, Minti 32: PSG 1-1 Bayern Munich
PSG na neman ta samu wata fenariti amma ba a bayar ba.
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga Lahadi 26 ga watan Afirilu zuwa Juma'a 1 ga watan Mayun 2026.
Mohammed Abdu da Haruna Kakangi
PSG na neman ta samu wata fenariti amma ba a bayar ba.
Ƙungiyoyin biyu na nuna ƙwarewa, kowace tana kai kora!
Wannan wasa yana ƙayatarwa.

Asalin hoton, Getty Images
Bai ɓaras ba!
Ƴan kallo na ta hura usur a gefen fili amma Harry Kane bai damu ba. Ya kaikaice ya jefa ƙwallo ta gefen dama, wanda hakan ya sa ya zura ƙwallo a wasanni 6 na gasar Champions League a jere.

Asalin hoton, Getty Images
PSG ce ta fara wasa.

Asalin hoton, Getty Images
Za mu kawo muku wasan Champions League zagayen daf da karshe tsakanin Paris St Geramin da Bayern Munich kai tsaye.
Shin sau nawa suka kara, kofuna nawa na gasar zakarun Turai suke da shi
Sai ku biyo mu kai tsaye.

Asalin hoton, Getty Images
John Stones ya yi godiya ga tasirin da Pep Guardiola ya yi a rayuwarsa ta tamaula, bayan da ya tabbatar cewa zai bar Manchester City a ƙarshen kakar bana.
Ɗan wasan mai shekaru 31 zai bar ƙungiyar Etihad, bayan kwantiraginsa ya ƙare a karshen kakar bana, shekaru goma da ya koma ungiyar.
Stones na daga cikin ƴan wasan farko da Guardiola ya saya a 2016, kuma ya buga kusan wasa 300, inda ya lashe manyan kofuna 19, ciki har da Premier League shida da kuma Champions League a 2023.
Stones, wanda ya wakilci ƙasarsa Ingila karo 87, ya fara wasan ƙungiyar Barnsley kafin ya koma Everton a 2013.
Salon wasansa a Goodison Park ya sa Manchester City ta kashe kusan fam miliyan 50 domin sayensa, wanda a lokacin ya zama na biyu mafi tsada a gurbin masu tsaron baya.
Stones na fatan kammala zamansa a City da ƙarin kofuna yayin da ƙungiyar ke fafutukar lashe Premier League da kuma FA Cup, bayan da ta lashe Carabao Cup.

Asalin hoton, Getty Images
Xabi Alonso da Andoni Iraola da Marco Silva na daga cikin kociyoyin da Chelsea za ta ɗauki ɗaya daga ciki, inji wasu rahotanni.
Kungiyar na shirin ɗaukar lokaci kafin zaɓar wanda zai maye gurbin Liam Rosenior, wanda aka kora makon da ya gabata, inda take nazarin ƴan takara da dama.
An fahimci cewa Chelsea na son koci mai gogewada kwarewa bayan gwajin da bai yi nasara ba tare da Rosenior, wanda bai taba horar da ƙungiya a Premier League b.
Ana sa ran za a kammala yanke shawara kafin kare kakar nan, inda kocin rikon ƙwarya Calum McFarlane ke jagorantar ƙungiyar a halin yanzu.
Kocin Fulham, Marco Silva, kwantiraginsa zai ƙare a ƙarshen kakar nana, kuma bai tabbatar da cewa zai ci gaba da zama a Craven Cottage ba, yayin da Iraola ya sanar a farkon Afrilu cewa zai bar Bournemouth a wata mai zuwa.
Shi kuwa tsohon ɗan wasan Liverpool, Alonso, baya aiki tun bayan da aka kora shi daga Real Madrid a watan Janairu.
Alonso mai shekaru 44 yana da ƙwarewa sosai, inda ya taba lashe UEFA Champions League sau biyu a matsayin ɗan wasa, sannan ya jagoranci Bayer Leverkusen da ɗaukar Bundesliga ba tare da shan kashi ba a 2024.
Biyu daga cikin kociyoyin Chelsea na baya-bayan nan ba su taba horar da ƙungiya a Premier League ba. Enzo Maresca ya lashe Championship da Leicester City a kakarsa guda, bayan da ya taɓa aiki da matasan Manchester City da kuma zama mataimaki ga Pep Guardiola.
Kwarewar Rosenior kuwa ta haɗa da kakar guda a Hull City da kuma wata 18 a Strasbourg, inda ya kai su gasar UEFA Europa Conference League a kakar da ta gabata.
Rahotanni sun nuna cewa a cikin ƙungiyar an amince cewa ɗaukar koci mara ƙwarewa ya kasance kuskure, kuma yanzu suna neman sabon salo daban wajen zaɓen koci na gaba.
An yi wa Luka Modric tiyata cikin nasara bayan raunin da yaji, kamar yadda hukumar ƙwallon kafar Croatia ta sanar, makonni kaɗan kafin dan wasan tsakiya na AC Milan mai shekaru 40 ya halarci gasar kofin duniya ta biyar a rayuwarsa.
Modric ya samu wannan rauni ne a wasa da Juventus da suka tashi 0-0 a filin San Siro ranar Lahadi.
AC Milan na matsayi na uku a teburin gasar, tana bayan Inter Milan da maki 12, yayin da wasanni huɗu - huɗu suka rage. Ana da shakku ko Modric zai iya taka rawa a sauran wasannin kakar, kuma ana iya bukatar ya sanya abin rufe fuska idan ya warke kafin gasar kofin duniya.
Gasar FIFA World Cup 2026, wadda Amurka da Canada da Mexico za su ɗauki nauyin shirya ta, za ta a fara ranar 11 ga watan Yuni, inda Croatia za ta kara da England da Ghana da kuma Panama.

