Hotunan jana'izar Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan

An wallafa

Dazu ne aka yi jana'izar Sarkin Ban Kano kuma tsohon Hakimin Dambatta Alhaji Mukhtar Adnan wanda ya rasu yau Juma'a da asuba.

Marigayin ya rasu yana da shekara 95 a duniya. Adnan yana cikin masu zaben Sarkin Kano -- shi kadai ne ya zabi sarakunan Kano guda hudu da suka hada da Alhaji Muhammadu Inuwa, Alhaji Ado Bayero a 1963, da Muhammadu Sanusi II a 2014 da kuma Alhaji Aminu Ado Bayero a 2020.

An yi jana'izarsa ne a garin Dambatta da ke jihar Kano kuma daruruwan mutane ne suka halarci jana'izar.

Ga wasu daga cikin hotunan ja'aizar tasa: