Yakin Tigray na Habasha: Dalilin da ya sa duniya ta damu a kansa

Wata mace tare da 'ya'yanta, a daidai lokacin da aka kawo agajin abinci da katifu a wata cibiyar kula da yara da ta koma sansanin 'yan gudun hijira ranar 11 ga watan Oktoba 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rikicin da ake yi a arewacin kasar ya sa mutane miliyan biyu sun rasa muhallinsu, wasu sama da hakan na tsananin bukatar agajin abinci
An wallafa

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi bulaguro zuwa Kenya , inda ya tattauna kan rikicin makwabciyarta Habasha.

Tuni aka umarci 'yan Amurka da Birtaniya su fice daga kasar tun ana da sauran jiragen fasinja kamar yadda Ministan Birtaniya ya bayyana.

Wannan shawara da aka bayar da kuma waiwaye kan abin da ya faru a Kabul a watan Agusta, an bayar da ita ne a daidai lokacin da alamu suka nuna cewa dakarun 'yan tawaye daga arewacin Tigray ka iya dannawa babban birnin kasar, Addis Ababa.

Shekara guda da fara yakin basasar, wanda ya jefa jama'a cikin mummunan yanayi, a bangare guda kuma kasashen duniya na jan hankalin bangarorin biyu kan abin da rikicin zai haifar ga kasar ta Habasha.

Matsin lambar da kasashen Afirka da jami'an diflomasiyyar Amurka ke yi wa Habasha na karuwa, kuma hakan babban tasiri zai yi ga yankin da ma duniya baki daya.

Me ya sa aka damu?

Adadin wadanda lamarin ya shafa daga bangarorin biyu zai yi matukar tasiri ga yankin da ma duniya baki daya.

Akalla 'yan yankin 400,000 ne ke cikin barazanar rashin abinci, yayin da yankin ke fama da rashin kashi 80 cikin 100 na magungunan da ake bukata, sai kuma wasu sama da miliyan biyu da aka tilastawa tserewa daga gidajensu.

Ana zargin gwamnati da hana kayan agaji shiga yankin Tigray da gangan, zargin da ta musanta.

Haka kuma, akwai shaidun da suka nuna cewa an yi ta kashe mutane, da azabtarwa, da cin zarafi ta hanyar lalata, da dukkan bangarorin biyu suka aikata.

Amma akwai wata manufa da suke da ita kan rikicin.

Kasar Habasha mai yawan al'umma miliyan 110, ita ce ta biyu mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka, ta kasance mai kwanciyar hankali kuma babbar kawar kasashen yammacin duniya.

Ana fargabar matukar tashin hankalin ya ci gaba, wannan ka iya janyo darewar ta gida biyu sakamakon yawan kabilu daban-daban da ake da su. Idan miliyoyin mutane suka tsere daga yankunan da ake tashin hankalin, to zai yi matukar wuya makwabtansu su samu kwanciyar hankali.

Kasar Habasha na iyaka da kasashe shida, biyu daga ciki na fama da tashin hankali wato Sudan ta Kudu da Somaliya, yayin da sauran kamar Sudan ba a dade da yin juyin mulki ba.

Dakarun Habasha na cikin kawancen dakarun Tarayyar Afirka da na Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da mayakan Islama na Somaliya, ana kuma fargabar za su iya janyewa idan kasashensu suka bukaci hakan.

Gabannin yin balaguro zuwa Afirka, Sakatare Blinken ya yi gargadin cewa rikicin da ake fama da shi zai tagayyara 'yan kasar da ma nahiyar baki daya.

Su ma dakarun Eritrea sun dade suna mara wa gwamnatin Habasha baya, kuma su ma lamarin ka iya shafarsu.

Dan zanga-zanga ya daga tutar Habasha a lokcin zanga-zangar 7 ga watan Nuwamba 2021 a birnin Addis Ababa, Ethiopia.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A farkon wannan watan, dubban 'yan kasar ne suka cika titunan birnin Addis Ababa domin nuna goyon baya ga gwamnati a yakin da take yi da 'yan twayen TPLF

A watan da ya gabata, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa kasar Turkiyya ta amince ta sayar wa sojojin kasar Habasha jirage marasa matuka. Wannan yarjejeniya na barazana ga kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da kasar Masar, wadda daman suke da jikakkiya tsakanin ta da Habasha kan batun mallakar Kogin Nilu.

