Fulani Makiyaya na kuka don a kai musu ɗauki a Kudancin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Wasu al'ummar Fulani Makiyaya da aka kora daga garin Igangan na jihar Oyo da ke kudancin Najeriya a bara, da yanzu haka ke gudun hijira a wasu wuraren na kukan neman taimako.
Makiyayan sun ce har yanzu suna cikin mawuyacin hali, kuma babu wani tallafi da aka kai musu.
Al'amarin dai ya tilasta wa da dama daga cikinsu yin barace-barace don samun abin da za su ci.
A watan Janairun shekarar da ta gabata ne aka kai wa Fulanin harin a rugagensu tare da kashe wasunsu da dabbobinsu da kona masu gidaje.
Shekara guda bayan harin da aka kai wa Makiyayan, a Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa ta arewa a jihar Oyo, har yanzu rayuwarsu tana cikin babbar matsala, a cewar Aliyu Dan Sarkin Fulanin jihar Oyo.
Ya ce har yanzu ba su da takamaiman wuri guda na zama, 'ya'yansu ba sa zuwa makarantar boko, babu makarantar allo wasu kafin su samu abinci matsala ce, wasu ma tun da aka yi abin, ba a san inda suke ba.
"Sana'o'in da muke yi a baya babu wadanda ba su da makwanci, amma a yanzu a masallaci mu ke kwana, wasu sai sun yi bara sannan suke samun abin kai wa bakin salati," in ji shi.
Dan Sarkin Fulanin na jihar Oyo ya kara da cewa, duk da wannan hali da suke ciki, har yanzu ba wani labarin tallafi da zai rage masu radadi matsanancin halin ƙunci da suka tsinci kan su.
Ya ce an kai mana wannan hari ne babu shiri an tarwatsa rayuwar wadanda, ba su ji ba, ba su gani.
Gwamnatin jiha ko tarayya ko karamar hukuma babu wani tallafi da suka ba mu, mun dai ji a rediyo an ce za a yi mana amma babu komai da muka gani yau shekara guda.
A bara ne dai wasu gungun wasu mutane suka kaddamar da hari a rugagen Makiyayan. Al'amarin da Aliyu Dan Sarkin Fulanin na jihar Oyo, ya ce ya haddasa masu asara mai dimbin yawa.
Makiyayan dai sun dage da jadada cewa su dai adalci suke nema.
BBC ta yi kokarin ji ta bakin Dakta Wasiu Olatunbosun, kwamishinan yada labarai na jihar Oyo, sai dai ya shaida mata cewa ba zai iya kara wani abu a hukumance kan wannan batu ba.
Rahotanni dai sun ce, an kai wa makiyayan wannan harin a bara a matsayin wani martani, game da hare-hare da miyagun laifuka da ake zargin wasunsu na aikatawa a yankin na Igangan.
Zarge-zargen da shugabannin makiyayan suka musanta, kuma suke nuni cewa, bai kamata a yi masu jama'u ba, musamman ma kasancewar sun kwashe shekara fiye da sittin suna zaune da al'ummomin yankin cikin kwanciyar hankali.











