Mansiya VP: Musulmar da 'yan Hindu suka nuna wa wariya kan kwaikwayon rawarsu

Mansiya VP

Asalin hoton, Mansiya VP

Bayanan hoto, Iyayen Mansiya sun karfafa mata gwiwa domin ta koyi rawa
    • Marubuci, Daga Sharanya Hrishikesh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC, Delhi
  • An wallafa

Mansiya VP tana shekara uku lokacin da mahaifiyarta ta shigar da ita Bharatanatyam, wani nau'in rawar gargajiya mai tsawon tarihi da ya samo asali a wuraren ibada.

Wani zaɓi da ba a saba gani ba ga ƴar Musulma daga Malappuram, gundumar da ke kudancin jihar Kerala.

Amma Amina, mahaifiyar Mansiyya a shirye take.

Ƴaƴanta biyu mata ba wai kawai rawar Bharatanatyam suka koya ba, har sauran raye-raye na gargajiya kamar Kathakali da Mohiniyattam.

Ba abu ba ne mai sauƙi - masu riko da addinin Musulunci a yankin sun ce bai dace mace ta koyi salon "raye-rayen Hindu ba." Iyalin sun sha jan hankali a kafofin yaɗa labarai.

A makon da ya gabata - shekara 24 bayan ta yi rawar Bharatanatyam - Masiya ta sake daukar hankali a kafofin watsa labarai. A wannan karon, saboda wani sakon da ta wallafa a Facebook da ya ja hankali bayan an hana ta yin rawa a bikin shekara-shekara da aka saba yi.

Dalili: saboda ita ba 'yar addinin Hindu ba ce.

Masu shirya gasar da farko sun karɓi buƙatarta ta shiga gasar, amma hukumomin wurin ibadar da suka hana ta yin rawar, sun kare matakinsu, suna masu cewa dole su bi al'ada.

Lamarin ya zama wani al'amari da ya ja hankali sosai.

Amma Masiya da ba ta karaya ba ta rubuta wani sako cewa: "Na kawo nan bayan fuskantar wariya mafi muni, wannan ba komai ba ne a gare ni."

Ƙalubalen farko

"Mun fuskanci ƙalubalen kuɗi amma muna cike da farin ciki," Mansiya - yanzu ƴar shekara 27 kuma take digiri na uku kan Bharatanatyam - ta yi bayani kan ƙuruciyarta.

Rawa ta shiga rayuwarsu ne bayan mahaifiyarta ta wani rawa a talabijin ya burge ta.

Ta samu goyon bayan mijinta VP Alavikutty, wanda a lokacin ke aiki a Saudiyya, Amina ta kai Mansiya da yayarta Rubiya koyon rawa kuma tare da tabbatar da sun ƙware.

Rayuwarsu ta rabu tsakanin makaranta da rawa da karatun addini - Amina mai bin dokokin addinin Musulunci ce. Mr Alavikutty, wanda ya dawo Kerela lokacin Mansiya ke ƙarama, bai damu da addini ba amma ba shi da matsala da matarsa ko kuma addinin ƴaƴansa.

A kullum bayan makaranta a ƙarshen mako, iyalin sukan ɗauki mota zuwa wurin malaman koyar da rawa a Kerala - inda Mansiya da Rubiya suka koyi kusan nau'in rawa iri shida.

Wani lokaci tafiyar da suke yi tana da nisa sosai sukan wuce unguwanni da dama a rana ɗaya.

"Akwai wahala, amma mun saba, ina jin daɗi," in ji Mansiya

Mansiya da iyayenta

Asalin hoton, Mansiya VP

Bayanan hoto, Mansiya da iyayenta

Ƴaƴan sun fara rawa a wurin ibada lokacin wasan yara - wuraren da ake bikin rawa a Kerela.

Amma rikici ya fara lokacin da kwamitin masallaci suka fara adawa.

Bayan haka, Mansiya ta ce, mambobin kwamitin da malaman islamiyya za su tambayi yara mata su yi alƙawalin ba za su taɓa yin rawa ba.

Mansiya, ta yi ƙarama a lokacin ta fahmci hakan, za ta amince, amma Rubiya za ta dawo gida tana kuka.