Har wa yau, Habasha ta sayo makamai daga kasashen China da Iran, sannan an yi amfani da jiragen Hadaddiyar Daular Larabawa wajen kai makaman, kamar yadda rahoton shafin intanet na Oryx ya rawaito.

A bangaren Amurka, ta dade tana kallon Habasha a matsayin babbar aminiya, musamman lokacin yaki da ta'addanci.

Ta taimaka wajen yaki da masu tayar da kayar baya a Somaliya, sojojin Habasha su ne a sahun gaba ta wannan fannin, ta kuma yi wa Amurka tayin amfani da sararin samaniyarta a lokacin yakin Iraqi. Tana daga cikin tsirarun kasashen Afirka da suka shiga wani kawance na Amurka mai suna ''Kawancen masu aniya''.

Kwanciyar hankali da zaman lafiya a kasar Habasha na da matukar muhimmanci ga kawayenta musamman Amurka wadda ke taimakawa da kudade, ta kuma kai agajin sama da dala biliyan hudu tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.

Sai dai wakilin Amurka na musamman a yankin, Jeffrey Feltman, ya zargi gwamnatin Habasha bisa matakan da take dauka na yaki da 'yan tawayen Tigray, wanda ya janyo mummunar yunwa a kasar, da kuma ya alakanta da kwatankwacin abin da shugaban Syria Bashar al-Assad ya janyo wa 'yan kasa.

Shin babban birnin na fuskantar barazana?

Bayan hare-hare da tashin hankali da kokarin dannawar da mayakan 'yan tawayen 'yantar da al'ummar yankin Tigray (TPLF) suke yi, da kuma dannawa babbar hanyar da za ta sada su da babban birnin kasar Addis Ababa, sai lamura suka kara munana.

Amurka ta fitar da sanarwar kwashe 'yan kasarta daga Habasha, shi kuma Firaiminista Abiy Ahmed ya sanar da ayyana dokar ta-baci a baki dayan kasar, tare da kiran a sake horas da karin sojoji.

Hukumomin Addis Ababa sun yi kira ga 'yan kasar su yi wa makamansu rijista.

Wata kungiya kuma babbar aminiya ga 'yan tawayen TPLF, ta ce suna dannawa kusa da Addis Ababa.

Yawan kabilu da birnin ke da su ya kara rura wutar tashin hankalin, inda wasu ke zargin hukumomi da far wa 'yan Tigray da cafke su.

Sai dai har yanzu dakarun na Tigray na da nisan kilo mita 300 zuwa birnin, inda suka ya da zango a garin Kombolcha.

Taswirar kasar Habasha

Tsohon mataimakin sakataren harkokin wajen Amiuka a Afirka Tibor Nagy, ya shaida wa BBC cewa: "Mayakan Taliban sun mamaye Afghanistan ta hanyar bude wuta a gagaruwa da kauyuka".

"Su ma mayakan TPLF abin da suke yi kenan, suna shanye duk wata matsin lamba, don haka idan abubuwan suka rincabe za a yi kare jini, biri jini a birnin."

Ya yi amanna da karbe iko da babban birnin barazana ce, kamar yadda ake fargabar kasashen da ke kera makamin nukiliya da yin amfani da shi ta hanyar da ba ta dace ba.

Mayakan TPLF sun ce abin da kawai suke bukata shi ne samun damar kai kayan agaji daukacin yankin Tigray.

"Za mu ci gaba da dannawa Addis Ababa, amma ba wai son shiga muke yi ba, ko aniyar amfani da karfin makamai, abin da kawai muke da bukata shi ne bude hanya domin kayan agaji su isa ga jama'armu," in ji mai magana da yawun TPLF Getachew Reda kamar yadda ya shaida wa shirin BBC Focus on Africa.

Gwamnatin Habasha ta ayyana 'yan tawayen TPLF a matsayin 'yan ta'dda, sannan firaiminista ya sha alwashin yakarsu ta kowacce hanya.

