Labaran wasannin BBC Hausa daga 26 ga Afirilu zuwa 1 ga watan Mayun 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga Lahadi 26 ga watan Afirilu zuwa Juma'a 1 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Haruna Kakangi

  1. , Atletico Madrid v Arsenal

    Nasara biyu kacal Atletico ta samu a karawa 12 da ta yi da ƙungiyoyin Premier (Canjaras 2, Rashin nasara 8), sai dai babu wata ƙungiyar Premier da ta taɓa doke ƙungiyar a gida a matakin kifa ɗaya ƙwale.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  2. , Atletico Madrid v Arsenal

    Arsenal ba ta yi rashin nasara ba a wasa 12 na gasar Champions League da suka gabata.

    Lokaci na ƙarshe da Arsenal ta yi wasa mafi yawa ba tare da rashin nasara ba a gasar Champions League shi ne tsakanin watan Maris na 2005 zuwa Afrilun 2006.

    Ƙungiyar ba ta yi rashin nasara ba har sai a karawarta da Barcelona a wasan ƙarshe, inda ta yi rashin nasara da ci 2-1.

    Idan ƙungiyar ta yi nasara ko canjaras a wasan yau, za ta sake nanata tarihin da ta kafa.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Barka da yamma!, Atletico Madrid v Arsenal

    A jiya an yi wasa mai ƙayatarwa tsakanin PSG da Bayern Munich.

    Masu masaukin baƙi Paris St-Germain ce ta yi nasara a wasan da ci 5-4, a wasan wanda ya ƙayatar sosai.

    Yau kuma Atletico ce ke karɓar baƙuncin Arsenal filin wasa na Riyadh Air Metropolitano.

    Dukkanin ɓangarorin biyu sun yi ƙaurin suna wajen tsaron baya da kuma cin ƙwallo daga bugun ƙusurwa.

    Ko yau ma za a ci ƙwallaye da yawa?

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Gola mai shekara 70 zai tsare raga a gasa mai daraja ta biyar a Sifaniya, Sifaniya

    Spain

    Asalin hoton, CD Lolunga

    CD Colunga na shirin saka mai tsaron raga mai shekaru 70, Mateos Gonzalez a gasa mai daraja ta biyar a Sifaniya ranar Lahadi, wani mataki da kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka ce zai sa ya zama ɗan wasa mafi tsufa da ya taɓa buga wasa a gasar Sifaniya.

    Gonzalez, wanda ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa tun yana da shekaru 43, yana taimaka wa masu tsaron ragar Colunga sanin makamar aiki a wannan kakar a gasar Tercera Federation Group Two.

    Gonzalez ya shaida wa jaridar gida “Las Provincias” cewa bai san ko zai buga cikakken wasan ba.

  5. , Daga Jaridu

    Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool na fatan dangantakar da ke tsakaninsu da RB Leipzig za ta taimaka mu su wajen siyan dan wasan Ivory Coast Yan Diomande mai shekaru 19 a farkon kasuwar musayar 'yan wasa ta bazara.(Football Insider), external

    Har ila yau Liverpool na bibiyar dan wasan Napoli Sam Beukema, mai shekara 27, wanda kocin kungiyar Arne Slot ya dade yana so. (Teamtalk), external

    Everton na shirin zawarcin dan wasan Manchester City Nathan Ake, mai shekara 31, a bazara yayin da dan wasan Netherlands ke neman karin lokacin wasa.(Football Insider), external

    Newcastle da Aston Villa na sha'awar dan wasan Sporting da Uruguay Maxi Araujo,mai shekara 26. (Sport Witness), external

    Dan wasan Feyenoord Ayase Ueda, mai shekara 27, ya shiga cikin jerin sunnayen 'yan wasa masu kai hari da Everton ke so a wannan bazara kuma Leeds da Tottenham da Brighton sun nuna su ma su na son dan kasar Japan . (Teamtalk), external

    Valencia ta kosa dan wasan Belgium Largie Ramazani ya koma dan wasan dindindin daga Leeds bayan dan wasan mai shekara 25 da aka bada shi aro ya nuna kwazo sosai a gasar La liga .(ElDesmarque - in Spanish)

  6. An dakatar da golan Zaragoza, Andrada wasa 13

    An dakatar da mai tsaron ragar Real Zaragoza, Esteban Andrada wasa 13, bayan da ya naushi wani ɗan wasa a karawar hamayya da aka doke su a karshen mako.

    An bashi jan kati a wasan da Huesca ta ci 1-0, hakan ya haddasa rikici tsakanin ɓangarorin kamar yadda hukumar ƙwallon kafar Sifaniya ta sanar ranar Laraba

    An ba Andrada katin gargadi na biyu a minti na 99, amma maimakon ya fita daga fili, sai ya ruga a guje ya je ya naushi kyaftin din Huesca, Jorge Pulido, a fuska, lamarin da ya tayar da tarzoma.

