Labaran wasannin BBC Hausa daga 26 ga Afirilu zuwa 1 ga watan Mayun 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga Lahadi 26 ga watan Afirilu zuwa Juma'a 1 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Haruna Kakangi

  1. , Atletico 1-1 Arsenal

    Filin wasa na Metropolitano ya sake kaurewa da sowa.

    Ƙasa tana girgiza saboda yadda magoya bayan Atletico Madrid ke tsalle suna sowa.

    Atletico ta dawo da karsashinta!

  2. Canjin ɗan wasa, Atletico 1-1 Arsenal

    Arsenal ta cire Martin Odegaard ta sako Eberechi Eze.

  3. ƘWALLO A RAGA: Atletico Madrid 1-1 Arsenal, Julian Alvarez (Minti na 55)

    Alvarez ya ɗauki ƙwallon da ƙarfi sosai, babu yadda David Raya zai yi da ita.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Fenariti: Atletico ta samu fenariti, Atletico Madrid 0-1 Arsenal

  5. Alvarez ya ɗauki bugun tazara mai kyau, Atletico Madrid 0-1 Arsenal

    Julian Alvarez ya ɗauki bugun tazara mai kyau a kusa da bakin da'irar Arsenal, sai dai ƙwallon ba ta je daidai ba, ta yi waje ta ɓangaren dama.

    Amma an tayar wa David Raya hankali.

  6. An dawo daga hutun rabin lokaci, Atletico 0-1 Arsenal

    Arsenal ce ta take ƙwallo.

  7. HUTUN rabin lokaci, Atletico Madrid 0-1 Arsenal

    An tafi hutun rabin lokaci a wannan wasa yayin da Arsenal ke gaba da ƙwallo ɗaya.

    Kamar yadda aka yi tsammani, dukkanin ƙungiyoyin sun nuna ƙwarewa wajen tsaron baya, amma da alama Arsenal ta yi amfani da damarta.

    Arsenal ce ta fi shafa ƙwallo, inda take da fozeshon 55 yayin da Atletico ke da 45.

    xx

    Asalin hoton, Getty Images

  8. , Atletico Madrid 0-1 Arsenal

    Gykeres ya buga fenaritin da kyau ba tare da nuna tsoro ba.

    xx

    Asalin hoton, Getty Images

  9. An yi ƙarin lokaci, Atletico Madrid 0-1 Arsenal

    Bayan cika minti 45 ana wasa a fallen farko yanzu an ƙara minti biyu.

  10. ƘWALLO A RAGA: Atletico Madrid 0-1 Arsenal, Viktor Gyokeres (Minti na 44)

    Viktor Gyokeres shi ne ya ɗauki fenaritin da ya samo, kuma ya jefa ta a raga.

    xx

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Fanareti: Arsenal ta samu fenareti, Atletico Madrid 0-0 Arsenal

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  12. 'Ratsa bayan Atletico na yi wa Arsenal wahala'

    Abin yana zama mai matuƙara wahala ga Arsenal ta ratsa bayan Atletico.

    Atletico ta daga wajen tsare baya sosai, tana kuma kai kora jefi-jefi.

    Lookman na ƙoƙari!

  13. , Atletico Madrid 0-0 Arsenal

    Noni Madueke ya kai wani hari mai kyau.

    Ya jawo ƙwallo daga ɓangaren dama sai dai ya zo tsakiya a kusa da bakin da'ira ya sharara ta, amma ba ta yi saiti sosai ba, ta fita waje.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  14. , Atletico Madrid 0-0 Arsenal

    Atletico ce ta fara wasan da zafi, amma abin da muke gani a yanzu shi ne kamar lokaci na ƙara tafiya ne Arsenal na ƙara ƙarfi.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Wasa ya ɗau zafi!, Atletico Madrid 0-0 Arsenal

    Wasa ya ɗauki zafi kowane ɓangare na kai kora.

    Yanzu abin da ya rage shi ne mu ga wane ne zai fara ɗaga raga?

  16. Ƙiris!, Atletico Madrid 0-0 Arsenal

    Julian Alvarez na Atletico Madrid ne ya kai wani mummunan farmaki, amma David Raya ya yi abin da ya saba.

    Ya kaɗe ƙwallon, ta tafi waje.

    Alvarez da Raya sun yi ƙoƙari!

  17. Ƙiris!, Atletico Madrid 0-0 Arsenal

    Atletico ta fara wasa da kuzari sai dai Arsenal ce ta fara kai hari na farko mafi haɗari.

    Noni Madueke ne ya ja ƙwallo a guje ta tsakanin ƴan baya ya kutsa cikin da'ira sannan ya kwaso ƙwallon ta sama.

    Gabriel Martinelli ya kai mata kai amma bai same ta ba.

    Piero Hincapie da ke bayansa ya iso da gudu ya bugi ƙwallo to amma ɓangaren da yake ya ƙure da ƙarfen raga sai ƙwallon ta fita waje.

  18. , Atletico Madrid 0-0 Arsenal

    Fili ya cika da sowa da waƙe-waƙen ƴan kallo.

    Tun minti 30 kafin a fara wasa ƴan kallo ke rera waƙe-waƙen ƙara wa ƙungiyoyinsu azama.

  19. AN FARA WASA, Atletico Madrid 0-0 Arsenal

    Atletico Madrid ce ta take wasa.

  20. , Atletico Madrid v Arsenal

    Arsenal da Atletico Madrid su ne ƙungiyoyi biyu da suka fi buga wasannin gasar Europen Cup/Champions League ba tare da lashe kofi ba.

    Arsenal ta buga wasanni 223

    Atletico Madrid ta buga wasanni 190