'Yan bangar siyasa sun hana kai sakamako hukumar zabe a Kogi
'Yan bangar siyasa sun tare wa jami'an INEC hanyar don hana su kai sakamakon zabuka zuwa hedikwatar hukumar da ke Jihar Kogi.
Wakilin BBC na wucin gadi da ke wajen ya ce tuni 'yan sanda da sojoji suka isa yankin don shawo kan lamarin wanda ke faruwa a yankin Kogi ta Yamma.
Kazalika kuma ana samun tashe-tahsen a Kogi ta Gabas sakamakon hana kai sakamakon zabe zuwa hukumar INEc ta jiha, abun da ke ta jawo tsaiko wajen tattara bayanan sakamakon 'yan majalisar dattijai da na jihar.
Kwamishinan zabe na jihar Kogi James Apam ya ce har yanzu ba su samu sakamako ko daya ba daga kananan hukumomi 21 na jihar. A yanzu dai rahotanni na cewa ana cike da fargabar abun da ka iya faruwa na rikici a jihar.