Abubuwan da gwamnonin APC da PDP suka tattauna a tarukan da suka yi daban-daban

Gwamnonin APC

Asalin hoton, APC

Bayanan hoto, Gwamnonin APC sun haƙiƙance cewa za a gudanar da babban taron jam'iyyar a watan Fabarairu
An wallafa

Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya sun jaddada cewa za a yi babban taron jam'iyyar a watan Fabrairu kamar yadda aka tsara tun da farko.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnonin sun shafe kusan duka daren Litinin suna tattaunawa a kan batun a Abuja kafin su cimma matsayar.

Bayanai na cewa gwamnonin sun tafka zazzafar muhawara gabanin cimma matsaya a kan lokacin da za a yi taron.

Wasu gwamnonin na da ra'ayin cewa a dage lokacin taron zuwa wani lokaci na gaba, yayin da wasunsu suka kafe a kan cewa kada a sauya lokacin taron daga abin da suka amince a baya aka kuma sanar da Shugaba Muhammadu Buhari shi ma ya amince.

Sai dai a taron na Lahadin nan, gwamnonin ba su fayyace takamaimiyar ranar da za a gudanar da taron ba.

A tattaunawarsa da manema labarai bayan taron, shugaban ƙungiyar gwamnonin na APC, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi ya bayyana cewa kwamitin riƙon jam'iyyar ne zai ayyana ranar zaben.

A wajen taron na ƙasa ne ake sa ran za a zaɓi sabbin shugabannin da za su ja ragamar jam'iyyar ta APC zuwa zaɓukan 2023.

Ana sa ran cewa nan gaba gwamnonin za su sanar da Shugaba Buhari matsayar da suka cimma.

Taron gwamnonin PDP

Gwamnonin PDP

Asalin hoton, Bauchi State Government

Bayanan hoto, Wannan ne karon farko da gwamnonin PDP ke ganawa da zaɓaɓɓun shugabannin jam'iyyar

Sai dai kwana ɗaya bayan da gwamnonin na APC suka yi taronsu a Abuja, su ma takwarorinsu na PDP yi nasu a birnin Fatakwal na Jihar Rivers.

A taron nasu, gwamnonin PDP sun tattauna ne kan makomar jam'iyyar da jadawalin tsare-tsare na ayyukanta da batun zaɓen 2023.

A cewar mataimakin sakataren watsa labarai na PDP Ibrahim Abdullahi, gwamnonin sun tatttauna kan batun tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023.

Ya ce wannan ne karon farko da gwamnonin suke yin taro da sabbabin shugabannin jam'iyyar da aka zaba aka kuma rantsar da su a karshen 2021.

Tarukan na gwamnonin APC da PDP dai su ne na farko a wannan shekara ta 2022, shekarar da harkokin zaɓen 2023 za su kankama.