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City za ta fuskanci ƙalubale bayan da za ta yi wasa huɗu cikin kwanaki 11 a wata mai zuwa, sakamakon sauya jadawalin wasu muhimman wasanni a fafatawar lashe Premier League.
Ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama za ta karɓi bakuncin Crystal Palace ranar Laraba 13 ga watan Mayu, sannan ta je gidan Bournemouth kwanaki shida bayan nan, yayin da wasan ƙarshe a FA Cup da Chelsea za ta yi ne ranar Asabar 16 ga watan Mayu.
Za ta fuskanci Crystal Palace ranar 13 ga watan Mayu, tun farko an tsara yin fafatawar ranar 13 ga watan Maris, amma aka ɗage, saboda lokacin City za ta fafata da Arsenal a Carabao cup.
Haka shima wasan Bournemouth an ɗage shi, saboda FA Cup da Man City za ta kara da Southampton.
Tun farko an tattauna tsakanin Man City da Palace da Bournemouth da mahukuntan tamaular Ingila kan warware ranar buga wasannin.
Itama Arsenal mai jan ragama a teburin Premier League za ta yi wasannin daf da daf, wadda za ta yi karawa uku a kwana bakwai.
Gunners ɗin za ta je Sfaniya domin buga wasan farko a daf da karshe a Champions League ranar Laraba, sannan takece raini da Fulham ranar Asabar a wasan Premier, sannan ta buga wasa na biyu da Atletico ranar Talata a makon gobe.
Sauran wasannin Manchester City:

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Real Madrid, Eder Militao, ba zai halarci gasar kofin duniya ba, bayan da aka yi masa tiyata sakamakon raunin da ya ji, kamar yadda ƙungiyar ta Spain ta sanar a ranar Talata. Wannan babban koma baya ne ga Real Madrid da ƙasarsa Brazil, kasa da kwanaki 50 kafin a fara gasar kofin duniya ranar 11 ga watan Yuni.
Real Madrid ta ce: “An yi wa ɗan wasa Éder Militão tiyata cikin nasara. Likita, Lasse Lempainen ne ya gudanar da aikin karkashin kulawar likitocin ƙungiyar. Militão zai fara jinya a kwanaki masu zuwa.”
Militao ya ji rauni ne a gasar La Liga da Real Madrid ta kara da Alaves makon da ya gabata, inda nan take ya nuna yana son a sauya shi.
Da farko an yi tunanin ɗan wasan mai shekaru 28 zai iya murmurewa kafin gasar kofin duniya, amma ƙarin gwaje-gwaje da aka yi masa, ya nuna cewa raunin ya dawo ne daga wanda ya taɓa samu a watan Disamba.
Haka kuma, Militao ya sha fama da manyan raunukan gwiwa sau biyu a ƴan shekarun nan.

