Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan hirar Shugaba Buhari da Channels TV

..

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Bayan shafe lokaci mai tsawo bai yi jawabi ko hira da ƴan jarida ba, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a karon farko a sabuwar shekarar 2022 ya tattauna da gidan talabijin na Channels a Najeriya.

Shugaban ya amsa tamabayoyi da dama daga ƴan jaridar duk da cewa a gabatarwar tattaunawar sai da ƴan jaridar suka ce sai da suka aika da tambayoyin da za a yi wa Buhari zuwa fadar shugaban ƙasa.

Tambayoyin sun haɗa da batun tsaro da tattalin arziki da batun yan sandan jihohi da batun ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda.

Abubuwan da suka fi jan hankali su ne batun ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda da batun ƴan sandan jihohi da kuma batun halin ko-in-kula da shugaban ya nuna dangane da wanda zai gaje shi.

Waɗannan lamuran sun jawo ce-ce-ku-ce matuƙa a shafukan sada zumunta da muhawara inda jama'a ke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu.

Me ƴan Najeriya suke cewa?

Tun da yammacin Larabar sunan Shugaba Buhari ke tashe a shafukan sada zumunta. A tuwita an yi amfani da sunansa sau fiye da 50,0000.

A Facebook kuma an yi magana kan hirar sau kusan 15,000 daga ranar Laraba zuwa Alhamis.

Da dama mutanen da suke tsokaci a shafukan sada zumunta na sukar shugaban ne da cewa ya gaza amsa tambayoyin yadda suka kamata. A ganinsu ma, ya bar jaki ne ya koma bugun taiki.

Wannan layi ne
Wannan layi ne

Bai kamata a ƙirƙiri 'yan sandan jihohi ba - Buhari

.

Asalin hoton, Channels TV

A cikin tattaunawar, Shugaba Buhari ya ce "babu maganar ƙirƙirar 'yan sandan jihohi" yayin da yake maganar rikicin makiyaya da manoma.

Dangane da wannan batu BBC ta tuntuɓi Farfesa Kamilu Sani Fagge, wanda mai sharhi ne kan al'amuran yau da kullum inda ya bayyana cewa bai ga laifin Shugaba Buhari ba don ya ƙi amincewa da kafa ƴan sandan jihohi.

"Idan aka duba irin abin da ya wakana a baya, yadda aka rinƙa amfani da su ƴan sanda, jam'iyya mai mulki takan yi amfani da ƴan sanda domin tursasa jam'iyya mai mulki domin cin zaɓe."

Ya bayyana cewa idan aka yi la'akari da yadda gwamnoni suka sa ƙananan hukumomi a cikin aljihunsu da kuma yadda sai wanda suke so a jiharsu zai yi tasiri, don haka a cewarsa samar da ƴan sandan jihohi zai ƙara wa gwamnoni ƙarfi.

Ya ce akwai hatsari a ce za a yi ƴan sandan jihohi saboda irin ƙarfin da gwamnoni suke da shi a yanzu inda ya ce za a rinƙa kama karya ne kawai.

Batun hauhawar farashi

Da aka yi wa shugaban tambaya abin da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki tun bayan hawansa mulki, sai Shugaba Buhari ya kada baki ya ce maganin wannan matsalar ita ce "A koma gona."

A kan hakan ne a shafin Tuwita Aishatu Yusufu ta ce:

"Shin an yi wa Buhari tambaya a kan ksashe-kashen da ake yi a gonaki?

Shin an yi wa Buhari tambaya a kan harajin da manoma ke biyan ƴan bindiga kafin su girbe shukarsu?

Shin an yi wa Buhari tambaya a kan manoman Zabarmari da aka kashe a gonakinsu?

Shin an yi wa Buhari tambaya a kan matan da ake yi wa fyaɗe ake kashe su a gonaki?"

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Short presentational grey line

Zaɓen 2023 ba matsalata ba ce - Buhari

..

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

A cikin tattaunawar, Shugaban ya ce "ba abin da ya dame shi" da babban zaɓen 2023 mai zuwa inda ya ce zaɓen ba matsalar shi ba ce.

A fahimtar Farfesa Kamilu, wannan irin siyasar Shugaba Buhari ce inda ya ce ko da yake bai yi la'akari da irin matsalar da abin da faru a baya ta ja masa ba.

"Misali lokacin da ya ci shugaban ƙasa aka zo za a yi jagoranci na majalisa, ya koma ya ce shi ba ruwansa duk wanda inna ta aura ya zama baba, daga ƙarshe abin ya zama babbar matsala a siyasarsa saboda yadda majalisar ta zama tamkar jam'iyyar hamayya," in ji shi.

Farfesa ya bayyana cewa Buhari na da ra'ayin cewa ba zai sa baki a batun wanda zai gaje shi ba, amma a cewarsa tun da harkar siyasa ce ya kamata a ce yana da sha'awa kan abubuwa yadda za su gudana.

"Ko da ba zai nuna wanda yake so ba, ya kamata ya tabbatar an tsaya an yi zaɓe na gaskiya da kuma ɗora Najeriya kan hanya saboda halin da ake ciki."

Short presentational grey line

Ba na goyon bayan zaɓen 'yar tinƙe - Buhari

A dai cikin tattaunawar, Shugaba Buhari ya ce ba ya goyon bayan tsarin zaɓe na 'yar tinƙe yayin zaɓen 'yan takara a cikin jam'iyyun siyasa, wanda sabuwar dokar zaɓe ta tanada.

A cewar Farfesa Kamilu, wannan zaɓe na ƴar tinƙe yana da alfanunsa da kuma rashin alfanunsa, inda ya ce daga cikin alfanunsa zai hana maguɗi da ake yi ta hanyar amfani da wakilan zaɓe ko kuma delegate wanda ake saye su.

Haka kuma ya ce rashin alfanunsa shi ma ana maguɗi wajen ƙirga mutanen da ake yi inda ya ce akwai kuma hatsari matuƙa wajen tara mutane masu yawa haka.

"Shi gundarin dokar zaɓen idan aka duba akwai sauye-sauye da yawa da ta kawo waɗanda za su inganta zaɓe a Najeriya, amma sai aka bar matsalar aka koma aka yi ta rigingimu a kan wannan zaɓe na ƴar tinƙe," in ji shi.

Short presentational grey line

Maganganun wasu a shafukan sada zumunta

Wani a Facebook Umar Fa'izu Saleh ya ce: "Bayan kallon hirar Shugaba Buhari da gidan talabijin na Channels, abin da na fahimta shi ne Buhari ba shi ke jan ragamar ƙasar nan ba.

Bai ma san ƴan Najeriya a yanzu ba sa ɗaukarsa da muhimmanci ba. Har yanzu gani yake ko kuma makusantansa suna gaya masa cewa har yanzu ƴan Najeriya na ganinsa a matsayin mutum mai daraja. Kai!

Kauce wa Facebook

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook

@ayemojubar ta ce: "Seun na gidan talabijin din Channels ya tambayi Buhari kan batun ƴan sandan jihohi, amma sai ya amsa masa da batun sarakunan gargajiya."

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wannan layi ne