Shin me ake sa rai Buhari zai yi bayan duba ƙwazon ministocinsa?

Buhari da Osinbajo

Asalin hoton, Buhari Sallau

An wallafa

Bayan da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya fara gwada ƙwazon ministoci da sauran manyan muƙarrabban gwamnatinsa ƴan ƙasar da dama na zuba ido da sauraren abin da zai iya biyo baya.

A ranar Litinin ne 11 ga watan Oktoba 2021 Shugaban ya ƙaddamar da taron kwana biyu na karatun-ta-natsu wanda ministoci da manyan sakatarori da sauran manyan muƙarraban gwamnatin ke halarta domin bibiyar ayyukan gwamnatin a tsakiyar wa'adin mulkinsa na biyu.

Duk da cewa gwamnatin Shugaban a yayin buɗe taron ta ce ministocinta sun cimma kimanin kashi 60 cikin 100 na manufofi guda 9 da ta tsara ayyuka da shirye-shiryen da take aiwatar wa 'yan ƙasar, akwai hasashen cewa wasu ministocin ka iya rasa muƙamansu bayan kammala taron a dalilin rashin bayar da gamsasshen sakamako na ayyukansu.

Idan dai ba a manta ba, a wata hira da BBC ta yi da kakakin Shugaba Buharin, Mallam Garba Shehu a watan Satumba, bayan cire Alhaji Sabo Nanono daga muƙamin ministan ayyukan gona da kuma Alhaji Saleh Mamman na ma'aikatar makamashi, kakakin ya ce matakin ''somin taɓi'' ne.

Tsoffin ministocin biyu wadanda shugaban ƙasar ya raba da aiki bisa abin da gwamnatin ta ce gazawa, su ne na farko da ya taɓa sauƙewa tun lokacin da ya kama mulki a 2015.

Haka kuma bayan ƙaddamar da taron na yanzu wanda za a kammala Talatar nan, a hira da BBC, kakakin gwamnatin, Mallam Garba Shehu ya ce, shugaban ƙasar wanda ke halartar karon da kansa, zai yanke hukuncin abin da zai biyo baya.

Kakakin ya yi matashiya cewa tun a lokacin da Buhari zai ƙaddamar da majalisar ministocin ya yi musu bayanin cewa zai ba su ayyukan da yake so a yi, wanda ya yi da kyau zai gani wanda ma bai yi ba zai gani.

A don haka ya ce yanzu za a saurara ne a ga matakin da shugaban zai ɗauka a kan ministocin kasancewar shi ne yake da wuƙa da nama a hannunsa.

A baya Shugaba Buhari yakan halarci irin wannan taro ne na bibiyar ayyukan ministocin nasa a lokacin buɗewa kawai, to amma saɓanin haka a wannan karon yana halarta inda ake komai a gabansa.

Gwamnatin ta ce ƙwararru ne daga ciki da wajen Najeriya suka tantance ayyukan ministocin bisa manufofi guda 9 da suka dace da alƙawurran da shugaban ya ɗaukar wa al'umma, wanda a bisa wannan doro ne zai yanke hukunci kan makomar kowa ne minista.

Wannan layi ne

Bayanan Shugaba Buhari a wurin buɗe taron

A jawabinsa na ƙaddamar da taron ranar Litinin shugaban ya gargaɗi dukkanin ministocin da manyan sakatarori da su ɗauki batutuwan da suka shafi aiwatar da ayyukan da aka ɗora musu na cimma muradu da manufofin gwamnatin da muhimmanci.

Shugaban ya ce dalilin taron bibiya da duba ƙwazon ministocin shi ne, domin a gano inda ak samu rauni domin a gyara ta yadda gwamnati za ta iya cimma burin ƴan ƙasar ta Najeriya.

"Shekara biyu da ƴan watanni a wa'adinmu na biyu, tsarinmu na gabatar da ayyukanmu da shirye-shiryemu domin nazari daga wata kafa mai zaman kanta da mu kanmu abu ne da ya kama tushe, ta hanyar bayar da rahotanni na ɓangarori a lokacin taron ministoci da sauran taruka," in ji Buhari.

Ya ce wannan tsari ya ba su damar bibiya da nazarin ayyukan ma'aikatun a shekara biyu da ta gabata wajen aiwatar da alƙawuran da aka yi wa ƴan Najeeriya.

Haka kuma a yayin taron Shugaba Buhari ya gabatar da tsarin sanin lura da yadda ake gudanar da ayyukan da gwamnati ta fi bai wa fifiko.

Ya ce wannan tsari wanda aka fra amfani da shi tun watan Janairu na wannan shekara, ya ba shi damar bibiya da sanya ido a kan ayyuka a zahiri kai tsaye da cikakkun bayanai.

Wannan layi ne