Matsalar tsaro za ta yi cikas ga zaɓen Najeriya na 2023 - HRW

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ...
An wallafa

Ƙungiyar da ke hanƙoron tabbatar da ƴancin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce rashin hukunta waɗanda aka kama da laifi a zaɓukan ƙasar na baya da kuma gazawar gwamnati na magance matsalar tsaro na barazana ga aiwatar da babban zaɓen ƙasar na 2023.

A ranar 25 ga watan Fabrairu ne al'ummar Najeriya za su zaɓi sabon shugaban ƙasa domin maye gurbin shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda ke kammala wa'adin shugabancinsa, tare da na 'yan majalisar dokokin tarayya, bayan mako biyu kuma za su fita domin kaɗa ƙuri'arsu a zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jihohi.

An dai yi ta samun barazanar tsaro game da zaɓen daga ƙungiyoyi daban-daban a faɗin ƙasar, ciki har da ƙungiyoyin 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma da kudu maso gabashin ƙasar, waɗanda ke yunƙurin daƙile yiyuwar zaɓen.

Wani bayani da ƙungiyar ta Human Rights Watch ta fitar a ranar Litinin ɗinnan ya nuna cewa har yanzu ƙasar ba ta ɗauki isassun matakan da za su kwantar da hankulan mutane ba kan cewa zaɓen zai tafi cikin lumana.

Su wane ne ke takarar shugabancin Najeriya?

Karin bayani kan 'yan takarar shugaban ƙasa na Najeriya

Zaɓi ɗan takara don ganin bayanansa

Bola Tinubu

All Progressives Congress (APC)

  • Shekaru: 70
  • Ya yi karatun akanta a jami'ar Chicago State University.
  • Gwamnan Jihar Legas karo biyu daga 1999 zuwa 2007.
  • Ya wakilci Legas ta Kudu a Majalisar Dattijai daga 1992 zuwa 1993.
  • Gagarumin ɗan siyasa a Najeriya, wannan ne karon farko da yake yin takarar shugaban ƙasa.
  • Adawa da mulkin soja.
  • Ya ninka kuɗin shigar Jihar Legas na shekara-shekara sama da sau huɗu daga biliyan N22.2 a 1999 zuwa biliyan N220.9 a 2007.
  • Ya fara aiki a matsayin mai binciken kuɗi da kuma ma'aji a kamfanin Mobil Producing Nigeria, ɗaya daga cikin kamfanonin man fetur mafiya girma a ƙasar.
  • Inganta harkokin fitar da kaya daga Najeriya zuwa ƙasashen waje da kuma rage dogaro da sayen kaya daga waje.
  • Rage rabin adadi na rashin aikin yi tsakanin matasa cikin shekara huɗu da kuma ƙirƙirar ayyukan yi miliyan ɗaya a ɓangaren sadarwa cikin shekara biyu.
  • Gyara tsarin shari'a don mayar da hankali kan kare afkuwar laifuka da kuma inganta yarda kan jami'an tsaro.

Atiku Abubakar

Peoples Democratic Party (PDP)

  • Shekaru: 76
  • Ya rike mukamin mataimakin shugaban Najeriya daga 1999 - 2007.
  • Ya samu digiri na biyu a ɓangaren alaƙa tsakanin ƙasashe daga jami'ar Anglia Ruskin University da ke Ingila.
  • Tsohon jami'in kwastam ne wanda ya shiga siyasa a farkon shekarun 1980.
  • Sau biyar yana yin takarar shugaban ƙasa ba tare da nasara ba; a 1993, 2007, 2011, 2015, da kuma 2019.
  • Ya kafa jami'ar American University of Nigeria, wadda ta bai wa 'yan matan Chibock tallafin karatu bayan Boko Haram ta sake su.
  • Hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ke da jari a harkokin fetur da noma da bankuna da sashen haɗa magunguna.
  • Ƙudirin sayar da kadarorin gwamnati.
  • Bai wa 'yan kasuwa ƙarin dama wajen haɓaka tattalin arziki.
  • Inganta haɗin kan ƙasa ta hanyar daidaito, da adalci tsakanin ƙabilun Najeriya.
  • Sauya tsarin tafiyar da gwamnati.

