Ku San Malamanku tare da Dr Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Dr Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo
An wallafa

Wani babban malamin Musulunci a jihar Kano da ke Najeriya Dr Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo, ya ce ba zai taɓa mantawa da alkahirin da marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ya yi masa na ba shi auren ƴarsa Malama Zainab a lokacin yana ɗalibi ba, duk da yawan mutanen da suka so aurenta.

Malamin ya faɗi hakan ne a hirasa da BBC Hausa a shirin Ku San Malamanku.

Haka kuma Dr Ibrahim ya ce ya tasirantu matuƙa da surukin nasa Sheikh Ja'afar Adam kuma har a yanzu yana daga cikin malaman da ba zai manta dan gudunmowar da suka bai wa rayuwarsa ba musamman a fannin ilimi.

Wane ne Dr Ibrahim Abdullahi Sani Rijiyar Lemo?

An haifi Dr Ibrahim Abdullahi Sani Rijiyar Lemoa jihar Kano, kuma a can ya girma ya yi karatu.

Ya fara karatu a Khairil Bariyya Islamiyya Rijiyar Lemo ta Sheikh Musa Hussaini Madabo, sannan ya koma Gobirawa Special Primary School Kofar Ruwa, ya kuma ƙrasa a Rijiyar Lemo Primary 'Yan Mata.

Bayan kammala karatun firamare ne ya tafi ƙaramar sakandare ta Kofar Ruwa Islamic Secondary School, inda bayan shekara uku ya koma babbar sakandare ta SAS duk a Kano.

Ya kammala sakandare a shekarar 1994, sannan ya wuce Jami'ar Musulunci a jamhuriyar Nijar inda karanta Shari'a da Ilimin Addinin Musulunci, ya kammala a shekarar 1999.

Ya koma Najeriya a shekarar, inda ya yi daura ta neman gurbin karatu a Jami'ar Musulunci ta Madina, ya kuma yi nasara ya tafi ya sake yin digiri a fannin Hadisi da Ilimin Addinin Musulunci, ya gama a shekarar 2003.

Dr Rijiyar Lemo ya zarce ya yi digiri na biyu a Madinan sannan ya yi digirin-digirgir duk a can.

Bayan komawarsa Najeriya ne ya fara koyarwa a Jami'ar Bayero Kano, sannan kuma yana ayyukan da'awa.

Kuma a yanzu haka shi nesakataren ilimi da ilimintarwa na ƙungiyar JIBWIS ta ƙasa.

Dr Ibrahim Rijiyar Lemo

Su waye gwanayensa a malamai?

Malam ya ce malaman sunnah da dama ababen kwaikwayonsa ne.

"Babban malamin da ya zame min abin kwaikwayo shi ne Muhd Sani Umar Rijiyar Lemo. Malamina ne tun a firamare, ina amfana da shi sosai har yanzu."

Sauran malaman da suka zame masa ababen kwaikwayo sun haɗa da Dr Bashir Aliyu Umar da Dr Jalo Jalingo sai kuma marigayi surukinsa Sheikh Ja'afar Mahmud Adam.

Sannan ya ce Sheikh Bala Lau shugaban ƙungiyar Izala ta ƙasa da sakataren ƙungiyar Sheikh Kabiru Haruna Gombe da Sheikh Yakubu Musa Sautus Sunnah da kuma Dr Abubakar Sani Birnin Kudu su ma malamai ne da yake matuƙar ɗauka a matsayin ababen kwaikwayonsa.

Wannan layi ne

Rubuce-rubuce

Baya ga kundin digiri na uku da ya rubuta, Malam ya fassara ayyuka da dama kamar ƙasidu da maƙaloli da mujallu musamman waɗanda suka shafi ayyukan alhazai.

"Akwai kuma waɗanda ba a riga an buga ba amma ana aiki a kansu kamars jerin littattafai a kan warware matsalolin zamantakewar aure a mahangar Musulunci," in ji malam.

Dr Ibrahim ya ce yana son harkar ilimi da karance-karancen littattafai sosai.

"Ina son littafi matuƙa. Ina sayen littafi ko nawa ne, ba na ƙyashin kashe kudi a sayen littafi. Ina kuma son turare, don ƙamshi na burge ni."

Da'awah

Malam ya ce a rayuwarsa yana matuƙar son harkar da'awa, saboda yana samun nutsuwa da kwanciyar hankali idan yana yin ta.

A cikin hirar ya bai wa BBC labarin abin da ya fi komai ba shi mamaki a harkar da'awa da yake yi, inda ya ce a watan Nuwamban 2021 a wata tafiyar da'awa da ya yi a jihar Neja ya ga abin al'ajabi da ba zai manta da shi ba.

"Mun je wani ƙauye Oran can cikin daji a jihar Neja amma ta jihar Kebbi ake shiga. Mutanen garin bambancinsu da tsirara kaɗan ne. Kuma haka nan suke rayuwarsu maza da mata.

"Sai na ce maza su koma gefe, mata ma haka. Haka za ka ga mace ƙirji a waje tana shayarwa. Wasu ma kusan haka suka zo babu riga. Suka yi ta kallonmu kamar sun ga wasu halittun daga wata duniyar.

"Amma kuma suna da sauƙin hali. Ba mu ɗauki lokaci muna ba su haske a kan Musulunci ba suka yarda za su shiga, mutum 566 ne suka karɓi Musulunci a take," kamar yadda malam ya shaida mana.

Malam yana da aure da 'ya'ya takwas.

Wannan layi ne