Tarihin Timbuktu: Dadaddun takardun Musulunci na Mali da aka wallafa a intanet

Asalin hoton, Google Arts and Culture
- Marubuci, Daga Nomsa Maseko
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa

An kaddamar da wani kudin nuna zane-zane don baje-kolin tarihin al'adun gargajiya na kasar Mali, wanda ke nuna dubban kasidu na dadadden tarihi.
An yi fasa-kwaurin takardun don tserar da su daga birnin Timbuktu, bayan da kungiyar masu tsattauran addinin Islama ta karbe ikon arewacin Mali a shekarar 2021.
Sun kunshi ilimin Afrika na karni da dama da kuma darussa da malanta kan batutuwa kama daga lissafi zuwa zane-zanen hatiman ilimin bokanci.

Asalin hoton, Google Arts and Culture

"Mafi matukar muhimmancin abu ga al'adun gargajiyar kasar Mali, suna nuna babban abin tarihi na sani a rubuce da kuma ingantaccen ilimi a Afirka,'' in ji Dakta Abdel Kader Haidara, wani mai kula da dakunan karatu da ajiyar litattafai da aka bayyana ya yi fasa-kwaurin rubutattun takardun zuwa wajen birnin Timbuktu, wanda kuma yana cikin wadanda suka gudanar da aikin.
Tarin takardun, da ake kira 'Mali Magic', sun kuma fito da al'adun gargajiya na kasar Mali da ya wuce batun rubutattun takardun.
Kamfanin nan mamallakin shafin intanet din matambayi ba ya bata wato Google ne ya hada su wuri guda, tare da hadin guiwar abokan hudda na cikin gida da kasashen waje.
Ya kunshi hoton rawar al'adun gargajiya ta kungiyar kabilun Dogon. Ya kuma nuna fasahar zane, kamar na Abdoulaye Konaté da ya samu lambar yabo, da wasu hotunan magina suna yi wa Babban Masallacin Djenné yabe.
Masallacin dai wani wurin tarihi da hukumar kula da layan tarihi ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO mai nisan kilomita 500 (mil 310) daga kudancin birnin Timbuktu.

Asalin hoton, Brian David Melnyk/ Google Arts and Culture

Asalin hoton, Google Arts and Culture


Asalin hoton, Google Art and Culture
Asalin dadaddun takardun an rubuta su ne da harshen Larabci na tsakiyar zamani, amma yanzu an fassara su zuwa harsunan Turanci, da Faransanci, da Spaniyanci da kuma Larabcin zamani, don mutane da dama su iya karantawa, abinda Manajan Tsare-tsare da ilimin kimiyya tarihi na kamfanin Google Coughenour ya shaida wa BBC shi ne ab una farko.
"Tattara bayanai a rubuce ta hanyar fasahar zamani da kuma kwafin rubutattun kasidun na da matukar muhimmanci, kana a karon farko muna fito da sakamakon ayyukan da muka yi ta fafutikar yi na tsawon shekaru,'' ya ce.
A cikin karni da dama, birnin Timbuktu ya kasance wata babbar cibiyar kayan tarihi a nahiyra Afirka, har ma da kasancewa cibiyar ilimin addinin Islama.
Masallatan birnin sun taka muhimmiyar rawa wajen yada addinin Musulunci a fadin yankin Afirka ta Yamma a cikin karni na 15 da na 16, kamar yadda hukumar UNESCO ta bayyana.
Cikin shekaru bakwai da suka gabata shugabannin gargajiya na kasar Mali, da masana tarihi, da kuma masu bincike kan kayan tarihi na zamani sun yi da aiki tukuru wajen tabbatar da ganin cewa dadaddun kasidun, da wasu tun a cikin karni na 11 aka rubuta su, kunshe da ingantattun tarihin kasar sun alkinta su ta hanyar tattara su wuri guda a zamanace.
Aikin ya bai wa mutane damar da za su yi koyi da wadanda suka gabace su, in ji Dakta Haidara (hoto na kasa).

Asalin hoton, Google Arts and Culture

Mayar da wadannan rubutattun kasidu zuwa cikin kundin fasahar zamani ya samo asali ne daga yin kira da kamfanin Google da Dakta Haidara ya yi a shekarar 2014.
Ya gayyaci kamfanin ne ya ziyarci kasar Mali don ya ga mashahuran kasidun birnin Timbuktu kana ya san dalilan da suka sa suke cikin hadari ko kuma barazana.
Lokacin da suka isa birnin, sun gano rubuce-rubuce da suka hada da littattafan Alkur'ani mai girma na farko da kuma wasu batutuwa daban-daban da suka hada da na ilimin taurari, da lissafi da kuma ilimin kimiyyar kasa.
Daga nan ne tawagar ta kudirin gudanar da aiki ba kawai na duba daruruwan shafukan don mayar da su cikin kundin fasahar zamani kadai ba ne, amma har da saka hotunan a shafin intanet.
Yanzu za a iya samun shafuka 40,000 a shafin yanar gizo, da ke kunshe da batutuwa da dama da suka hada da kimiyyar ilimin halittu da wakoki.

Asalin hoton, Google Arts and Culture

Asalin hoton, Google Arts and Culture

Aiki ne da 'yan kasar Mali suka shafe shekaru da dama suna sa ido a kai, tun bayan da mayaka masu kaifin kishin Islama suka bank awa dakunan ajiyar litattafai wuta a birnin Timbuktu a yayin da suke kokarin kone takardu masu daraja.
A cikin watanni shida aka yi fasa-kwaurin tarin rubutattun kasidun daga cikin Timbuktu zuwa Bamako babban birnin kasar Mali, saboda lokaci na kurewa na kokarin cetowa tare da adana takardun daya lalatarwa.
A shekarar 2016 Kotun Hukunta masu Aikata Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ICC ta yanke wa wani ake zargi dan kungiyar masu tsattsauran addinin Islama ne, Ahmad Al Faqi Al Mahdi, da aikata laifin bayar da umarnin kai hare-hare a kan gine-ginen addini da na tarihi a Timbuktu hukuncin daurin shekaru tara a gidan yari tare da neman gafara.
Shi ne karon farko da kotun ta ICC da ke birnin Hague ta yanke hukunci kan lalata wuraren tarihi.

Asalin hoton, Google Arts and Culture

Amma kuma, wannan aiki na alkinta muhimman kasidun kasar Mali ba shi ne yunkuri a karon farko ba.
A shekarar 2003 n3 Jami'ar Cape Town ta kaddamar da aikin alakinta takardun Tombouctou, tare da jaddada "al'adun rubutattun kasidu a fadin nahiyar Afirka", kamar yadda shafin yanar gizon ya nuna.
Har ila yau, dakin ajiyar litattafai na Amurka US Library of Congress ya saka wasu daga cikin wadannan takardu a shafin intanet.
Dukkan hotunan na da hakkin mallaka.











