Nijar: Dabbobi na cikin tsa-ka mai wuya a Nijar saboda yunwa

A Jamhuriyar Nijar, wasu shugabannin Fulani ne suka fara kira ga takwarorinsu makiyaya, su sayar da rabin dabbobinsu, su sai abincin dabbobi don kauce wa yunwa.
Sun ce duk da tallafin mahukunta da na ƙungiyoyi da suke sa ran samu, amma halin ƙarancin abincin dabbobi da aka shiga tun a yanzu, babban abin fargaba ne.
Koini Maje, wani jagoran makiyaya daga yankin Bermo, ya shaida wa BBC cewa, yawan wutar dajin da aka samu a yankin na cikin manya dalilan da suka haifar da wannan matsala.
Ya ce, gobarar da aka yi a yankin Bermo ita ta cinye rabin dajin yankin abin da ya haifar da karancin abincin dabbobin ke nan.
Koini Maje, ya ce" A yanzu abincin da ke cikin gonaki duk ya kare abin da ya sa makiyaya suka koma gida suka zauna kenan, to a gida kuma ga hatsi na tsada don haka dole dusa ma tayi tsada, sannan 'yan kasuwa ma kansu na kara kudin abubuwa".
Makiyayin ya ce, a dajin da aka yi gobarar duk rabin ciyawar da ke wajen ta cinye saboda wuta.
"Don haka shi ne muke kira ga manya-manyan kungiyoyi kamar su Aren da Kapan da kuma Ropen, da kuma kungiyoyin da ke bayar da dusa da su taimaka wajen samar wa da dabbobi da abincin da za su ci," in ji Koini Maje.
Ya ce, " Abin takaicin ma shi ne ga farashin dusa ya tashi a kasuwa a wajejenmu, kuma dusar da gwamnati ta kai dauki wuraren da ake da karancin abincin dabbobin kadan ne bai wadatar da".
Jagoran makiyayan, ya kuma yi kira ga 'yan uwansa makiyaya da su zauna a wurarensu, sannan su adana dabbobinsu.
Ya ce," Babbar shawarata a nan ita ce makiyaya su sayar da rabin dabbobinsu su sayi abincin dabbobi ga sauran, shi ne mafita".
Makiyayin ya ce, da asara gara gidadanci, ma'ana da mutum ya yi asarar dabbobinsu duka saboda yunwa gara ya sayar da wasu ya siy awa sauran abinci don su rayu.
Ya ce kiwo irin na da ba kamar na yanzu bane, don duk abubuwa sun canja, saboda haka dole makiyaya su fahimci haka sai a zauna lafiya in ji Koini Maje.











