Labaran wasannin BBC Hausa daga 26 ga Afirilu zuwa 1 ga watan Mayun 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga Lahadi 26 ga watan Afirilu zuwa Juma'a 1 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Haruna Kakangi

  1. Katin gargaɗi, PSG 5-4 Bayern Munich (Minti na 78)

    Michael Olise na ta wahalar da ƴan PSG har ta kai ga Fabian Ruiz ya samu katin gargaɗi.

  2. , PSG 5-4 Bayern Munich

    Abin ba a cewa komai, wannan wasa sai wanda ya gani.

  3. ƘWALLO A RAGA: PSG 5-4 Bayern Munich, Luis Diaz (Minti na 68)

    Da farko ba a bayar da ƙwallon ba amma daga baya an ce ta ciyu.

    Liuz Diaz daga gefe ya jefa ƙayatacciyar ƙwallo ta gefen ƙarfen raga bayan samun fasin daga Harry Kane.

    Yanzu wasa 5-4!!

    xx

    Asalin hoton, Getty Images

  4. , PSG 5-3 Bayern Munich

    An zura ƙwallo TAKWAS, ga shi kuma akwai sauran mintuna 25 kafin a kammala wasa.

  5. ƘWALLO A RAGA: PSG 5-3 Bayern Munich, Dayot Upamecano (Minti na 65)

    An saka wata ƙwallo!

    xx

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Canjin ɗan wasa, PSG 5-2 Bayern Munich

    PSG ta cire Warren Zaire-Emery ta sako Fabian Ruiz.

  7. ƘWALLO A RAGA: PSG 5-2 Bayern Munich, Ousmane Dembele (Minti na 59)

    Wasa ya ƙare!

    Bayern na dannawa gaba amma da alama abin da PSG ke so kenan.

    Desire Doue ya jefa wa Ousmane Dembele ƙwallo daga nesa, ya wuce mai tsaron baya Dayot Upamecano ya jefa ƙwallo a raga.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  8. ƘWALLO A RAGA: PSG 4-2 Bayern Munich, Khvicha Kvaratskhelia (Minti na 56)

    PSG suna da kyau!

    An mayar wa Neuer da ƙwallo amma ba yadda ya dace ba, sai kawai ya buga ƙwallon waje amma sai ta faɗa ƙafar Achraf Hakimi, shi kuma ya tura ƙwallo zuwa ƙafar Khvicha Kvaratskhelia inda shi kuma nan take ya ƙarasa da ita cikin raga.

  9. Bayern ba ta nuna gajiyawa, PSG 3-2 Bayern Munich

    Bayern na nuna dagiya. Sun tsare baya kuma suna danna PSG.

  10. PSG ta kai kora, PSG 3-2 Bayern Munich )Minti na 53)

    Ousmane Dembele ya kai kora mai kyau inda hakan ya jefa Manuel Neuer cikin razani.

  11. , PSG 3-2 Bayern Munich

    Za mu ga yadda za ta kaya a wannan yanayi bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

    PSG za ta iya tunanin ita ce za ta samu nasara, ita kuma Bayern za ta yi ƙoƙarin ganin an tashi tana sa ran zuwa wasan ƙarshe.

  12. AN DAWO DAGA HUTUN RABIN LOKACI, PSG 3-2 Bayern Munich

    Bayern ce ta take ƙwallo!

    Bayern ta yi sauyinɗan wasa, ta cire Alphonso Davies ta sako Konrad Laimer.

  13. , HUTUN RABIN LOKACI: PSG 3-2 Bayern Munich

    Ko za a iya tashi 6-6 a daren yau?

  14. An tafi hutun rabin lokaci, PSG 3-2 Bayern Munich

    Wannan na daga cikin karawa mafi ƙayatarwa tsakanin ƙungiyoyin nan.

  15. ƘWALLO A RAGA!, Ousmane Dembele (Minti na 45+5)

    Babu kuskure kwata-kwata, ya jefa ƙwallon a raga.

    Duk da cewa ana cikin matsi amma Ousmane Dembele ya nuna karaya ba.

    Manuel Neuer ya yi sulu zuwa dama, amma Dembele ya buga ƙwallon da ƙarfi ta yadda babu yadda zai yi da ita.

  16. FEANARITI: An bai wa PSG bugun fenariti

    Ousmane Dembele ne zai buga.

  17. VAR: Ana duba yiwuwar fanareti

    Ousmane Dembele na son a ba PSG fenariti.

    Ya ce yana da yaƙinin ƙwallo ta taɓa hannun Alphonso Davies.

    wants a penalty. He's pretty sure of it after the ball strikes the arm of Alphonso Davies.

  18. An ƙara minti ɗaya, PSG 2-2 Bayern Munich

    An ƙara minti ɗaya bayan ƙarewar mintuna 45 ana shafa wasa, kuma a yanzu PSG ta samu bugun ƙusrwa.

  19. ƘWALLO A RAGA! PSG 2-2 Bayern Munich, Michael Olise

    Ikon Allah sai kallo, abin ba a cewa komai!

    Wannan wasa dama yana zaƙi amma Michael Olise ya ƙara mai sukari.

    Ya ja ƙwallo ya wuce ƴan wasan PSG uku, ya mayar da ƙwallon ƙafarsa ta hagu sannan ya nana ta a raga.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  20. ƘWALLO A RAGA! PSG 2-1 Bayern Munich, Joao Neves (Minti na 33)

    Reshe ya juye da mujiya!

    Ƴan wasan PSG ne suka zari ƙwallo a guje har suka samu bugun ƙusrwa. Ousman Dembele ne ya ɗauko bugun kwana zuwa kan Joao Neves.

    Ya kara mata kai da kyau!

    XXX

    Asalin hoton, Getty Images