Amma Amina da Mr Alavikutty za ta jaddadawa ƴaƴansu cewa za su ci gaba da yin rawa.

"Ban san yadda suka yi ba, amma ba su taɓa nuna muna ɓacin ransu ba," in ji Mansiya.

Mr Alavikutty - wanda ya yi wasan kwaikwayo a titi lokacin da yana ƙarami - ya ce sun amince ne saboda sun san ba su yi wani abu marar kyau ba.

Amma abubuwa sun ƙara yin muni bayan an gano Amina tana da ciwon kansa a 2006.

Yayin da Mr Alavikutty ke ƙoƙarin samun kuɗin magani, Mansiya ta ce tayin tallafi daga ƙasar waje ya gamu da cikas saboda kwamitin Masallaci - waɗanda ke fushi da burinta na yin rawa - sun ki amincewa da buƙatarsu.

"Nakan tafi da mahaifiyata kullum ina neman taimakon sauran mambobi," in ji Mansiyya.

"Halin da ta shiga, a cewarta ya sa ta fara sauya tunaninta kan addini.

Lokacin da Amina ta rasu a 2007, Mansiya ta ce an hana ta wurin da za su binne ta a makaɓarta.

Shekaru na gaba sun kasance cikin kaɗaici da ƙalubale - musamman bayan Rubiya ta bar gida zuwa karatu a jihar Tamil Nadu - amma burin Mansiya na rawa na nan tare da samun goyon bayan mahaifinta.

Rarrabuwar addini

Rikicin addini na Indiya sau da yawa yana haifar da sabani - binciken Pew na 2021 ya gano cewa yawancin mutane a cikin addinai suna goyon bayan jurewa na addini da kuma wariyar addini.

Mansiya ta tabatar da haka da ita da Rubiya - da ake kira "ƴaƴan VP" - "sun yi rawa a wurare da dama a yankin Malappuram". Sun yi farin jini a ko ina.

Abu ɗaya da ba za ta manta ba shi lokacin da mambobin kwamiti suka ƙi amincewa da su saboda su Musulmai ne.

"Amma bayan mun yi rawa, abin ya ja hankalinsa ya zo ya rungume mu," in ji ta.

Lokacin da Koodalmanikyam suka nemi ta tura buƙatarta yankin Thrissur, ta tuntuɓi masu shirya bikin waɗanda suka ce ta tura bayananta. Da ta nemi irin bayanan da suke buƙata, ya bayyana kamar bayanan da suka shafi rawa, ba a ambaci addini ba, in ji Mansiya.

Ta kwashe tsawon makwanni tana atisaye lokacin da masu shirya bikin suka kira suka shaida mata cewa ba ta cikin waɗanda za su yi rawar domin shugabannin wurin ba su amince da wanda ba Hindu ba ya shiga.

Yawanci wuraren Hindu ana barin mabiya waɗansu addinai shiga su yi ibada, amma sun jaddada cewa ƴan Hindu ne kawai za su iya wuce wuraren da ake addu'o'i.

Mansiya VP

Asalin hoton, Mansiya VP

Bayanan hoto, Iyayen Mansiya sun karfafa mata gwiwa domin ta koyi rawa

Bayan haka ne, shugabannin addinin suka ki amincewa da bukatar Mansiya saboda za su "bi da kuma aiwatar da al'adun da aka saba da su".

Ta samu goyon bayan 'yan siyasa da mawaka - mawakan Hindu uku sun janye daga bikin kwana goma da za a yi nan gaba domin nuna masa goyon baya.

Iyaye da 'yan uwanta suma sun mara mata baya - ciki har da surukanta mabiya addinin Hindu, wadanda kan je wuraren bauta akai-akai.

Mr Alavikutty bai damu da abin da ya faru ba - ya ce wani abu ne "da ba shi da muhimmanci", a cewarsa, idan aka kwatanta da abubuwan da suka yi fama da su.

Mansiya ta ce ta wallafa batun a Facebook ne saboda dalili guda daya.

"Idan ko da mutum daya ne ya karanta shi kuma ya fahimci cewa harkar raye-raye ba ta nuna bambancin addini, zan yi matukar farin-ciki."

Presentational grey line