Asalin hoton, Getty Images
Paris Saint-Germain za ta kara da Bayern Munich a wasan farko zagayen daf da karshe a Champions League ranar Talata a Faranasa.
PSG, mai kofin Champions League na bara ta kawo wannan matakin bayan doke Liverpool, ita kuwa Bayern mai Champions League shida ta yi waje da Real Madrid ne.
Ga abinda ya kamata ya kusa kan wasan PSG da Bayern Munich:

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta doke Brentford 2-1 a Old Trafford a wasan mako na 34 a Premier League da suka buga ranar Litinin.
United ta faracin ƙwallo ta hannun Casemiro daga baya Benjamin Sesco ya kara na biyu tun kan hutu, daga baya Brentford ta farke ta hannun Mathias Jensen saura minti uku a tashi daga karawar.
Ƙyaftin Bruno Fernandes ne ya bayar da ƙwallo na biyu aka zura a raga, kenan yana da hannu a cin 140 a United ya ci 70 ya bayar da 70 aka zura a raga a Premier League na biyar a jerin irin wannan kwazon da su Cristiano Ronaldo suka yi.
Da wannan sakamakon Man United ta ci gaba da zama a mataki na uku da maki 61 da tazarar uku tsakani da Liverpool ta hudu da kuma Aston Villa ta biyar.
Ita kuwa Brentford tana ta taran teburi da maki 48, kuma saura wasa huɗu-huɗu a kammala kakar nan.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙyaftin din Liverpool, Virgil van Dijk, ya ce ya yi imanin za a yi wa Mohamed Salah kayatatcen bikin ban kwana da ya dace, koda ya gama buga wasannin kakar nan, sakamakon raunin da ya ji.
Ɗan wasan tawagar Masar yaji rauni a karawar da Liverpool ta doke Crystal palace a Premier League, kuma saura wasa huɗu - huɗu suka rage a kammala kakar nan.
Liverpool na jiran sakamakon gwaji don sanin girman raunin, kuma duk da zai zama abin takaici idan Salah bai samu damar yin bankwana a fili ba—inda Brentford za su ziyarce su a wasan ƙarshe a kakar—Van Dijk ya ce hakan ba zai rage irin girmamawa da soyayyar da za a nuna wa Salah ba.
Salah ya zura ƙwallo 257 a wasa 440 tun zuwansa a 2017, kuma mutane biyu kacal ne suka fi shi wannan tarihin a kungiyar da ya haɗa da Ian Rush da kuma Roger Hunt.
A wasannin da ya buga a Liverpool, ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarori ciki har da lashe Champions League da kofunan Premier League biyu da FA Cup da kuma EFL Cup,

Asalin hoton, Getty Images
Trevoh Chalobah ya amince cewa ƴan wasan Chelsea dole su ɗauki nasu kason laifi kan rikice-rikicen da suka kai ga korar Liam Rosenior.
Nasarar da suka samu a wasan kusa da na ƙarshe a FA Cup a ranar Lahadi da cin Leeds United 1-0 a Wembley ta nuna kokarin Chelsea da kai wasan karshe karon farko a FA Cup tun bayan 2022.
Ƙwazon da Chelsea ta yi a FA Cup ya bambanta da wanda ta yi a wasan da Brighton ta doke ta 3-0 a Premier League da ta kai ta yi rashin nasara ta biyar ba tare da cin ƙwallo ba, hakan ya sa aka kori Rosenior.
Enzo Fernandez ne ya ci ƙwallon da ta kai Chelsea wasan karshen a FA Cup a karkashin kocin rikon ƙwarya Calum McFarlane, wanda zai ja ragama zuwa karshen kakar nan.
Babban aikin da ke gaban McFarlane mai shekaru 40 shi ne gyara mummunan salon wasan Chelsea a Premier League, inda suka yi rashin nasara biyar a jere ba tare da sun zura ƙwallo ba—wanda shi ne mafi muni tun 1912—da kuma dawo da fatansu na samun gurbin zuwa Champions League a baɗi.

