Endsars:'Yan Najeriya na tunawa da harbe-harben Lekki shekara ɗaya da zanga-zangar

'Yan Najeriya da dama suna ta bayyana ra'ayoyinsu kan shekara ɗaya bayan zanga-zangar ƙin jinin rundunar ƴan sandan da ke yaƙi da fashi da makami na Sars.
A shekarar 2020 ne ƴan ƙasar da dama musamman daga kudanci suka shafe makonni suna gudanar da zanga-zangar a wasu manyan biranen ƙasar, sai dai sun yi ta samun turjiya daga ɓangaren jami'an tsaro.
A shafin matambayi ba ya ɓata na Google, kalmar Endsars ita ce ta biyu da aka fi dubawa a ranar Laraba 20 ga watan Oktoban 2021, sannan a shafin Tuwita ma an ƙaddamar da maudu'in #EndSARSMemorial wato #TunawadaEndsars wanda aka yi amfani da shi sau fiye da 500,000 da safe.
A hannu guda kuma, masu fafutuka sun ce za su yi watsi da gargaɗin da hukumomi suka yi musu tare da ƙaddamar da gangami a biranen da ke faɗin ƙasar, don tunawa da ranar da suka ce jami'an tsaro sun yi amfani da ƙarfi wajen murƙushe zanga-zangar.
Ranar Laraba 20 ga watan Oktoban 2021 ne aka cika shekara ɗaya cif da dakarun tsaro suka far wa masu zanga-zanga a dandalin Lekki Toll gate, inda aka zarge su da buɗe wa mutane wuta da kashe wasu da dama.
Masu fafutuka sun ce an kashe mutum 12, duk da cewa dai masu zanga-zangar da jami'an tsaro sun yi ta musu a kan ainihin abin da ya faru.
Sai dai a yayin da masu fafutuka suka dage kan cewa za su sake zama a dandalin lekki don tunawa da wannan rana, ita kuma rundunar ƴan sandan jihar Legas ta ce ta haramta duk wani tattaki tare da cewa taruka a killace a cikin wani waje ne kawai abin da aka yarda da su.
Amma duk da wannan gargaɗi, bidiyon da suka karaɗe shafukan sada zumunta a ranar Laraban sun nuna yadda mutane ke ta taruwa a dandalin Lekki da nufin jimamin abin da ya faru a baran.
Me mutane ke cewa?
Maudu'ai na ta tashe a shafin Tuwita kamar su #EndSARSMemorial da #LekkiMassacre2020 da #RestInPeace duk don tunawa da ranar.
Yawanci mutane a Tuwita suna jajantawa ne ga wadanda suka rasa rayukansu, wasu kuma suna tuna abin da suka kira muguntar ƴan sandan, wasu kuwa na tunawa da fin ƙrfin da suka ce jami'an tsaro sun nuna musu a yayin zanga-zangar.
Ga dai abin da wasu ke cewa a shafin:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
EiE Nigeria @EiENigeria ya ce: "Idan muna so abin ya wuce, dole mu tuna baya. Ta haka muke samun waraka. Hakan yana da muhimmanci a matsayinmu na ƙsa.
"Allah Ya ji kan 'yan uwa da abokan arziki da suka rasa rayukansu sakamakon cin zarafin da ƴan sanda ke yi. Muna yi wa waɗanda har yanzu suka shan wahala addu'a da kuma wadanda suka rasa danginsu. #EndSARS #EndSARSMemorial."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
ENISA @IAmENISA ta ce: "Shekara ɗaya kenan tun bayan fafutukar EndSars, ji nake kamar jiya abin ya faru. Sai dai abin takaici ne idan na tuna da mutanen da suka rasa rayukansu da ba su ji ba ba su gani ba, a wajen neman haƙƙoiƙinsu na ƴan adam. Ba za mutaɓa mantawa ba." #EndSARSMemorial #EndSARS
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Wannan kuwa wallafa hotunan wasu daga cikin waɗanda suka mutu ya yi yana cewa: "Allah Ya ji ƙanku gwarazanmu."
Karin wasu labaran masu alaka
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International a ranar Larabar ta ce har yanzu babu wanda aka gurfanar a gaban ƙuliya kan azabtarwa da tashin hankalu da kashe-kashen masu zanga-zangar.
Ta kuma har yanzu ana ci gaba da samun rahotannin cin zarafain da ƴan sanda ke yi a faɗin ƙasar.

Mene ne Endsars?
#Endsars wani maudu'i ne da ya yi ta tashe bayan da matasa suka mamaye tituna a watan Oktoban 2020 don nuna adawa da cin zarafin da rundunar ƴan sanda ta musamman mai yaƙi da fashi da makami ta SARS ke yi wa mutane a Najeriya.
An fara zanga-zangar ne ranar 8 ga watan Oktoban 2020 cikin lumana inda aka shafe kwanaki ana yi, amma daga baya ƴan daba sun ƙwace ragamar zanga-zangar inda suka fara lalata gibe-ginen gwamnati da na ƴan kasuwa afadin ƙasar.
Ƙungiyar Amnesty international ta ce an kashe fiye da mutum 50 yayin zanga-zangar. Ita ma ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Human right watch ta ce a ƙalla mutum 15 aka harbe ranar 20 ga watan Oktoban 2020 a dandalin Lekki tollgate a Lagos.

