Sojojin Faransa sun yi ruwan wuta a garin Tera na jamhuriyar Nijar

France

Asalin hoton, STEPHANE DE SAKUTIN

An wallafa

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun ce akalla mutum biyu ne suka rasu sannan da dama suka jikkata sakamakon ruwan wuta da kuma harbi ta kasa da wasu da ake kyautata zaton sojojin kasar Faransa ne suka yi kan garin Tera na yankin Tillabery da ke yammacin jamhuriyar.

Wani wanda ya shaida yadda al'amarin ya faru wanda kuma shi ma Allah ya tseratar, ya shaida wa BBC cewa da misalin karfe goma na safiyar ranar Asabar ne wani gungun sojojin kasar ta Faransa ya nemi ya kutsa garin na Tera domin wucewa zuwa birnin Yamai.

To sai dai al'ummar garin bisa hadin gwiwar jami'an tsaro sun rufe hanya cewa sojojin na Faransa ba za su wuce ba.

Daga nan ne kuma sojojin wadanda fararen fata ne suka bude wuta ta sama da kasa, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen biyu, a kokarinsu na tarwatsa jama'a.

An dai jiyo sojojin na Faransa na cewa 'babu wanda ya isa ya hana mu shiga jamhuriyar Nijar domin mallakarmu ce", a yaren Faransanci.

Tun dai a ranar Juma'a ne aka fara samun takun saka tsakanin bangarorin biyu, bayan da sojojin suka iso bakin garin da karfe biyar na asuba.

Kafin nan dai sai da aka samu irin wannan tankiya da sojojin na Faransa da al'ummar wasu yankunan kasashen Burkina Faso da Cote-D'Ivoire.

Ana dai ta mamakin yadda alakar kasar Faransa ke kara yin tsami da kasashe rainonta.

Masana na ganin Faransar na yin barazana ne ga yunkurin kasashen na Afirka da ta raina zamanin mulkin mallaka, na neman ballewa daga hannunta bisa abin da suka kira 'zaluncin nasara'.

A baya-bayan nan ne dai aka nuna wani majigi da aka yi wa lakabi da suna 'African Apocalypse' a Burtaniya wanda ya nuna yadda kasar Faransa ta 'kashe da wulakanta' kabilar Hausawa a jamhuriyar ta Nijar zamanin mulkin mallaka