FGC Yawuri: Wata 11 babu duriyar 'yan matan sakandaren Kwalejin Tarayya

A ranar Litinin ne ragowar ɗaliban sakandiren Yawuri a jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya ke cika wata 11 a hannun 'yan fashin daji.
A tsakiyar watan Yunin bara ne 'yan fashin daji suka auka Kwalejin Tarayya ta Yawuri, kuma suka yi awon gaba da gwamman ɗalibai.
Sai dai kuma 'yan fashin da suka yi garkuwa da ɗaliban sun saki dukkan mazan da ke hannunsu amma suka ci gaba da riƙe wasu 'yan mata.
'Gwamnati ba ta komai kan ceto yaranmu'
Jiya Lahadi da yamma iyayen ɗaliban sun gudanar da taro game da wannan lamari, kuma ɗaya daga cikinsu ya fada wa BBC cewa har yanzu basu debe tsammanin sake haduwa da ya'yan nasu ba.
Cikin yanayi na damuwa da takaici, daya daga cikin iyayen yace ''ana rana ana hunturu ana ruwa ana zafi yarannan na hannun barayi saboda Allah.''
Mahaifin ya kara da cewa suna zargin cewa babu abunda gwamnatin Jihar Kebbi ke yi don ganin ta kwato musu 'ya'yansu hannun yan bindigar.
Da ya ke magana kan gwamna Atiku Bagudu mahaifin ya ce ''shi Atiku Bagudu da ya yi alkawarin cewa zai kubutar da yaran gaba daya idan mun tuntube shi ta waya ma baya daukar wayarmu.''
''Ainihin wanda ya hada mu dashi wanda dashi ake zuwa daji lokacin ya nuna mana cewa ba batunmu yake ba, kuma ya kira shi ga waya ma baya dauka.'' In ji mahaifin.
Akan haka ya ce suka sake zama wasu wasu iyaye, don su sake lale, kuma su samu tabbaci daga gwamnati cewa ta gaza don su daina dogara gare ta.
Ina matsalar take?
A cikin watan Janairu ne hukumomi a jihar Kebbin suka tabbatar wa da BBC cewa 30 daga cikin daliban da malami ɗaya sun kubuta daga hannun 'yan bindigar.
Kuma a lokacin sun shaida wa BBC cewa an kubutar da daliban ba tare da an biya kudin fansa ba.
Kazalika sun tabbatar cewa har yanzu akwai sauran daliban da ke hannun 'yan bindigar, wadanda su ma ake sa ran kubutar da su nan ba da jimawa ba, a cewar hukumomin.
To amma har yanzu babu dauriyar sauran daliban da hukumomin basu tabbatar da adadinsu ba.
Satar ɗaliban domin neman kuɗin fansa kusan ya zama ruwan dare a Najeriya, musamman arewacin ƙasar.
Wannan na daga cikin dalilan da masana ke cewa na tasiri ko kassara ilimi a wasu yankunan arewacin, saboda fargabar tura yaro makaranta.
Kuma wani abin damuwa shi ne gaggara gane ina matsalar take, musamman wajen ceto mutane ko daliban da ake garkuwa da su.
Mahukunta Najeriya dai na yawaita cewa suna daukan matakai, sai dai a galibin lokuta hare-haren 'yan bindiga na zuwa wa mutane ne babu tsanmani a lokutan da ake tunani sauki ya soma samuwa.










