Ambaliyar ruwa ta hallaka mutum 26 a Indiya

Ambaliyar ta janyo katsewar hanyoyi sakamakon bishiyoyin da suka toshe tituna

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Sama da mutum 26 ne ambaliyar ruwa ta hallaka a kudancin Indiya, sakamakon ruwan saman da aka sheka kamar da bakin ƙwarya lamarin da ya janyo toshewar hanyoyi a wasu garuwan da ƙauyuka.

Gidaje da dama ruwan ya yi awon gaba da su, yayin da mutane suka maƙale a Kottayam da ke jihar Kerala.

Hotunan bidiyo da aka dauko sun nuna yadda aka kubutar da wasu mutane da ke cikin motar bas, lokacin da direban ya gagara ci gaba da tafiya saboda ƙarfin ruwan.

An shafe kwanaki ana sheƙa ruwan sama a jihar Kerala, lamarin da ya haddasa zaftarewar kasa, kuma sojojin Indiya sun shiga aikin ceto.

Jami'ai sun ce a ranar Lahadi an yi amfani da jirage masu saukar ungulu domin kai wa wadanda ke bukatar taimako kayan agaji, sakamakon rashin hanyar mota.

A wani lamari mai sosa zuciya da kamfanin dillancin labarai PTI ya rawaito a gundumar Kottayam, wasu iyalai su shida ciki har da kakarsu mai shekara 75 da yara uku duka sun mutu, saboda babu ta inda za su gudu.

An kuma gano gawar wasu yara 'yan shekara 8 da 4 a ƙarƙashin ɓaraguzan gidansu a Idukki, an kuma ci gaba da neman wasu ƙarin biyar da ake kyautata zaton ruwa ya tafi da su.

A ɓangare guda kuma hukumomi na amfani da kwale-kwale domin aikin ceto, musamman a yankin Kollam da kogi ya yi ambaliya, babu hanyar mota sakamakon bishiyoyin da suka kakkarye tare da toshe hanyoyin.

Iyalai dai na ci gaba da neman 'yan uwansu, dan haka ne hukumomi ke cewa adadin wadanda suka mutu ka iya haura 20.

Ba safai ake samun ambaliyar ruwa mai karfi irin wannan a jihar Kerala ba.

Lokaci na karshe da aka samu ambaliyar ruwa mafi muni a jihar ta fuskanta cikin shekaru 100, shi ne shekarar 2018, inda mutum 400 suka mutu, sama da miliyan daya suka rasa muhallansu.