Matar da ta rubuta littafin 'Yadda za ki Kashe Mijinki' da aka yanke wa hukuncin daurin rai-da-rai

Nancy Crampton Brophy

Asalin hoton, Multnomah County Sheriff's Office

    • Marubuci, Daga Sam Cabral
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Washington
  • An wallafa

Wani alkali a gundumar Oregon ta yanke wa wata mata Nancy Crampton Brophy, wacce mawallafiya ce ta Romawa da ta wallafa littafin 'yadda za ki kashe mijinki', hukuncin daurin rai-da-rai a gidan yari saboda harbe mijinta har lahira da ta yi.

An sami Crampton Brophy, mai shekara 71 da laifin kisan kai a watan da ya gabata. Wasu masu taimaka wa alkali a wajen shari'a sun gano cewa ta harbi mijinta mai shekara 26 a 2018 a kan kudin inshorar lafiya na dala miliyan 1.5.

Kafin ta aikata laifin, Crampton Brophy ta kasance wata mawallafiya wacce litattafan da ta wallafa irinsu 'The Wrong Husband' da kuma 'The Wrong Lover' suka kasance masu nishadantarwa da kuma sanya kokonta a zukatan masu karatu.

Marigayin mijinta, Daniel Brophy mai dafa abinci ne sannan da yin aikin koyarwa a wata kwaleji da ke gundumar Oregon.

An same shi kwance da raunin harbi a dakin cin abinci na kwalejin a watan Yunin 2018, inda aka zargi matarsa da laifin kashe shi a watan da ya gabata.

Lamarin ya ja hankalin mutane da dama musamman ma a kan wata takarda da Crampton Brophy ta rubuta shekaru da suka wuce kan 'yadda za ki kashe mijinki' kafin ta aikata laifin.

"Abin da na sani a kan kisan-kan shi ne ko waye kan iya aikata hakan matukar aka kai shi bango," ta fada a wani saƙo da ta wallafa a shafinta kafin ta goge.

Ta ambaci jerin hanyoyin da masu aure za su bi wajen kashe abokan zamansu, ta hanyar amfani da bindiga da wuƙa zuwa guba da kuma waɗanda ake biya su aikata kisa, kafin ta wallafa littafin "abu ne mai sauƙi a yi wa mutane fatan mutuwa maimakon kashe su".

Ta ƙara da "idan mai kisan-kai yakan iya bari na, a gaskiya ba na son zama a gida yari".

Wani alkali ya yanke hukuncin ƙin amincewa da rubutun a matsayin shaida a shari'arta saboda an rubuta ta shekaru da suka gabata a mastayin wani bangare na taron karawa juna sani.

Sai dai masu gabatar da ƙara ba sa buƙatar rubutun nata.

Sun yi muhawarar cewa Crampton Brophy tana da niyya da kuma kudin kashe mijinta, inda suka nuna yadda ma'auratan suka samu sabani kan kudi, sannan ta kuma samu makudan kudaden inshora bayan mutuwarsa.

Daniel Brophy

Asalin hoton, Daniel Brophy/LinkedIn

Wani hoton bidiyo a kotu ya nuna Crampton Brophy na kai wa-da-kawowa a mota zuwa cibiyar da mijinta ke koyarwa lokacin da aka aikata kisan kan.

Duk da cewa 'yan sanda ba su sami makamin da mai kisan ta yi amfani da shi ba, amma an ga lokacin da ta sayi bindigar.

Da take tsaye a gaban kotun domin kare kanta, mawallafiyar ta ce ta samu matsalar ''manta abubuwa'' daga safiyar da aka same shi a mace.

Sai dai ba ta musanta cewa ita aka gani tana tuƙa mota zuwa cibiyar ta gundumar Oregon ba.

Wasu masu taimaka wa alkali 12 sun same ta da laifin kisan-kai bayan muhawara ta akalla kwana biyu.

Hukuncinta na ɗaurin rai-da-rai da aka sanar ranar Litinin na dauke da damar yi mata afuwa bayan shekara 25. Sai dai lauyoyinta sun ce suna shirin daukaka ƙara.

Gabanin yanke hukuncin, iyalai da 'yan uwa na tsohon mai dafa abincin sun gabatar da jawabai.

"Ƙin yanke shawarar yin kariya da zamba da sata da kuma kashe mutumin da ya kasance babban abokinki, cewar Nathaniel Stillwater, ɗa ga Brophy, wanda ya haifa da wata tsohuwar matarsa ta baya.