Fulani na cikin tashin hankali a kudancin Kaduna - Ruebe Fulbe

Fulani Makiyaya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ana yawan zargin 'yan ƙabilar Fulani da kai hare-hare da sace mutane don neman kuɗin fansa a arewacin Najeriya
An wallafa

Wata ƙungiyar bunƙasa rayuwar matan Fulani a Najeriya mai suna Rueɓe Fulɓe, Global Rights and Development Initiatives, ta koka kan abin da ta kira ƙuntatawa da ci gaba da kashe-kashen wasu Fulani da ba su ji ba ba su gani ba a wasu sassan ƙasar.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati ta ɗauki ƙwararan matakai don kare rayuka da dukiyar al'ummar Fulani.

Hafsat Adamu da ake yi wa laƙabi da Batunga, ita ce shugabar ƙungiyar reshen jihar Kaduna kuma a tattaunawarsu da Yusuf Tijjani ta ce yanayin da Fulani ke ciki musamman a Kudancin Kaduna ya kai intaha.

"Kuka muke kullum ba a jin kukanmu, mu mun rasa ma yadda ake so a yi da Fulani a ƙasar nan, ba a kudu ba, ba a arewa ba, ba a gida ba, ba a waje ba," in ji ta.

"Abubuwan da ke faruwan nan sun ishe mu, mu mun rasa yadda za mu yi."

Yusuf: Me ake yi wa Fulanin da kuke cewa abubuwan da ake muku sun ishe ku?

Batunga: Tun da aka soma abubuwan nan, za a je gidan Fulani a kashe su a kwashe musu dabbobi, a yi wannan, a yi wancan. Har yanzu dai ba mu samu nutsuwa da kwanciyar hankali ba.

Ba mu da kwanciyar hankali a Kudancin Kaduna. Ka ga yanzu duk lokacin da aka ce an yi sulhu, to bayan kwana biyu za ka ji an kai hari, an kashe Bafulatana.

A gona a kashe, a kiwo a kashe. Yanzu ka ga satin da ya wuce ɗin nan, an kashe wani yaro makiyayi a jeji, aka cire kansa aka bar gangar jikin.

Masu tafiya a mota da na ƙafa duk ba su tsira ba.

Yusuf: Me za ki ce kan zargin da ku ma Fulani aka daɗe ana yi muku a kudancin Kaduna cewa kuna kai hare-hare?

Batunga: Ikon Allah! Wannan fa shi ne a dake ka a hana ka kuka. Mu Fulani ba ma faɗa. Ai a Kudancin Kadunan muka tashi, a nan aka haife mu.

Yusuf: Gwamnati ta sha cewa ana tura jami'an tsaro don samar da zaman lafiya.

Batunga: Kila jami'an tsaron ba su isa ba ne. Kowane lokaci ana irin wannan tashe-tashen hankali. Yau a ce an yi sulhu gobe a ce an ƙara. Ƙila jami'an tsaron ba su ishe su ba ne, ko kuma an raina waɗanda suke wajen.

Yusuf: Kun taɓa kai wa gwamnatin Kaduna ƙorafi kan halin da ake ciki?

Batunga: Mun yi yunƙuri har takarda mun rubuta. Wallahi muna so mu ga gwamna amma ba mu samu ganinsa ba.

Yusuf: A taƙaice yanzu me kuke so gwamnati ta yi muku?

Batun: Mu dai yanzu muna so gwamnatin jiha da ta tarayya da Buhari su taimake mu wannan wuta ta mutu.

Yanzu mu dai Fulani ba dama ka tura yaro niƙa sai a kashe shi. Mace ba za ta fita ita kaɗai ba sai a tare ta, namiji ma idan ya fita shi kaɗai za a tare shi. To ina zaman lafiya a nan?

In kuma ƙila waɗanda suke sashen wajen sun fi ƙarfin gwamnati ne to shi ne ba mu sani ba.

Ka ga mu mata mun fi jin zafin haihuwa, mun gaji da muna haifar 'ƴa'ƴa ana kashe mana su.

Idan kuma akwai wata ƙasa ne da za a tsince Fulanin da ke kudanci a mayar da mu to sai gwamnatin tarayya ta nuna mana inda za mu koma, domin gaskiya mu wallahi rayukanmu duk a haɗari suke.