    Sai da ta kai an rike shi daga baya jami'an tsaro suka yi wajen filin da shi zuwa ɗakin hutuwar ƴan wasa.

    Kwamitin ladabtarwa na RFEF ya yanke hukuncin cewa laifin ya cancanci hukuncin dakatarwa mafi tsauri na wasa 12, tare da ƙarin wasa guda ɗaya na dakatarwa kai tsaye saboda jan katin da aka ba ɗan wasan mai shekaru 35.

    Mai tsaron ragar Huesca, Dani Jimenez, wanda shi ma aka kora bayan da ya doki Andrada yayin rikicin, an dakatar da shi wasa huɗu.

    Haka kuma, ɗan wasan Zaragoza, Dani Tasende, wanda aka ba jan kati saboda ya doki ƙafar abokin hamayya bayan da aka duba VAR, an dakatar da shi wasanni biyu.

  7. Darren England ne zai busa wasan Man City da Chelsea a FA Cup, FA Cup

    An nada Darren England a matsayin alkalin wasan ƙarshe a FA Cup tsakanin Manchester City da Chelsea a watan Mayu.

    Darren England, wanda ya jawo cece-kuce ta dalilin VAR a shekarar 2023, an zaɓe shi ya jagoranci wasan ƙarshe na FA Cup na watan gobe.

    Nadin England domin wannan babban wasa tsakanin Manchester City da Chelsea a ranar 16 ga Mayu yana nuna yadda ya taka rawar gani a wannan kakar, kuma babban ci gaba ne a aikinsa bayan kuskuren VAR da ya janyo cece-kuce a wasan Premier League tsakanin Tottenham da Liverpool a watan Satumbar 2023.

    England ya yi kuskure wajen kin soke hukuncin da aka yanke a fili na hana ƙwallon Luis Diaz saboda satar gida. Tun daga lokacin bai jagoranci wani wasa ba na tsawon watanni uku, sannan bai koma aikin VAR ba sai a watan Afrilu na shekara ta gaba.

    England, wanda aka naɗa a matsayin alkalin Premier League a 2020, ya kasance mai jiran-ko-ta-kwana a wasan ƙarshe a FA Cup a bara, kuma ya taba zama mataimaki a wasan ƙarshe a 2015.

  8. , Daga jaridu

    Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham ta nuna matukar sha'awar daukar dan wasan Manchester United Marcus Rashford, mai shekara 28, idan har suka kauce wa faduwa daga gasar firimiya bayan da Barcelona ta nuna shakkun mayar da dan wasan Ingila na dindindin wanda aka ba ta shi aro .(Sport - in Spanish), external

    Akwai yuwuwar"dan wasan Ingila Anthony Gordon mai shekaru 25 ya bar Newcastle a bazara. (Athletic - subscription required), external

    Chelsea ta tuntubi kocin Bournemouth mai barin gado Andoni Iraola kan mukamin kocinta.(Football London), external

    Daraktan wasanni na Arsenal Andrea Berta ya je Istanbul a ranar Lahadi don kallon Galatasaray a yayin da ake rade-radin cewa Gunners na son dan wasan kungiyar da kuma Najeriya Victor Osimhen mai shekara 27. (AS - in Spanish), external

    Jose Mourinho zai iya koma wa Real Madrid a matsayin kocinta a karo na biyu a lokacin bazara inda kocin na Benfica shi ne wanda shugaban kungiyar Florentino Perez ya fi so a cikin wadanda su ke zawarci (Athletic - subscription required), external

  9. Mudryk ya ɗaukaka kara kan dakatar da shi shekara huɗu

    Mudryk

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan Chelsea, Mykhailo Mudryk, ya ɗaukaka ƙara zuwa Court of Arbitration for Sport kan hukuncin dakatar da shi shekaru huɗu da Football Association ta ɗora masa saboda amfani da ƙwayoyi kara kuzari da aka haramta.

    Ɗan wasan tawagar Ukraine mai shekaru 25 ya shafe kusan wata 18 bai buga wasa ba, bayan wani “sakamakon gwajin fitsari da aka same shi da laifi daga nan aka dakatar da shi na wucin gadi a watan Disambar 2024.

    An tuhume shi a watan Yunin 2025, sannan daga baya FA ta yanke masa hukuncin dakatarwar shekaru huɗu – wanda shi ne mafi tsauri – kamar yadda wani mai magana da yawun kotun wasanni ta duniya ya bayyana.

    FA ba ta bayyana cikakken bayani kan wannan shari’ar ba.

    A irin waɗannan lokuta, ana yawan ƙididdige lokacin hukuncin daga ranar da aka fara dakatarwar wucin gadi, wanda ke nufin zai iya dawowa buga wasa kusan a watan Disambar 2028.

