Antonio Guterres zai gana da shugaba Buhari na Najeriya

Asalin hoton, BSGH
A ranar Laraba ne ake sa ran Sakatare Janar na Majalasar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, zai gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a yayin ziyarar da ya kai kasar.
Sai da babban jami'in na Majalisar Dinkin Duniyar ya fara kai ziyara Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda ya gana da Gwamna Babagana Umara Zulum, da kuma iyalan mutanen da rikicin Boko Haram ya yi sanadin rasa rayukansu.
Fadar gwamnatin Najeriya dai ta bakin mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ta shaida wa BBC cewa suna maraba da wannan ziyara ta Antonio Guterres.
Malam Garba Shehu ya ce sai babban jami'in ya isa fadar gwamnatin Najeriya sannan zai yi bayani a kan abin da kawo shi, domin su ba su san batutuwan da ya zo da su ba.
Ya ce "Kunnenmu a bude yake idan ya zo sun gana da shugaba Buhari kamar yadda aka tsara, sannan ya yi bayani a kan gudunmawa ko kuma karin gudunmawar da Majalisar Dinkin Duniya take ganin za ta bai wa Najeriya a kan halin da take ciki na matsalar tsaro."
Malam Garba Shehu ya ce ba mamaki baya ga gudunmuwa, jami'in zai iya janyo hankalin kasashen duniya masu arziki su zo su ba da nasu tallafin, saboda gwamnatin tarayya ita kadai ba za ta iya ba, bisa la'akari da yadda matsalar tsaro ta jefa yankuna da dama na Najeriya cikin ƙunci.
Ana sa ran Sakatare Janar din zai kuma gana da shugabannin addinai da na kungiyoyin mata da matasa da kuma shugabannin kamfanoni masu zaman kansu.
Baya ga wadannan mutane da zai gana da su, zai kuma gana da jami'an difilomasiyya.
Kafin ya kai ziyara Najeriya, sai da ya je Jamhuriyar Nijar ya gana da shugaban kasar Muhammed Bazoum, inda har ya yaba da irin kokarin da jami'an tsaron kasar ke yi wajen yaki da masu tayar da kayar-baya.
Kazalika, ya yi kira ga kasashen duniya su taimaka wa sojojin Jamhuriyar Nijar ɗin domin yaki da masu tayar da kayar-baya da suke yawan kai hare-hare a kasar.
A yayin da jawabi lokacin ziyararsa a Niamey babban birnin kasar, babban jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rikicin da ke faruwa a yankin Sahel ya zama babbar barazana ga duniya.
Antonio Guterres ya kara da cewa Jamhuriyar Nijar ba za ta iya tunkarar matsalar masu ikirarin jihadi ita kadai ba kuma ya yi kira ga wasu kasashe su taimaka mata da horaswa da kuma kayan yaki.










