Babban wakilin Amurka a Afghanistan zai sauka daga muƙaminsa

Asalin hoton, Getty Images
Manzo na musamman da Amurka ta aika Afghanistan zai sauka daga muƙaminsa ƙasa da wata biyu bayan Amurkar ta janye daga ƙasar.
Zalmay Khalilzad ne ya jagoranci tattaunawa tsakanin Amurka da Taliban sai dai bayan kasa cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu bayan shafe watanni ana tattaunawa, sai Taliban ɗin ta ƙwace iko da Afghanistan ɗin.
Taliban ɗin ta ƙwace ƙasar baki ɗaya bayan samun nasarar ƙwace babban birnin ƙasar Kabul.
Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya sanar da cewa mataimakin Mista Khalilzad, Thomas West ne zai karɓi muƙamin.
"Zan miƙa saƙon godiya gareshi bayan shekarun da ya shafe yana yi wa Amurkawa aiki," in ji Mista Blinken a wata sanarwa da ya fitar wadda ke nuni da murabus ɗin Mista Khalilzad a ranar Litinin.
A wata wasiƙa da ya aika wa Mista Blinken, Mista Khalilzad ya fito fili ya bayyana cewa ba a samu wani ci gaba da aka yi hasashen za a samu ba a tattaunawar siyasa da aka yi tsakanin Amurka da Taliban.
Ya kuma bayyana cewa dalilan da suka sa hakan na da girma matuƙa inda ya ce nan da makonni zai bayyana ra'ayinsa kan dalilan.
A wasiƙar da ya aika, ya ce zai sauka ne sakamakon sabon tsarin da Amurka ta ɗauka tsakaninta da Afghanistan inda ya kuma ce bai ji daɗin halin da mutanen Afghanistan suka shiga ciki ba a halin yanzu.
Mista Khalilzad mai shekara 70, an haife shi a Afghanistan inda ya girma a Kabul. Ya shahara wajen diflomasiyya inda ya riƙe muƙamai a lokacin tsofaffin shugabannin Amurka da suka haɗa da mulkin Donald Trump da Barack Obama da George W Bush.
Shi ya jagoranci tattaunawar da aka yi tsakanin Taliban da Amurka har aka saka hannu kan wata yarjejeniya da ake kira Doha Agreement wadda aka cimma a Fabrairun bara, wadda a cikin yarjejeniyar ne a saka ranar da dakarun Amurka za su janye daga Afghanistan.
Ko a watan da ya gabata sai dai jami'ai a Amurka suka ƙara tunar da cewa ƙwace ikon da Taliban ta yi na da alaƙa da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ɓangarorin biyu.