    Sai dai yanzu an ɗaukaka ƙara zuwa CAS da ke Switzerland, kuma majiyoyi na kusa da ɗan wasan suna fatan zai iya komawa fili tun daga kakar wasa mai zuwa.

    A wata sanarwa da aka bai wa BBC Sport, CAS ta ce: “Mun tabbatar da cewa mun karɓi ƙarar da Mykhailo Mudryk ya shigar kan FA a ranar 25 ga Fabrairu 2026. A halin yanzu ɓangarorin suna musayar takardun hujjoji, kuma har yanzu ba a tsara ranar sauraron ƙarar ba.”

    BBC ta fahimci cewa Mudryk ya yi hulɗa da maganin mai suna Meldonium, wanda zai iya ƙara ƙarfin numfashi da sa juriya, yayin da yake tare da tawagar Ukraine a watan Oktoban 2024.

    Mudryk, wanda ya koma Chelsea a watan Janairun 2023 kan kuɗin euro miliyan 70 (£61m), bai buga wani wasan gasa ba tun watan Nuwamban 2024.

  10. Mainoo ya tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a Man United, Manchester United

    Manchester United

    Asalin hoton, Getty Images

    Kobbie Mainoo ya sabunta kwantiragi a Manchester United, kamar yadda rahotanni suka nuna.

    Mai shekaru 21, wanda ya fito daga makarantar horar da an wasan ƙungiyar, ya buga karawa 98 da zura ƙwallo bakwai, ciki har da a wasan ƙarshe a FA Cup a 2024 inda United ta doke abokiyar hamayya Manchester City.

    A baya an yi tunanin cewa makomar Mainoo zai bar Old Trafford, bayan da ba a saka shi a wasanni karkashin Ruben Amorim, kuma ba a bayar da raonsa ba a watan Agusta.

    A watan Janairu ma an sa ran za a bayar da aronsa, amma bayan nadin Michael Carrick a matsayin kocin riƙon ƙwarya, sai ya ci gaba da saka shi a wasannin daga nan ya koma taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa ƙungiyar da ta hau matsayi na uku a gasar Premier League.

    A lokacin ne aka fara tattaunawa kan sabunta kwantiraginsa, kuma rahotanni sun ya amince da sabuwar yarjejeniya da zai ci gaba da taka leda zuwa karshen kakar 2031.

    Tun farko yarjejeniyar Mainoo za ta kare a Old Trafford a karshen kakar baɗi, amma yanzu zai ci gaba da taka leda a ƙungiyar.

    Haka kuma rawar da yake takawa a United, tawagar Ingila ta mika masa goron gayyata da ya fara a wasan ƙarshe a Euro 2024, wanda ke neman gurbi a cikin tawagar Thomas Tuchel domin buga gasar kofin duniya.

  11. Abin da ya kamata ku sani kan wasan Atletico da Arsenal a Champions League, Champions League

    Champions League

    Asalin hoton, Getty Images

    Atletico Madrid za ta kara da Arsenala wasan farko zagayen daf dakarshe a Champions League da za su kara a Sifaniya ranar Laraba.

    Ƙungiyoyin biyu ba wadda ta taɓa lashe kofin, illa kungiyar Sifaniya ta kai zagayen karshe sau uku ita kuwa ta Ingila sau ɗaya ta kai karawar karshen.

    Ga jerin abubuwan da ya kamata ku sani kan wasan:

    Wannan shi ne karo na huɗu da Atletico Madrid da Arsenal za su haɗu a Champions League. A baya, Atletico ta yi nasara da jimillar ƙwallaye 2-1 a wasan kusa da na ƙarshe a Europa League a 2017/18 (1-1 a Landon, 1-0 a Madrid), yayin da Arsenal ta doke su da ci 4-0 a gida a wasan na uku acikin rukuni a Champions League a wannan kakar.

    Atletico ta yi nasara sau biyu a cikin wasa 12 a baya a UEFA da ta buga da ƙungiyoyin Ingila (ta yi kunnen doki biyu, ta sha kashi sau takwas), amma a Madrid ta sha kashi sau biyu cikin wasa 18 da ta buga da su (ta ci tara, da canjaras bakwai).

    Atletico ta yi nasara a wasa 11 cikin 15 a fafatawar gida-da-waje da ta yi da ƙungiyoyin Ingila a UEFA, ciki har da dukkanin daf da karshe uku: da Liverpool a Europa League 2009/10, da Chelsea a Champions League 2013/14, da kuma Arsenal a Europa League 2017/18.

