Hotunan jana'izar Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan

An wallafa

Dazu ne aka yi jana'izar Sarkin Ban Kano kuma tsohon Hakimin Dambatta Alhaji Mukhtar Adnan wanda ya rasu yau Juma'a da asuba.

Marigayin ya rasu yana da shekara 95 a duniya. Adnan yana cikin masu zaben Sarkin Kano -- shi kadai ne ya zabi sarakunan Kano guda hudu da suka hada da Alhaji Muhammadu Inuwa, Alhaji Ado Bayero a 1963, da Muhammadu Sanusi II a 2014 da kuma Alhaji Aminu Ado Bayero a 2020.

An yi jana'izarsa ne a garin Dambatta da ke jihar Kano kuma daruruwan mutane ne suka halarci jana'izar.

Ga wasu daga cikin hotunan ja'aizar tasa:

Jana'izar Sarkin Bai

Asalin hoton, Instagrfam/Kwankwasiyya_Nigeria

Bayanan hoto, Masu sarauta da dama ne suka halarci jana'izarsa ciki har da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero.
Jana'izar Sarkin Bai

Asalin hoton, Kwankwasiyyasa_nigeria

Bayanan hoto, Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yana cikin wadanda suka halarrci jana'izar
Jana'izar Sarkin Bai

Asalin hoton, Kwankwasiyya Reporters

Bayanan hoto, Dandazon jama'a sun yi wa Dambatta tsinke domin halartar jana'izar
Jana'izar Sarkin Bai

Asalin hoton, other

Bayanan hoto, An binne shi ne a gidansa da ke garin na Dambatta
Jana'izar Sarkin Bai
Bayanan hoto, Jamai'an tsaro sun yi aiki sosdai domin shawo kan mutane su bi doka