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich na shirin fara tattaunawa da Harry Kane kan sabunta kwantiragi a ƙarshen kakar wasan bana a cewar Karl-Heinz Rummenigge.
Kane ya zama kashin bayan ƙungiyar tun bayan komawarsa Jamus daga Tottenham a lokacin a 2023 a yarjejeniyar da ta kai kusan fam miliyan 100.
Kyaftin din Ingila ya zura ƙwallo 138 a wasa 141 da ya buga wa Bayern, amma a kaka mai zuwa zai rage masa shekara ɗaya kacal a kwantiraginsa ya kare.
Ɗan wasan mai shekaru 32 ya sha nanata cewa yana farin ciki a Munich, kuma rahotanni sun nuna cewa iyalinsa sun riga sun saba da rayuwa a Jamus.
Kane ya lashe kofin Bundesliga biyu tare da Bayern, kuma ya taimaka musu kaiwa zagayen kusa da na ƙarshe a Champions League a wannan kakar, inda za ta kara da Paris Saint-Germain.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan tawagar Croatia, Luka Modric, za a yi masa tiyata, saboda raunin da ya ji, kamar yadda ƙungiyar AC Milan ta sanar a ranar Litinin, makonni kaɗan kafin ya halarci gasar kofin duniya ta biyar a rayuwarsa yana da shekaru 40.
Modric ya samu wannan rauni ne bayan karo da kai da dan wasan tsakiya na Juventus, Manuel Locatelli, a wasan da suka tashi 0-0 a filin San Siro ranar Lahadi. Ya bar fili saura mintuna 10 a kammala wasan.
Duk da yana jin zafi sosai, Modric ya ci gaba da zama a benci har zuwa ƙarshen wasan ba tare da samun kulawar likitoci ba, amma bayan gwaji da aka yi masa an gano cewa sai an yi masa tiyata a wannan ranar Litinin.
AC Milan na matsayi na uku a teburin Serie A, tana bayan Inter Milan da maki 12 tare da wasanni huɗu da suka rage, kuma akwai shakku ko Modric zai iya taka leda a sauran wasannin kakar nan.
Ana sa ran zai iya bukatar sanya abin rufe fuska (protective mask) idan ya warke kafin fara gasar kofin duniya.
Gasar FIFA World Cup 2026, wadda Amurka da Canada da Mexico za su ɗauki nauyin shirya ta, za ta fara ranar 11 ga watan Yuni, inda Croatia za ta hadu da England da Ghana da kuma Panama.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan tawagar Netherlands, Xavi Simons, ya ce zuciyarsa ta karaya, bayan da aka tabbatar ba zai buga sauran wasannin kakar ba tare da Tottenham, haka kuma ba zai halarci gasar kofin duniya ta bana ba, sakamakon raunin da ya ji
An ɗauki Simons a kan gadon ɗaukar marasa lafiya a zagayena biyu a wasan da Tottenham ta doke Wolverhampton Wanderers da ci 1-0 a ranar Asabar a Premier League.
Ɗan wasan mai shekaru 23 ya faɗi ƙasa bayan karo da mai tsaron baya na Wolves, Hugo Bueno. Duk da ya tashi da farko, sai ya sake faɗuwa.
Tottenham ta tabbatar cewa za a yi wa Simons tiyata nan da makonni masu zuwa, dalilin da zai yi jinya mai tsawo.
Wannan rauni ya zo ne a lokacin da Tottenham ke ƙoƙarin tsira daga faɗuwa daga Premier League a kakar bana.
Duk da ta yi nasarar doke Wolves, har yanzu tana cikin yankin barin Premier League tana ta ukun karshe, kuma saura karawa huɗu huɗu a kammala kakar nan.
Gasar FIFA World Cup 2026 da za a yi a Amurka da Canada da Mexico za a fara daga ranar 11 ga watan Yuni, inda Netherlands za ta fara wasa a rukuni da Japan a ranar 14 ga watan Yuni.

Asalin hoton, Getty Images
Watakila Kylian Mbappe ba zai buga wasan El Classico ba tsakanin Barcelona da Real Madrid, sakamakon raunin da ya ji.
Ƙyaftin din tawagar Faransa sai sauya shi aka yi a minti na 81 a wasan da suka tashi 1-1 da Real Betis a gasar La Liga ranar Juma’a.
Real Madrid ta bayyana cewa Mbappe yana da “rauni a kafarsa ta hagu” kuma suna jiran ganin yadda zai warke.
Real Madrid, wadda take ta biyun teburin La Liga da tazarar maki 11 tsakani da Barcelona ta ɗaya, kuma saura wasa biyar - biyar da suka rage, za ta ziyarci Espanyol ranar Lahadi daga nan ta je filin Camp Nou a ranar 10 ga watan Mayu.
Tuni dai Real Madrid ta fice daga Champions League a hannun Bayern Munich, kuma yanzu tana fuskantar kammala kakar nan ba tare da lashe kofi ba a kakar nan, kuma karo na biyu a jere.
Mbappe, wanda ya taɓa jinyar kusan wata guda a farkon shekarar nan saboda matsalar raunin gwiwa, ya zura ƙwallaye 24 a wasa 28 a La Liga, sannan ya ci 15 a karawa 11 a Champions League a wannan kakar.