafin wasan:
- Manchester United ta yi rashin nasara a wasa biyu na baya a lik a hannun Brentford, fiye da yadda ta yi nasara a kanta a wasa 11 da suka wuce (United ta ci takwas da canjaras biyu aka doke ta ɗaya daga ciki.
- Brentford na neman ta doke Manchester United gida da waje a kakar guda (league double) karo na biyu a tarihi. Na farko shi ne a 1936-37, lokacin da Manchester United ta faɗai daga babbar gasar lik.
- Wannan shi ne wasa na shida da Manchester United za ta yi a ranar Litinin a wannan kakar ta Premier League. Wannan shi ne mafi yawa tun kakar 1995-96 (shima shida), yayin da mafi yawansu shi ne bakwai a kakar 1992-93.
- Tun bayan da ta sha kashi 1-0 a hannun Everton a watan Nuwamba, Manchester United ta zura ƙwallo a wasa 21 a jere a Premier League. Wannan shi ne mafi tsawo da ta yi a jere bayan ritayar Alex Ferguson (lokacin da suka zura ƙwalo a wasa 23 a jere tsakanin Nuwamba 2012 zuwa Afrilu 2013).
- Brentford ta yi canjaras a wasa biyar a jere a Premier League. Ƙungiyar ƙarshe da ta yi irin haka ita ce Manchester City wadda ta yi bakwai a jere a 2009.
- Manchester United ta sha kashi 2-1 a hannun Leeds United a wasan gida a makon jiya ranar Litinin, amma ba ta yi rashin nasara a gida sau biyu a jere ba tun Mayu 2025.
- Bruno Fernandes ya bayar da ƙwallo a zura a raga sau 18 a wannan kakar. Mutane uku ne kawai suka fice wannan bajintar da ya haɗa da Thierry Henry (20 a 2002-03), Kevin De Bruyne (20 a 2019-20), da Mesut Özil (19 a 2015-16).