Peter Obi

Labour Party (LP)

  • Shekaru: 60
  • Gwamnan Jihar Anambra sau biyu daga 2007 zuwa 2014.
  • Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019.
  • Ɗan kasuwa ne da ya karanta fannin falsafa a Jami'ar Najeriya, Nsukka.
  • Ya kafa wata gidauniya mai kuɗi dala miliyan 156 ƙunshe da kadarori ya zuwa lokacin da ya bar gwamnati.
  • Ya sauya Anambra daga matsayi na 26 zuwa na 1 a jerin jihohin da suka fi cin jarrabawar fita daga sakandare ta NECO da WAEC.
  • Ya mallaki harkokin hada-hada da suka samar da dubban ayyukan yi.
  • Tabbatar da sa ido a aikin gwamnati da kuma yaƙi da rashawa.
  • Mayar da Najeriya ƙasa mai sayarwa maimakon mai saye.
  • Fifita rayuwar ɗan Adam ta hanyar zuba jari a ɓangaren ilimin-komai-da-ruwanka na STEM, da sashen lafiya, da kuma ayyukan raya ƙasa.

Rabiu Kwankwaso

New Nigeria Peoples Party (NNPP)

  • Shekaru: 66
  • Ministan Tsaro daga 2003 zuwa 2007
  • Gwamnan Jihar Kano daga 1999 zuwa 2003, da kuma 2011 zuwa 2015.
  • Ya wakilci Mazaɓar Madobi a Majalisar Wakilai a 1992 da kuma Mazaɓar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019.
  • Yana da digirin digirgir a injiniyanci daga jami'ar Sharda University da ke Indiya.
  • Ba da tallafin karatu da yunƙurin taimaka wa mutane.
  • Ƙara yawan ɗaliban firamare a 2011 daga miliyan ɗaya zuwa miliyan uku a 2015 lokacin da ya bar ofis.
  • Ya ƙaddamar da ciyar da ɗalibai 'yan firamare da ba su kayan makaranta kyauta.
  • Ya kafa Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil da kuma jami'ar Northwest, waɗanda su ne jami'o'in gwamnatin Kano kawai zuwa yanzu.
  • Samar da ayyuka ta hanyar zuba jari a ɓangaren noma.
  • Shawo kan matsalar tsaro.
  • Bin doka da ƙa'idar aiki.

A cewar arahoton, tarihin zaɓukan Najeriya ya nuna yadda zaɓukan ke cike da rigingimu da sauran laifukan zaɓe.

Ƙungiyar ta Human Rights Watch ta ce zaɓen Najeriya na 2015 wanda ya bai wa shugaba mai ci Muhammadu Buhari nasara a matsayin ɗan takarar jam'iyyar adawa na farko da ya yi nasara zaɓen ƙasar shi ne ake gani wanda aka yi cikin kwanciyar hankali.

To amma an samu 'yar hatsaniya a zaɓen 2019, ciki har da amfani da jami'an tsaro wajen yin barazana ga masu kaɗa ƙuri'a da kuma 'yan dabar siyasa da ke yi wa 'yan siyasa aiki.

Rahoton na Humar Rights Watch ya ce a ƙarƙashin dokokin kare haƙƙin bil'adama, wajibi ne gwamnati a matakin tarayya da kuma matakai na ƙasa su ɗauki duk matakan da suka dace wajen ganin jami'an zaɓe da ƴan jarida da kuma jami'an ƙungiyoyin masu zaman kansu ba su fuskanci kowane irin barazana ba a lokacin zaɓe.

Sai dai rahoton ya ce duk da kiraye-kirayen da ake yi kan hukumomin Najeriya su tabbatar da adalci a kan waɗanda aka kama da laifin hannu a rikice-rikicen zaɓe na baya, ƙungiyar ta Human Rights Watch ta gano cewa babu wani ci gaba da aka samu.

Ya ƙara da cewa kwamitin da rundunar sojin Najeriya ta kafa domin yin binciken zarge-zargen cin zarafi da kisan jami'ai masu alaƙa da zaɓe, an ba shi mako biyu ne kawai ya gabatar da bayanan da ya samu a watan Maris na 2019, sai dai shekara huɗu bayan haka, babu wani bayani daga gwamnati kan abubuwan da kwamitin ya gano.

A watan Janairu Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC, ta bayyana cewa za ta gudanar da zaɓukan ƙasar na 2023 a faɗin ƙasar, har da wuraren da ake fama da rikici, duk da matsalolin tsaro da ake fuskanta.

A jihjohin Arewa maso yamma, kamar Zamfara, da Katsina, ƴan bindiga na cin karensu babu babbaka tun bayan da matsalar ƴan fashin daji ta ƙazanta.

A Kudu maso gabashin ƙasar kuwa, kamar a jihar Imo, ana ci gaba da fuskantar barazanar ƴan bindiga da kuma mayaƙan IPOB, waɗanda ake zargi da kai hare-hare a kan ofisoshin hukumar zaɓen ƙasar da kuma cibiyoyin jami'an tsaro.