Yadda kudan zuma ke bin zuma haka jama'a ke bin Buhari - Adesina

Buhari a wajen kamfe

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Shugaba Muhammadu Buhari dan siyasa ne da yake da farin jini wanda ta kai 'yan kasar na binshi kamar yadda kudan zuma ke bin zuma domin so da kauna, wanda kusan a tarihin kasar a iya cewa ba wani dan siyasa da yake a raye ko wanda ya mutu da yake da wannan farin jini, in ji kakakin shugaban Mista Femi Adesina.

Kakakin ya yi wa shugaban wannan koɗa da yabo ne a wata maƙala da ya rubuta wadda ya saba yi a duk mako, wadda kuma kamar maimaici ne na irin kalaman da mataimakin shugaban, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi a lokacin da yake jawabi ga jami'an diflomasiyya a ofishin jakadancin Najeriyar a London, a makon da ya gabata.

Mista Adesina ya ce yadda mutane ke tururuwa domin halartar duk inda Shugaba Buhari yake, ko fitattun ƴan siyasa irin su Dr Nnamdi Azikiwe da Cif Obafemi Awolowo da Mallam Aminu Kano ba su kai shi ba, duk kuwa da cewa har shugabanni ne da suka yi farin jini tare da bauta wa Najeriya, da suke da magoya baya da har yanzu ake martaba su.

Makalar ta Adesina wadda kusan tambihi ne na bayanan da Farrfesa Osinbajo ya yi na yabo da koda Buhari, ya ce duk kalaman da mataimakin ya yi a wancan jawabi na London haka suke, domin mataimakin shi ma mutum ne mai gaskiya;

"Mataimakin Shugban Kasa Yemi Osinbajo mutum ne mai gaskiya. Duk abin da ya gaya ma, ka dauke shi da muhimmanci. Kai za ma ka iya daukar shi ka je banki, domin chakin banki ne da ba za a taba kin karba ba," in ji kakakin.

Ya kara da cewa, "A iya cewa; daman me za a yi tsammanin ji daga bakin mutum na biyu a kan maigidansa? Ba zai soke shi a cikin jama'a ba, saboda kila zai bukaci goyon bayansa a nan gaba wajen neman mukamin shugaban kasa, zai fadi dadadan abubuwa a kansa."

Ya yi bayanin cewa e lalle haka ne amma fa ga dan siyasa da yake da buri. ''To amma ga mu da muke aiki tare da shugabannin biyu, mun san cewa Farfesa Yemi Osinbajo ba irin wadannan 'yan siyasr ba ne.

"Mutum ne mai gaskiya, mai ƙeƙe da ƙeƙe , wanda ke dogaro ga Ubangiji a kan duk wani abu. Ba abin da yake dauka a mutu ko ai rai, saboda haka zai iya zabar ya yi shiru da bakinsa a kan dabi'un Shugaban, don ka da a yi masa wata fassara ta daban," in ji shi

"Da ya ce Buhari kusan shi ne dan siyasa mafi farin jini a tarihi, na yarda, ba wai kawai da jin hakan da kunne ba, a'a domin na gani da idona."

Buhari da mukarrabansa

Asalin hoton, Buhari Sallau

Kakakin ya ce shekarunsa sun kai ya ga ƴan siyasa iri daban-daban a zamaninsu.

Ya ce ya ga mai girma Obafemi Awolowo da gwani mai muhibba Nnamdi Azikiwe da Shehu Shagari da Aminu Kano da M.K.O Abiola da Bashir Tofa, da sauransu da dama, amma bai ga wanda ya ke da irin kwarjini da farin jinin jama'a ba, kamar Muhammadu Buhari

Ya ce kuma duka wadannan a fadin kasar ne kama daga, kudu da arewa. Mutane na binsa kamar yadda kudan zuma ke bin zuma.

Wannan layi ne

'Babu wani shugaba a Najeriya da ya taɓa samun farin jinin Buhari'

Mista Adesina ya ce ya kewaya ko ina fadin Najeriya da Shugaban. Kuma ya je kasashen waje da yawa tare da shi, saboda haka bai ga wani shugaban Najeriya na da ko na yanzu ba da yake da farin jini da kwarjini na irin na Buhari ba.

Ya ce wannan shi ne dalilin da yake ganin idan mataimakin Buharin ya bayyana shugaban da cewa kusan shi ne dan siyasa mafi farin jini da aka taba samu a kasar a zamanin nan, ba za a ce ya yi kuskure ba.

Mista Adesina ya jaddada maganarsa da bayar da misalin yadda jama'a suka yi tururuwa domin tarbar shugaban lokacin da ya dawo daga tafiyar da ya yi wadda ya fi dadewa domin jinya a London.

Ya ce a wannan rana ta 27 ga watan Agusta saboda cikar dan adam da ababana hawa sai da ta dauke su kusan linki biyu ko uku na lokacin da ya kamata su dauka daga filin jirgin sama kafin su isa fadar shugaban kasa.

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Wannan layi ne