"Za mu yaki makiyanmu da karfin da muke da shi, mu kuma sadaukar da jininmu ga al'ummar Habasha, har sai mun dago martabarta," in ji Mista Abiy..

Shin an fara tattaunawar sulhu?

Abin fargabar yanzu shi ne shiga sabon babi da rikicin ya fada, zai kuma yi matukar wuya dukkan bangaren biyu su ajiye makamansu.

Ana kuma fargabar tashin hankalin ka iya shafar kasashe makwabta.

Kungiyar TPLF ta kulla kawance da wasu kungiyoyin na kasar da ba sa ga maciji da gwamnati inda kawancen ke son kawo karshen gwamnatin Abiy.

Wakilin kungiyar Tarayyar Afirka, kuma tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya yi bayanin 'yar karamar damar kafar tattaunawa tsakanin masu rikici da juna.

"Babu isasshen lokacin shiga tsakani," kamar yadda ya shaida wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, bayan tattaunawa da bangaren gwamnatin Habasha da na 'yan tawaye a ziyarar da ya kai kasar a baya-bayan nan.

Ya yi kiran a yi amfani da maslaha da matakan siyasa wajen warware rikicin, ko da yake bai yi karin bayani kan yadda za a cimma hakan ba.

Sai dai jakadan Majalisar Dinkin Duniya, Taye Atske Selassie, ya ce masu shiga tsakanin za su fuskanci tarin matsaloli. Ya kara da cewa yana mutunta kiran a sasanta, amma ya ci gaba da bayyana 'yan tawayen Tigray a matsayin "gungun masu aikata muggan laifuka".

Masu zanga-zanga dauke da tutar Tigray a ranar 4 ga watan Nuwamba 2021 a birnin Washington, DC

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, 'Yan Tigray mazauna Amirka sun yi maci a birnin Washington DC , a ranar da aka cika shekar daya da fara yakin

Kakakin TPLF Mista Getachew, ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa yawancin shirin tattaunawar sulhun da ake yi ana kokarin kubutar da Firaiminista Abiy, ba wai a tattauna ainahin abin da ya janyo tashin hankalin da kasar ke ciki da rigimar siyasa.

Wata hanya da za a sanya bangarorin biyu zama teburin sulhu shi ne, janyo Amurka da China, da kasashe kamar Turkiyya su hada karfi da karfe domin magance matsalar, in ji Mista Nagy.

"Abiy ba zai iya kaucewa abin da Amurka da China suka gindaya ba."

Ya ce abu na farko da ya kamata a yi domin kawo karshen yakin shi ne kai kayan agaji, sai kuma a hankali a fara amfani da tattaunawar siyasa.

Akan me ake yin yakin?

Ya samo asali ne kan rashin daidaituwa tsakanin firaiminista Abiy da kungiyar TPLF, wadda kusan shekaru 27 suka mamaye madafun ikon kasar Habasha tare da mai da yankin Tigray saniyar ware.

A shekarar 2018 ne Mista Abiy ya zama firaiministan Habasha, bayan zanga-zangar da kabilar Oromo suka yi.

Da ma Oromo sun dade suna jan ragmar kasar, inda shi kansa Mista Abiy dan kabilar Oromo ne, kuma yana daga cikin kawancen da ke jan ragamar kasar, da kuma ake yi wa kallon wanda zai kawo karshen rikicin da ke shinfide a kasar.

A kokarin kawo sauyi, wanda yake amfani da siyasa da wanzar da zaman lafiya da dadaddiyar alaka da makwabciyar kasar Eritrea, sai yakin Tigray ya ga an ware shi gefe guda.

Shekara daya ta da gabata ne rashin jituwa ya fito fili tsakanin Mista Abiy da 'yan tawayen kungiyar 'yantar da yankin Tigray TPFL, inda yaki ya barke tsakaninsu.

An dai zargi 'yan tawayen Tigray da kai hari kan sansanin sojin gwamnati tare da sace makamai, don haka gwamnatin Habasha ta mayar da martani, lamarin ya kara kazancewa tare da janyo tashin hankalin da har yanzu ya ki ci ya ki cinyewa.