Mahdi Aliyu Gusau: Majalisar Dokokin Zamfara ta tsige Mataimakin Gwamna

Asalin hoton, Mhadi Ali Gusau
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara a ranar Laraba ta kaɗa ƙuri'a domin tsige mataimakin gwamnan jihar Barrista Mahdi Aliyu Gusau.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan majalisa 20 cikin 24 sun zaɓi a tsige mataimakin gwamnan bayan wani rahoto da kwamitin shari'a a jihar ya gabatar a kansa da ya same shi laifi kan zarge-zargen da ake yi masa.
Ɗaya daga cikin ƴan majalisar da suka halarci zaman Honarabul Ibrahim Tudu Tukur mai wakiltar Bakura ya tabbatar wa BBC da cewa su 21 cikin 24 suka halarci zaman kuma mutum 20 sun amince da a tsige mataimakin gwamnan.
Tsigewar ta biyo bayan amincewa da rahoton da wani kwamitin bincike da ya binciki zarge-zargen da ake yi wa mataimakin gwamnan na saba ka'idar aiki ya mika.
Mataimakin gwamnan ya yi zargin cewa an yi masa bi-ta-da-kulli ne saboda ya ki sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da gwamnan jihar.
A wata hira da ya taba yi da BBC mataimakin gwamnan Zamfara Mahdi Aliyu Gusau ya ce gwamna Matawalle bai nemi shawararsa ba har zuwa lokacin da ya yi wanka zuwa jam'iyyar APC.
Daga cikin dalilan da majalisar ta bayyana na tsige mataimakin gwamnan sun haɗa da rashin amsa gayyatar da aka yi masa ba, batun da Mahdi Aliyu Gusau ya ce an saɓa doka wajen bin ka'idar tsige shi, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadi.
Honorabul Faruk Musa Dosara shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar ya kuma shaida wa BB cewa: "Dama a baya an gabatar da tuhumar da ake yi wa shi mataimakin gwamna ga babbar mai shari'a ta jihar Zamfara.
Ko da yake an gabatar da wannan rahoto na kwamitin kudi na jihar Zamfara, sai aka kafa kwamitin lauyoyi masu zaman kansu da ba su da alaƙa da gwamnati ko siyasa. Bayan an rantsar da su sun ci gaba da aikinsu.
"A wannan rana ce suka kawo mana rahotonsu a gaban shugaban majalisa.


To ko waɗanne laifuka ne ƴan kwmaitin suka sami mataimakin gwamnan da su har aka tsige shi?
Honorabul Faruk ya ce laifukan da muke tuhumar sa da su duk sun tabbatar da su, bisa ga shaidun mutane daban-daban da suka karɓa.
Sun binciki laifukan kuma sun tabbatar da cewa lallai sun faru, inda suka tabbatar da laifuka biyu cikin uku, suka bar ɗaya da ba su ce komai ba a kansa.
"A kan haka ne sifika da sauran ƴan majalisa suka shiga zauren suka karɓi rahoton, bayan haka ne aka ce a jefa ƙuri'a ta yarda ko ƙin amincewa da rahoton da suka kawo.
"Daya bayan ɗaya aka kira kowane ɗan majalisa ya jefa ƙuri'ar tsige mataimakin gwamna. CIkin mu 20 da muka jefa ƙuri'a ban da sifika duk mun yarda da a tsige shi.
"Bisa wannan ƙuri'a ne aka tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara a yau 23 ga watan Fabrairtun 2022," a cewar dan majalisar.
Wannan tsigewa na nufin a yanzu kujerar mataimakin gwamnan jihar Zamfara babu kowa a kanta, don haka abu na gaba shi ne a ɗora sabon mataimaki.
"Mun tura wa ɓangaren zartarwa na jihar Zamfara cewa daga yanzu mataimakin gwamna ya zama tsigagge, akwai buƙatar su turo sunan wani a matsayin mataimakin gwamna don majalisa ta tantance shi ta duba in ya cancanta sai ta ba da dama ya zama mataimakin gwamnan," a cewar Honorabul Faruk.
A farkon wannan mako ne mataimakin gwamnan Zamfaran da aka tsige, Mahdi Aliyu Gusau, a wata hira da BBC Hausa ya ce ana yi masa bita-da-ƙulli ne saboda ya ki bin gwamnan jihar Bello Matawalle zuwa jam'iyyar APC.
Sai dai Honorabul Faruk ya ce batun ba gaskiya ba ne. "Ai ba yau aka fara ba a Najeriya, a samu gwamna da mataimakin gwamna daga jam'iyyu daban-daban.
"Kawai dai ya bar ayyukan da ya kamata ya yi ne waɗanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya rataya masa ya yi a matsayinsa na mataimakin gwamna.












