Bayanai da rahotanni kan zaben Najeriya na 2019

Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu

  1. Waiwaye adon tafiya...

    Za mu soma wadannan rahotanni ne da waiwayen abubuwan da suka faru dangane da bayyana sakamakon zabe ranar Litinin, inda hukuma zaben Najeriya ta bayyana sakamakon zaben jihohi 12. INEC ta ce Muhammadu Buhari ya yi nasara a jiha bakwai, yayin da Atiku Abubakar ya lashe jiha biyar.

    Sakamakon zaben Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Barkanmu da safiya

    As salamu alaikum. Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da asubahi. Da fata za ku ci gaba da bibiyar wannan shafi namu inda muke kawo muku labarai da rahotanni da sharhi kan yadda ake bayyana sakamakon zaben Najeriya da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu. Za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook

    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
  3. Sai gobe, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    A nan za mu dakatar bayanai kai-tsaye da muke kawo wa dangane da sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zaben Najeriya ke tattarawa.

    Za mu ci gaba da kawo ma ku bayanai da rahotanni kai-tsaye gobe idan Allah Ya kai mu.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu.

    Awwal Ahmad Janyau ne ke ma ku sallama.

    Awwal Janyau
  4. An dakatar da tattara sakamako zuwa gobe, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da dakatar da tattara sakamakon zaben shugaban kasa zuwa gobe.

    Ya ce a za a sake bude cibiyar tattara sakamakon da misalin karfe 10 na safiyar Talata.

    Yanzu sakamakon jihohi 12 hadi da Abuja babbar birnin Tarayya aka sanar.

    Dan takarar jam’iyyar APC Muhammadu Buhari ya lashe jihohi bakwai, yayin da abokin hamayyarsa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe jihohi biyar.

    Hukumar zaben Najeriya

    Asalin hoton, @inecnigeria

  5. Atiku ya doke Buhari a Ebonyi, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya lashe zabe a jihar Ebonyi da kuri’a 258,573 inda dan takarar APC shugaba Buhari ya samu kuri’a 90,725.

    Buhari da Atiku

    Asalin hoton, Getty Images

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Ana jiran sakamakon Ebonyi, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Zauren tattara sakamakon zaben shugaban kasa

    Asalin hoton, INEC

  7. jihohi 10 da Abuja yanzu aka sanar, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Dan takarar APC shugaba Muhammadu Buhari ya lashe jihohi bakwai yayin da abokin hamayyarsa Atiku Abubakar ya lashe jihohi uku da Abuja.

  8. Atiku ya doke Buhari a Enugu, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya lashe zabe a jihar Enugu da kuri’u 355,553 inda dan takarar APC shugaba Buhari ya samu kuri’a 54,423.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. An ci gaba da bayyana sakamako

  10. Malam Shekarau ya zama Sanata

    Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya lashe kujerar sanata a Kano ta tsakiya.

    Shekarau na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 506,276 inda ya kada abokin hammayarsa na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’a 29,775.

    A hirarsa da BBC bayan sanar da sakamakon zaben, Shekaru ya ce babu wani sanata a Najeriya da ya samu yawan kuri’unsa.

    Ya kuma yi watsi da zargin cewa ba zai goyi bayan Buhari ba a majalisar dattawa, yana mai cewa Mahassada ne ke son hada shi da Buhari.

    Tsohon gwamnan wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC dab da zabe ya ce zai ba shugaba Buhari cikakken hadin kai musamman wajen tabbatar da sasanci tsakanin bangaren majalisa da bangaren shugaban kasa.

    Tsohon gwamnan Kano Malam Shekarau

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Ana jiran isowar sakamakon wasu jihohi, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Hukumar zabe

    Asalin hoton, INEC

  12. Buhari a ofishin tattara alkalumma na APC a Abuja, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Shugaba Buhari yana duba sakamakon zaben 2019 a ofishin tattara alkaluma na jam'iyyar APC a Abuja ranar Litinin.

    Shugaba Buhari

    Asalin hoton, Presidency

    Shugaba Buhari

    Asalin hoton, Presidency

  13. Buhari ya yi wa Atiku fintikau a Yobe, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Buhari ya lashe jihar Yobe da yawan kuri'u 497,914 yayin da Atiku na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 50,763

    Buhari

    Asalin hoton, Presidency

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Atiku ya lashe Abia, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Atiku ya doke Buhari a jihar Abia inda jam'iyyarsa ta PDP ta samu kuri'a 219,698, jam'iyyar APC ta Buhari kuma ta samu 85,058.

    Atiku Abubakar

    Asalin hoton, @atiku

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Atiku ya doke Buhari a Ondo, Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

    Jam'iyyar PDP ta lashe zaben shugaban kasa a jihar Ondo da kuri'u 275,901, yayin da APC ta samu kuri'u 241,769.

    Atiku Abubakar

    Asalin hoton, @atiku

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Wamakko ya lashe kujerarsa ta sanata

    Sanata Aliyu Magatakarda Wammako, ya lashe kujerar majalisar dattawa ta Sokoto ta arewa a karkashin jam'iyyar APC da kuri'u 172,980 inda ya doke abokin hamayyarsa Ahmed Mohammed Maccido na PDP wanda ya samu kuri'a 138,922.

    Wamakko

    Asalin hoton, @WamakkoAliyu

  17. 'Yan daba na yi wa 'yan kabilar Igbo 'barazana' a Legas

    Tun bayan zaben da aka gudanar a ranar Asabar har yanzu shagunan 'yan kabilar Igbo a kulle suke sakamakon barazana da 'yan daba suka yi masu na su tattara kayayyakinsu su koma yankinsu.

    'Yan daban sun yi zargin cewa 'yan kabilar Igbo mazauna Legas ba su zabi jam'iyyar APC ba a zaben da aka gudanar.

    A yanzu haka 'yan sanda a jihar na kokarin shawo kan wannan lamari. Abubuwa sun lafa a wannan wurin amma har yanzu akwai dar-dar sakamakon ba a san abinda zai iya faruwa ba.

    BBC
    BBC
  18. Ra'ayoyi daga shafin Twitter

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  19. PDP ta yi watsi da sakamakon zabe

    Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta yi watsi da sakamakon zaben da ake gabatarwa a Abuja inda ta bayyana cewa sakamakon ba sahihi ba ne.

    A wata sanarwa, shugaban jam'iyyar ta kasa Uche Secondus ya ce sakamakonsu da suka tattara daga kowace mazaba a kasar ne sahihai.

    Jam'iyyar ta PDP ta zargi jam'iyyar APC da hada baki da hukumar zabe wajen aringizon kuri'u da kuma soke zabuka na rumfunan zabe da dama.

    PDP ta kuma yi kira da a yi gaggawar sakin Buba Galadima da sauran manyan jami'anta da aka kama a kudu maso yammacin Najeriya.

  20. An tafi hutu

    Hukumar INEC ta tafi hutu na takaitaccen lokaci sai karfe 8:00 na dare ake sa ran cewa za a ci gaba da karba da kuma bayyana sakamakon zaben shugaban kasa.