Yakin Ukraine zai haddasa yunwa a duniya - MDD

Antonio Guterres (left), Anthony Blinken (right)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Antonio Guterres ya ce mamayen da Rasha ke yi a Ukraine ne ya kara tsananta matsalar karancin abincin
An wallafa

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa yakin da ake yi a Ukraine yana kara jefa duniya cikin hadarin karancin abinci da kuma yunwa a watannin da ke tafe.

Da yake magana a taron kolin Majalisar a New York, Antonio Guterres ya ce kutsen na Rasha, ya sake ta'azzara matsalar karancin abinci, wadda daman tuni matsalar karuwar yanayin zafi a duniya da kuma annobar korona suka shafa.

Majalisar ta ce a cikin shekara biyu kadai yawan mutanen da ke fama da karancin abincin ya ninka biyu daga miliyan 135 zuwa miliyan 276, a yau.

Cibiyoyin kudi na duniya, da suka hada da Bankin Duniya sun sanar da bayar da tallafin biliyoyin dala domin sassauta lamarin.

gona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun a baya shugaban Bankin Duniya David Malpass ya yi gargadin cewa yakin da Rasha ke yi a Ukraine zai haddasa karancin abinci a duniya

Mista Guterres ya gaya wa mahalatta taron cewa ba wata hanya managarciya ta shawo kan wannan matsala ta yunwa a sakamakon karancin abincin, da ta durfafo ba tare da an shigar da bangaren samar da abinci na Ukraine ba, hadi kuma da takin zamanin da Rasha da kuma Belarus ke samarwa a kasuwanni ba, duk da yakin da ake yi.

A tsakaninsu, Ukraine da Rasha suna samar da kusan kashi daya bisa uku na yawn alkamar duniya.

Babban Sakatare ya matsa sosai a kokarin da yake na ganin an bayar da wat dama ta fitar da kayan abinci a tsanaki ba tare da wata matsala bad aga Ukraine ta kasa da kuma ta ruwa.

Alkama

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban shirin samar da abinci na Majalisar ta Dinkin Duniya, David Beasley ya yi gargadin cewa muddin aka ki bude tashoshin jirgin ruwa na Ukraine, to hakan na nufin kaddamar da yaki a kan samar da abinci a duniya, wanda hakn zai kai ga haifar da yunwa, da sabauta al'amuran kasashe da kuma gagarumar kaurar gama-gari ta jama'a

Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken - wanda ke shugabantar taron na samar da abinci, ya zargi Rasha da laifin ta'azzara matsalar, wadda daman tuni annobar korona da ta dumamar yanayi suka kara.

Mista Blinken, ya ce akwai bukatar kasashen duniya su gaggauta dukar mataki domin fuskantar matsalar:

Ya ce, ''muna bukatar kasashe da su himmatu da bayar da sabbin karo-karo mai yawan gaske domin cike gibin da kungiyoyin agaza wa jama'a da hukumomi da key ki da karancin abinci ke fuskanta.

Sakataren wajen Amurkar ya ce akwai kiyasin tan miliyan 22 na alkama da sauran nau'ukan hatsi jibge a rumbunan Ukraine a yanzu haka.

Wanda abinci ne da zai iya kaiwa kai tsaye ga taimakon wadanda ke bukata idan da za a fitar da shi daga kasar.

Ya bayar da misalin alkaluman Bankin Duniya, da ke nuna cewa yakin na Ukraine zai iya jefa karin mutum miliyan 40 cikin tsananin talauci da karancin abinci a shekarar nan.