Mali: Kasashen Yamma sun soki kasar Rasha kan ‘aikewa’ da sojojin haya

Kasashen Yammacin duniya kawaye fiye da gwammai ne suka yi alla-wadai da abin da suka kira aike wa da sojojin haya na kasar Russia zuwa kasar Mali.
Sun bayyana cewa hakan ka iya "ta'azzara matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin Afirka ta Yamma" da ke fama da kungiyoyin maso jihadi.
Kasashen Turai 15 da Canada sun zargi kasar Russia da bayar da taimakon kayan aiki wajen aikewa da sojojin haya daga kamfanin horar da sojiji na Wagner.
Kasar Russia ta musanta alakar gwamnati da kamfanin sojojin mai zaman kansa.
A baya bayan nan ne Kungiyar Tarayyar Turai ta sanya takunkumi kan kamfanin na Wagner group, tare da zargin hannu a aikata mummunan cin zarafin bil adama.
A shekarar 2014 ne aka gano kamfanin wanda ya yi kaurin suna, lokacin da take goyon bayan 'yan a-waren kasar Russia a lokacin rikicin gabashin kasar Ukraine. Tun bayan wannan lokacin ne ta rika mu'amala a wasu kasashe da suka hada da Syria, da Mozambique, da Sudan, da Libya da kuma Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.
A wata sanarwa a ranar Alhamis, kasashen Yamma sun yi gargadin cewa aikewa da sojojin hay ana Wagner ka iya kara 'tazazzara matsalolin da suka shafi 'yancin bil adama a kasar Mali da kuma yin barazana da haifar da cikas ga yarjejeniyar zaman lafiya da sasantawa' a kasar da rikici ya daidaita.
Sun kuma bayyana cewa sun yi "matukar nadama" da zabin mahukuntan kasar Mali wajen amfani da "kudaden da daman ba su wadace su ba" wajen biyan sojojin hayar na kasashen waje a maimakon taimaka wa sojojin kasar.
Sanarwar dai ta hadin guiwa ce da kasashen Belgium, da Canada, da Jamhuriyar Czech, da Denmark, da Estonia, da Faransa, da Jamus, da Italiya, da Lithuania, da Netherlands, da Norway, da Portugal, da Romania da Sweden da kuma Birtaniya suka fitar.
Kasar Faransa - tsohuwar uwargijiyar kasar Mali - ba ta jima da janye sansaninta na karshe a arewacin Malin ba, wani bangare na janye dakarunta da ke fafatawa da mayaka masu tsattauran ra'ayin addinin Islama a yankin Sahel.
Kasar ta Mali ta mayar da martani game da abubuwa da suka farun a baya bayan nan.












