Me ya sa ake ce-ce-ku-ce kan komawa dogaro da man Saudiyya?

Boris Johnson in Saudi Arabia

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya kare balaguron da ya yi zuwa Saudiyya, yana mai cewa ana buƙatar "babban ƙawance" domin kawo ƙarshen dogaro da man Rasha da kuma gas.

Amma ƙarfafa hulɗa da ƙasar na cike sarƙaƙiya musamman daga maso sukar ƙasar kan keta haƙƙin ɗan Adam.

Me ya sa man Saudiyya ke da muhimmanci?

Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun sanar da cewa za su daina sayen mai da gas na Rasha saboda abkawar da ta yi wa Ukraine. Amma farashin ya tashi sama.

Saudiyya ita ce wadda ta fi fitar da mai a cikin ƙungiyar Opec kuma za ta iya taka rawa wajen rage farashi ta hanyar kara yawan man da take fitarwa

Hakan na nufin ƙasahen yammaci na buƙatar yarda da ci gaba da inganta amince tsakaninsu da gidan masarautar Saudiyya.

Amfani da hukuncin kisa

Saudiyya tana cikin ƙasashen da ke zartar da hukuncin kisa.

A watan Maris ta zartar wa mutum 81 hukunci a rana ɗaya - fiye da adadin da ta zartar a bara. An same su da "munanan laifuka" da suka hada da ta'addanci da garkuwa da mutane da fyade, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Saudiyya SPA ya ruwaito.

Hukumomin kare haƙƙin ɗan Adam sun ce da dama ba a yi masu shari'ar adalci ba a Saudiyya. Zargin da gwamnati ta musanta.

Kisan ɗan jarida mai adawa

Martabar Saudiyya ta ragu sosai sakamakon kisan ɗan jarida Jamal Khashoggi a 2018, ɗan jarida da ke zaune a Amurka wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar gwamnarin Saudiyya.

Ƙwararriya kan kare haƙƙin ɗan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya Agnes Callamard ta ce jami'an Saudiyya "sun yi amfani da hanyoyi na gwamnati wajen kisan Khashoggi" a ofishin jekadancinta a Santabul.

An tuhumi Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman da wasu manyan jami'an Saudiyya da bayar da umarnin kisan. Kuma duk da Yariman mai jiran gado ya musanta amma ƙimarsa ta zube.

Ɗaure mata masu gwagwarmayar ƴancin mata

Saudi activist Loujain al-Hathloul is pictured on her way to the state security court in the Saudi capital Riyadh on March 2, 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An saki Loujain al-Hathloul a watan Fabrairu bayan ta shafe kusan shekara uku a tsare

A 2018, hukumomin Saudiyya sun kama mata ƴan gwagwarmaya 13 waɗanda suka jagoranci gwagwarmayar soke haramta wa mata tukin mota.

Aƙalla mata huɗu daga cikinku ana zargin an ci zarafinsu tare da azabtar da su.

A 2020, kotu ta musamman kan ayyukan ta'addanci ta samu Loujain al-Hathloul da laifuka na cin amanar ƙasa.

Bayan kotun ɗauka ta tabbatar da hukuncin, ƙungiyar Amnesty International ta ce "yadda Saudiyya ta ƙi wanke Loujain al-Hathloul, hakan ya nuna hukumomin ƙasar sun ɗauki gwagwarmaya ta lumana a matsayin aikata laifi.

Murƙushe masu ilimi da malamai da masu neman sauyi

Areej al-Sadhan her brother Abdul Rahman's graduation

Asalin hoton, Areej Al-Sadhan

Bayanan hoto, Areej al-Sadhan ta ce an azabtar da dan uwanta Abdul Rahman kafin a daure shi tsawon shekara 20

Ba mata ƴan gwagwarmayar tabbatar da ƴan mata ne aka kama ba a Saudiyya inda aka haramta jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyi masu zaman kansu na hare haƙƙin ɗan adam.

Gomman ƴan gwagwarmaya da malaman boko da na addini da masu rajin tabbatar da sauyi ne aka kama tun 2017, saboda sun gudanar da ƴancinsu na faɗin albarkacin baki, kamar yadda hukumomin kare haƙƙin ɗan adam suka bayyana.

Da dama sun fuskanci abin da ƙungiyar Amnesty ta bayyana rashin adalci a shari'ar da aka yi masu kan laifukan ta'addanci da hukunci mai tsari da ya kunshi har da hukuncin kisa.

Kwanaki kafin sayen Newcastle, kotu ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara 20 kan wani ma'aikacin agaji Abdul Rahman al-Sadhan kan sakon da ya wallafa na raha yana kalubalantar hukumomi.

Yaƙin Yemen

A man walks through the remains of a building destroyed in a Saudi-led coalition air strike in rebel-held Sanaa, Yemen (7 October 2021)

Asalin hoton, EPA

Ana caccakar Saudiyya kan yakin da take yi a maƙwabciyarta Yemen wanda ya haifar da mummunan ayyukan jin-kai a ƙasar.

A 2015 ƙawancen ƙasashe da Saudiyya ke jagoranta suka abka wa Yemen bayan ƴan tawaye sun ƙwace kusan yammacin ƙasar tare da tilastawa shugaban ƙasar tserewa.

Sama da mutum 100,000 rahotanni suka ce an kashe a faɗan Yemen.

Dubbai kuma sun mutu ta dalilin matsololi da suka shafi rashin abinci da lafiya da wasu buƙatu na yau da kullum. Matakin da ƙawancen ya ɗauka ya hana isar da taimako da mutum miliyan 20 da ke buƙatar agajin gaggawa.

Kwararru a Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce dukkanin ɓangarorin sun aikata laifukan yaƙi, ko da yake ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta ya nanata cewa ya kiyaye dokar yaƙi.

Hukunta masu auren jinsi

Duk da Saudiyya ba ta da wata doka kan jinsi, amma duk wata hulɗa bayan aure, da ya haɗa da luwaɗi da maɗigo haramtacce ne a ƙasar.

Ƙarƙashin shari'ar musulunci a ƙasar, za a iya yanke wa ƴan maɗigo da luwaɗi hukuncin kisa.

Haka kuma an haramta wa namiji ya mayar da ɗabi'unsa na mata ko kuma mace ta saka kayan maza.

A watan Yulin 2020 wata kotu ta taba yanke wa wani ɗan Yemen hukuncin ɗaurin wata 10 a gidan yari kan wallafa wani bidiyon da ke kiran ƴancin daidaito da ya hada har da na ƴan luwaɗi.