Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Bayanai da rahotanni kan zaben Najeriya na 2019

Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu

  1. Yadda aka kai dare ana kidayar kuri'u, Zaben shugaban kasa a Najeriya

  2. Yadda ma'aikatan BBC ke hidima da aikin zabe

  3. An rufe rumfunan zabe da dama, Zaben shugaban kasa a Najeriya

    'Yan Najeriya sun fara dakon sakamakon zaben shugaban kasa bayan rufe rumfunan zabe a mafi yawancin sassan kasar.

    A yayin da aka soma kidayar kuri'u, har yanzu akwai inda ba a kammala zaben ba saboda tsaikun kawo kayayyakin zabe da wuri da kuma tangandar na'ura da aka samu.

    Shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmood Yakubu ne zai bayyana wanda ya yi nasara a zaben na shugaban kasa a hukumance bayan kammala tattara sakamakon zaben daga jihohin Najeriya 36 hadi da Abuja.

  4. Atiku ya kada Buhari a rumfar Villa, Zaben shugaban kasa a Najeriya

    Dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya kada abokin hamayyarsa Shugaba Muhammadu Buhari a daya daga cikin rumfunan fadar shugaban kasar.

    Wakilinmu a fadar Shugaban kasar Haruna Shehu Tangaza ne ya tabbatar da sakamakon.

  5. Wasu daga cikin ra'ayoyinku a shafin Twitter

  6. PDP ta sha kaye a rumfar zaben gidan gwamnatin Sokoto, Zaben shugaban kasa a Najeriya

    APC ta lashe rumfar zaben gidan gwamnatin Sokoto.

    Gwamna mai ci a yanzu shi ne Aminu Waziri Tambuwal kuma dan jam'iyyar PDP ne.

  7. Donald Duke ya fadi a rumfar zabensa

    Dan takarar SDP Donald Duke ya fadi a rumfar zabensa inda ya samu kuri'u 6.

  8. Buhari ya lashe rumfar zaben Dankwambo

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya lashe zabe a rumfar zaben Gwamnan Gombe Hassan Dankwambo.

  9. Atiku ya fadi a rumfar zabensa

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya lashe zabe a rumfar zaben dan takarar PDP Atiku Abubakar. APC ta samu 186 PDP ta samu 167.

  10. Wasu ra'ayoyinku daga Facebook

  11. 'Yan Najeriya na tafka muhawara a shafukan sada zumunta (kashi na biyu)

    Maudu'i na biyu ma fi shahara shi ne #Okota wanda a cikinsa mutane ke ta tafka muhawara da wallafa hotuna dangane da yadda ake magudin zabe da sayen kuri'u da fasa rumfunar zabe da ma kisan jama'a, a unguwar Okota da ke birnin Lagos.

    Wasu masu wallafe-wallafen sun zargin jami'an tsaro da satar kayan zabe da fasa rumfunan zabe da ma tursasa masu zabe a maudu'an #Rivers da #Aguda a jihar Rivers.

    Wani maudu'i kuma da ya tayar da hankali sannan ya kunshi kalamai da wallafe-wallafen nuna kiyayya da barazana ga zaman tare shi ne maudu'in #Igbos.

    A wannan maudu'i dai an ta musayar kalamai marasa dadi tsakanin 'yan kabilar Igbo da sauran kabilun Najeriya, inda wasu kabilun ma suke barazanar ganin sun kori 'yan kabilar Igbo daga garuruwansu musamman na yankin kudu maso yammacin Najeriya.

    Jama'a da dama sun yi amfani da wadannan maudu'ai wajen fallasa abubuwan da suka wakana a mazabunsu.

    Yayin da wasu ke ganin abubuwan da aka wallafa a wadannan maudu'ai ka iya taimaka wa hukumar zabe da jam'iyyun siyasa sanin abubuwan da ke faruwa a wuraren da idanunsu ba su kai kai ba, wasu kuwa na ganin irin wadannan wallafe-wallafe ka iya janyo rikici ne kawai da watsa labaran kanzon kurege.

  12. 'Yan Najeriya na tafka muhawara a shafukan sada zumunta (kashi na daya)

    Ku san za a iya cewa kafafen sada zumunta sun dade ba su samu rubdugun jama'a ba irin wannan rana da 'yan Najeriya ke kada kuri'ar zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki.

    Tun dai wayewar garin Asabar ne maudu'ai iri-iri suka yi ta cin kasuwa a kafar Twitter kuma kusan duk sa'a guda sai an sami wani sabon maudu'i.

    Yanzu dai batun da yake tashe shi ne #NigeriaDecides2019 wanda yake cike da wallafe-wallafe na masu zabe daga sassa daban-daban na Najeriya.

    Mutane kan aiko da hakikanin bayanan abubuwan da ke faruwa a rumfunan zabensu tun daga lokacin fara kada kuri'a har zuwa rufewa da kuma kidaya kuri'un da aka kada.

    Kawo yanzu ma wasu wadanda suka jira aka kidaya kuri'un da suka kada sun fara wallafa sakamakon abun da aka samu a akwatin da suka kada, inda suke fallasa yawan kuri'un da wasu manyan 'yan siyasa suka samu a mazabunsu.

  13. Jamila Nagudu a mazabar Ajiya a Yola

    Jarumar Kannywood, Jamila Na Gudu a mazabar Ajiya da ke Yola a jihar Adamawa

  14. An fara kirga kuri'u a Aba ta jihar Abia

    Wakilin BBC sashen Igbo, Ikechukwu Uzu-Kalu a wata mazaba a Aba ta jihar Abia, kudu maso yamma, inda tuni aka fara kada kuri'u.

  15. Yara manyan gobe

    Wadannan yaran a jihar Gombe sun yi fatan ina ma a ce shekarunsu sun kai yin zabe da ake gudanarwa a wannan lokacin?

  16. An yi hargitsi a karamar hukumar Ogori ta jihar Rivers

    BBC ta tabbatar da rahoton tashin hankali a karamar hukumar Ogori Mangongo jihar Kogi.

    Wani jami'in karamar hukumar Mr Goke Oparison ya bayar da rahoton cewar wasu da makamai sun ziyarci wasu wuraren kada kuri'u, inda suka cinna wa katunan zabe wuta an kuma ji karar tashin bindiga.

    Sai dai har yanzu ‘yansanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.

  17. Bidiyon yadda aka kona kuri'un zabe a Legas

    An kona kuri'un ne a mazabar Alimosho, rumfar zabe mai lamba 2

  18. Bidiyon yadda ake kirga kuri'u

  19. An gama kada kuri'a a fadar shugaban kasa

    A yanzu haka dai an gama kada kuri'a a fadar shugaban kasa a rumfa mai lamba 021 da mai lamba 022. Ana sa ran za a fara rarrabe kuri'un kafin a fara kirgasu da misalin karfe 4:00 na yammaci. Jama'ar da suka kada kuri'a a rumfunan na nan sun yi zaman dirshen suna jira a fara kirga kuri'unsu.

  20. Wasu daga cikin ma'aikatan BBC

    Hotunan wasu daga cikin ma'aikatan BBC bayan tattaunawa a kan yadda za a ci gaba da inganta shirye-shiryen da ake gabatarwa ta redyio da intanet musamman a kan zaben Najeriya.