    Ƙungiyar ta Spain ta kai wasan kusa da na ƙarshe a European Cup/Champions League karo na bakwai, inda ta yi nasara uku, ta sha kashi karo uku a cikin shida da suka gabata. Na ƙarshe ya kasance a 2016/17 lokacin da ta sha kashi 4-2 a hannun Real Madrid, yayin da nasararta ta ƙarshe a wannan mataki ita ce a 2015/16 lokacin da ta doke Bayern Munich da dokar ƙwallon waje.

    Jimillar ƙwallo 34 da Atletico ta ci a wannan kakar ita ce mafi yawa da ta taɓa yi a European Cup/Champions League (dukkan mataki). Na baya baya nan shi ne ƙwallo 26 a kakar 2013/14.

    Arsenal ta yi nasara a wasa bakwai bayaa a Champions League da ta buga da ƙungiyoyin Spain, ciki har da doke Atletico da 4-0 a gida a bana. Ita ce ƙungiya ta farko a tarihin gasar da ta yi nasara a wasa bakwai a jere kan ƙungiyoyin Spain. Haka kuma ta yi nasara a wasa huɗu a bayan nan da ta buga a waje da ƙungiyoyin Spain.

    Gunners ta yi nasara a wasa biyar, da sha kashi huɗu a cikin tara da suka gabata a fafatawar gida-da-waje a Champions League da ƙungiyoyin Spain. Wannan shi ne karo na biyu da ta kai daf da karshe a gasar tana fuskantar ƙungiyar Spain, bayan ta yi nasara a kan Villarreal da jimillar 1-0 a 2005/06.

    Arsenal ta kai wasan kusa da na ƙarshe a Champions League karona biyu a jere – karo na farko a tarihinta – kuma wannan shi daf da karshe na huɗu gaba ɗaya. Ta doke Villarreal a 2005/06, amma ta sha kashi a biyun da suka biyo baya a wannan mataki, a hannun Manchester United a 2008/09 da kuma Paris Saint-Germain a kakar da ta gabata.

    Ƙungiyar Landon ita ce kaɗai ba a doke ta ba a Champions League a wannan kakar (ta ci karawa 10, ta yi canjaras biyu). Idan aka duba gaba ɗaya, ta sha kashi sau biyu kacal a cikin wasa 22 na baya bayan nan a gasar (ta ci wasa 17 da yin canjaras uku).

    Arsenal ta sha kashi sau ɗaya a cikin wasa 11 a bayan nan da ta buga a waje a Champions League (ta yi nasara tara da canjaras ɗaya.).

  12. An kafa tarihi!, PSG 5-4 Bayern Munich

    Wannan ne wasan kusa da na ƙarshe na gasar Champions League da aka fi zura ƙwallo a tarihi.

    Ya yi daidai da wasan Rangers da Eintrancht Frankfurt a zamanin da ake buga gasar European Cup, inda aka tashi wasan Rangers 3-6 Eintracht Frankfurt a kakar wasa ta 1959-60

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  13. AN TASHI WASA: PSG 5-4 Bayern Munich, PSG 5-4 Bayern Munich

    An tashi wasa PSG na gaba da ƙwallo ɗaya.

    Akwai sauran kallo a falle na biyu!

    Ousmane Dembele

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ousmane Dembele

    Wannan ne karon farko da PSG ta doke Bayern Munich tun daga 7 ga watan Afrilun 2021.

    Magoya bayan Bayern Munich sun miƙe tsaye domin jinjina wa ƴan wasansu waɗanda suka yunƙuro bayan an danna su ƙasa.

    Daga 5-2 suka yunƙura aka tashi 5-4.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  14. , PSG 5-4 Bayern Munich

    Bayern na dannawa, tana son ta samu ƙwallo ta biyar kafin a tashi.

    Bayern ta cire Aleksandar Pavlovic ta sako Nicolas Jackson.

    xx

    Asalin hoton, Getty Images

  15. An ƙara minti huɗu, PSG 5-4 Bayern Munich

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  16. , PSG 5-4 Bayern Munich (Minti 89)

    Achraf Hakimi ya ja ƙwallo da gudu sai kuma kawai ya tsaya ya riƙe cinyarsa.

    Wannan ba abu ne da PSG za ta ji daɗi ba.

  17. PSG ta yi canjin ƴan wasa, PSG 5-4 Bayern Munich (Minti 85)

    An sako Lucas Hernandez da Senny Mayulu, an cire Khvicha Kvaratskhelia da Nuno Mendes.

  18. An shiga minti 10 na ƙarshe!, PSG 5-4 Bayern Munich (Minti na 81)

    Mene ne kuma za mu gani kafin a tashi wannan wasa?

  19. Hakimi ya samu kati, PSG 5-4 Bayern Munich (Minti na 80)

    Shi ma Achraf Hakimi ya kamu katin gargaɗi.

  20. Canjin ɗan wasa, PSG 5-4 Bayern Munich (Minti na 79)

    Bayern ta cire Jamal Musiala ta sako Leon Goretzka.