Me ya faru a dandalin Lekki toll gate?

Asalin hoton, Getty Images
Daya daga cikin manyan abubuwan da suka faru a zanga-zangar Endsar shi ne zargin harbin kan mai uwa da wabi da sojojin Najeriya suka yi wa masu zanga-zangar da ba sa ɗauke da makamai a dandalin Lekki tollgate, wajen da suka mayar da shi sansaninsu tsawon kwanaki.
Wasu masu zanga-zanga sun yi ikirarin cewa an kashe mutane da dandalin, amma gwamnatin Najeriya ta ce babu wanda ya mutu. Ministan yaɗa labarai Lai Muhammed a lokacin ya ce 'ta yaya za a yi kisan kiyashi ba tare da ganin gawa ko ɗaya ba..
Rundunar sojin Najeriya ta amince cewa ta yi harbe-harbe a dandalin Lekki a yayin zanga-zangar, amma ta ce "da harsasan roba aka yi harbin kuma babu wanda aka kashe."
A ranar 20 ga watan Oktoban 2021 wasu ƴan Najeriyar sun sake taruwa a dandalin don tunawa da waɗanda suka ce an kashen, wasu kuma suna nasu juyayin ne a shafukan sada zumunta.

Me masu zanga-zangar ke son cimma?

Asalin hoton, Getty Images
Masu zanga-zangar sun bazama kan tituna ne suna so gwamnati ta haramta rundunar ƴan sanda ta musamman me yaƙi da fashi da makami ta SARS.
Suna zargin SARS da cin zarafin matasa ba gaira ba dalili, suna karɓar wayoyinmu mutane da ƙarfi da kuma karɓar kuɗaɗe daga wajensu.
Matasan sun ɗauki kwalaye suna waƙe-waƙen nuna ɓacin rai. Sun ziyarci ofisoshin gwamnoni a gadin ƙasar don miƙa ƙorafe-ƙorafensu da kuma buƙatar neman sauyi.
Sun tare ƙofar shiga dandalin Lekki a Legas suka ce ababen hawa ba za su wuce ba sai gwamnati ta masa buƙatarsu.
Matasa sun kuma tare wurare da dama a faɗin Najeriya kamar a jihohin Abuja da Imo da sauransu.
Daga baya kwalliya ta biya kuɗin sabulu kan batun don kuwa Shugaba Buhari ya bayar da umarnin soke rundunar SARS ba tare da ɓata lokaci ba.

Yadda ƴan daba suka ƙwace ragamar zanga-zangar Endsars
Zanga-zangar ta rikiɗe zuwa rikici a yayin da ƴan daba suka shiga cikinta. Sun fara kai hari ofisoshin ƴan sanda da kan dukiyoyin mutane.
Bayanan ƴan sanda sun nuna cewa an kai hari kan ofisoshin ƴan sanda fiye da 100. Hukumomin ƴan sanda sun ce an kashe jami'ansu da dama a harin da ƴan daban suka dinga kai wa.
Jami'an tsaro sun far wa masu zanga-zangar inda suka kama da yawansu.
A wasu wuraren kuma mutane sun yi amfani da damar zanga-zangar suka dinga wawaso a rumbunan abinci na gwamnati da na ƴan kasuwa.
Bidiyo da hotuna sun yaɗu sosai da ke nuna mutane na kwasar abin da suka kira "ganima."

Ko an daina cin zarafin mutane da ake zargin ƴan sanda na yi?
Duk da cewa gwamnati ta ji koken matasan ta soke rundunar SARS, har aynzu akwai rahotannin cewa ana ci gaba da samun cin zarafin da ƴan sanda ke yi wa mutane a faɗin ƙasar.
A ranar Asabar 16 ga watan Oktoban 2021 ma wani bidiyo ya yaɗu a shafukan sada zumunta da ke nuna wani ɗan sanda ya mari wani matashi a jihar Kogi.
Rahotanni sun ce tawagar da ɗan sanda ke ciki sun kuma karɓi naira 25,00 daga wani mutum a wajen da ƙarfin tuwo.
Sufeto Janar na ƴan sanda ya bayar da umarnin yin bincike kan lamarin tare da da kama ɗan sandan.
Amma har yanzu ƴan Najeriya suna ƙorafi kan yadda har yanzu ƴan sanda ke karɓar kuɗi daga wajen mutane da ƙarfin tuwo, yayin da wasu kuma ke ƙwace wayar mutane suna bincike a ciki.













