Sauyin yanayi: Yaya rayuwa take a wajen da yake da zafin da ya kai 50C?

A yanzu matsalar sauyin yanayi ta zamo ba abar damuwa ba. A wasu sassa na duniya tuni aka fara fuskantar matsalar.
Shekarar 2021 ita ce shekarar da aka fi fuskantar tsananin zafi. Miliyoyin mutane na rayuwa cikin matsanancin zafi, inda suke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa ko kuma wutar daji. A nan, wasu mutane biyar sun yi bayani a kan yadda tsananin zafi ya sauyawa musu rayuwa.

'Mun fuskancin rashin bacci'

Shakeela Bano, tana yi wa iyalanta shimfida a saman rufin gidansu mai hawa daya a India. A wasu daren ana yin tsananin zafin da ba za a iya kwanciya a cikin daki ba.Ta ce shi kansa saman gidan nasu da suke kwanciya da daddare wani lokacin ko tafiya akai ba za ka iya ba, gaskiya a wasu daren ma ko bacci ba sa iya yi.
Shakeela na zaune ne tare da mijinta da 'yarsu da kuma jikokinsu uku a dakin da babu taga a garin Ahmedbad. Fanka daya ce suke amfani da ita.
Sauyin yanayi na nufin cewa birane a India na da zafin da ya kai ma'aunin celcius 50.
A gidaje kamar na Shakeela, a yanzu zafin da suke dashi ya kai ma'aunin celcius 46C. Jiri kan debe ta a lokacin zafi. Jikokinta kuwa na fama da kurajen gumi a wasu lokutan ma har gudawa suke saboda zafi.
A gargajiyance, hanyoyin da ake bi wajen rage jin zafi kamar shan madara mai sanyi da kuma ruwa da lemon tsami yanzu duk ba sa aiki. A maimakon haka suna ranto kudi su yi wa gidajensu farin fenti saboda yana rage zafi.
A cewar Shakeela, akwai dama idan suka yi haka, saboda dakin na yin sanyi sannan kuma yara na yin bacci sosai.Ta nuna daya daga ciin jikokinta da ta ce baya iya bacci da rana, amma a yanzu yana bacci.

'Zafi kamar wuta'

"Ina zaune wajen da yake akwai zafi," Sidi Fadoua ya fada. To amma kuma zafin da ake a arewacin Mauritania da ke yammacin Afirka, a yanzu mutane na shan wuya wajen tafiyar da rayuwa da ma aiki a irin wannan yanayin. Ya ce zafin da ake a nan ya wuce hankali.
Sidi, mai shekara 44, na zaune a wani karamin kauye da ke kusa sahara.Yana aiki a wata mahakar gishiri da ke kusa da wasu rukunin gidaje. Aikin na da wuya, a yanzu ya kara wuya saboda yadda ake fama da tsanain zafi a yankin saboda sauyin yanayi. Ya ce ba za a su iya rayuwa a wannan yanayi ba, don su ba injina ba ne.
Domin kaucewa aiki a cikin wannan yanayi na zafi, Sidi ya fara aikin dare.
A yayin da Sidi ke kara samun mutanen da ke makwabtaka da shi, a yanzu ya yanke shawarar komawa birnin Nouadhibou da ke gabar teku inda zai rinka samun iska mai dadi.
A wannan birnin, Sidi na fatan samun aiki a ma'aikatar sarrafa kifi.

'Yaya za a kawar da gobaba?'

Patrick Michell, shi ne shugaban yankin Kanaka Bar First Nation, ya fara ganin sauyi a wani gandun daji yankinsa da ke Colombiar Birtaniya da kuma Canada fiye da shekaru 30 da suka gabata. Akwai rashin wadattacen ruwa a koguna wajen.
A wannan yanyi na zafi, abin da yake fargaba akai ya zama gaskiya. A samu tsanani zafi a arewacin Amurka. A ranar 29 ga watan Yunin 2021, zafin da aka yi a garinsa ya kai ma'aunin celcius 49C. A washe gari matarsa ta tura masa hoton da ya nuna zafin da aka yi a garin a ranar ya kai 53C, jim kadan da tura masa wannan hoton sai gobara ta tashi a garin.
'Yarsa, Serena, tana da juna biyu na wata takwas, ta hada sauran 'ya'yanta da kuma karensu suka bar gidan da suke.Ta ce."Mun bar gidan tare da kayanmu, wutar da ta tashi ta ba mu tsoro sosai".
Patrick, ya yi kokari ya koma gida don ganin ko zai iya ceto gidansu, amma ina lamarin ya canja saboda sauyin yanayi ya ce wannan wutar dajin ta koma gobara.

' A lokacin nake karama, lamarin ba haka yake ba'

" A lokacin da nake karama yanayin ba haka yake ba", in ji Joy, wadda take rayuwa a yankin Niger Delta a Najeriya. Yankin na daya daga cikin yanki mafi gurbacewar muhallaji a duniya, sannan kuma a kullum zafi na karuwa dare da rana.
Joy na na amfani da wannan zafin wajen yin tafiyoka ta sayar a kasuwa.Ta ce," ba ni da tsawon gashi, saboda idan na bari gashina ya yi tsawo zai iya konewa saboda tsananin zafi".
Sauyin yanayi a nan na mana babbar illa, saboda abubuwa ba sa tafiya yadda ake so, in ji Joy.

'Wannan zafin ba na lafiya ba ne'

Shekaru shida da suka wuce, Om Naief, ta fara shuka bishiya a wani waje. Ma'aikaciya ce da ta yi ritaya a Kuwait, ta damu da karuwar yanayin zafin da ake samu.
Ta ce," Na yi magana da wasu jami'ai, sun ceabu ne mai wuya a yi shuka a kan kasa".Ta ce kasar saboda tsananin zafi ba iya yin komai. Ina son yin wani abu da zai taimaka wa Kowa, in ji ta.
Om, wadda ke rayuwa a yankin gabas ta tsakiya, inda ake samun tsananin zafi ba zata iya jurewa wannan yanyi ba.A kan samu zafin ya kai 50C.
Mazauna yankin dai na ganin cewa zafin da ake fama da shi a yanzu ba na lafiya ba ne.

Hotunan da ke sama na Getty Images ne. Su kuma bidiyo kan sauyin yanayi sn same su ne daga Farfesa Ed Hawkins da Jami'ar Reading.













