Sakon Shugaba Buhari ga ƴan Najeriya kan cikar ƙasar shekara 61 da samun ƴanci

Nigeria at 61

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

An wallafa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ranar 1 ga watan Oktoban 2021 ba ta bikin murnar cika shekara 61 da samun 'yancin kan kasar daga Turawan Mulkin Mallaka ba ce kawai, har ma da murnar haɗa kan ƴan ƙasar daga ƙabilu da addinai da yankuna daban-daban.

Ya bayyana hakan ne a jawabinsa na murnar cikar Najeriya shekara 61 da samun ƴanci a ranar Juma'a, inda ya ce har yanzu akwai ƴan ƙasar da wannan rana ke da muhimmanci a wajensu.

"Kyakkyawan fata da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da nasarar Najeriya da ƴan ƙasar ke nunawa ce suka sa take ci gaba da kasancewa dunƙulalliya," in ji shugaban.

Ga dai muhimman batutuwan da ya faɗa a jawabin nasa:

1. Ya ku ƴan Najeriya, wata 18 ɗin da suka gabata sun kasance daga cikin mafiya wahala a tarihin Najeriya. Tun bayan yaƙin basasa, ina tababar idan mun ga wani lokaci da aka samu ƙaruwar ƙalubale kamar irin wanda muke gani a yanzu.

2. Shugaban ya yi doguwar magana kan yadda annobar cutar korona ta yi tasiri a kan abubuwa da yawa a ƙasar.

"Shirinmu na ainihi mafi muhimmanci da muka tsara yi a shekarar 2020 shi ne ci gaba da farfaɗo da tattalin arziƙi daga matsin da ya shiga da kuma magance matsalolin tsaro a yankunan da ke fama da hakan.

"Sai mummunan tasiri da annobar cutar korona ta yi ya sa muka sauya salo da sake manufofi."

Nigeria at 61

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

3. Ƴan Najeriya sun haɗa kai wajen yaƙar cutar COVID-19. Hakan ce ta sa cikin yardar Allah muka fi ƙarfin wannan annobar.

"Bala'in da aka yi hasashen cewa ƙasar za ta gani har yau ba mu gan shi ba. Ko nau'in Delta na cutar koronan da ke ci gaba da yaɗuwa, mun samar da matakan kariya a yanzu da nan gaba," in ji shugaban.

Daga nan sai ya yi kira ga ƴan ƙasar da kar su yi ganganci wajen ƙin ci gaba da ɗaukar matakan kariya daga cutar. Yana mai cewa duk da dai gwamnati na nata ƙoƙari, to su ma sai sun taimaka.

4. Shugaba Buhari ya kuma yi magana a kan yadda ake ci gaba da fama da samun wadatar riga-kafin cutar korona a duniya, ya ce gwamnatin Najeriya na duba dukkan hanyoyin da suka kamata don samar wa ƴan ƙasar sahihin riga-kafin.

Ya ce tuni aka yi amfani da riga-kafi miliyan biyar ga ƴan Najeriya kuma za a cin gaba da sayen su.

5. "Tuni na bai wa Ma'aikatun Kuɗi da na Kasafi da Lafiya da Ilimi da Kimiyya da Fasaha umarnin yin aiki tare da kamfanonin harhaɗa magunguna na cikin gida da na ƙasashen waje da ƙungiyoyin bincike don bunƙasa harkar samar da magunguna a ƙasar."

Shugaban ƙasar ya ce tuni Hukumar Zuba Jari ta Najeriya ta fara haɗa dala miliyan 200 kan wannan shiri na bunƙasa harkokin samar da magani a ƙasar.

6. Shugaban ƙasa ya ce "a yayin da tattalin arziƙinmu ke ci gaba da farfaɗowa bayan saka dokokin kullen cutar korona, sai kuma matsalar rashin tsaro ke ta'azzara a wasu sassan ƙasar."

Amma ya ƙara da cewa "a wata huɗun da suka gabata, zaƙaƙuran sojoji da jami'an tsaronmu sun samu gagarumar nasara wajen magance waɗannan sabbin matsalolin tsaron. Amma muna ci gaba da yaƙar maƙiyan namu kuma muna samun nasara."

Nigeria at 61

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

7. A farkon shekarar nan Buhari ya ce ya ƙaddamar da tsarin tabbatar da tsaron hanyoyin ruwa na bai ɗaya, mai taken Deep Blue Project, waɗanda aka tsara don samar da tsaro a hanyoyin ruwa na Najeriya har zuwa mashigar Tekun Guinea.

"Ina farin cikin sanar da ƴan Najeriya cewa an kawo mana muhimman kayan aikin wannan shirin, kuma kwanan nan za a ga tasirinsa," ya ce.

8. Ya kuma yi magana kan miƙa wuyan da mayaƙan Boko Haram ke yi a arewa maso gabashin Najeriya.

9. Don ƙarfafa yaƙi da ƴan bindiga, shugaban ƙasar ya ce Rundunar Sojin Najeriya ta ɗauki ƙarin jami'ai fiye da 17,000 a muƙamai daban-daban.

"Sannan na ba da umarnin ƙarin ɗaukar sabbin jami'an ƴan sanda 10,000 duk shekara har nan da shekara shida.

"Kuma ina farin cikin sanar da ku cewa dukkan kayan yaƙi na rundunar sojin saman da muka saya shekara uku da suka gabata sun fara isowa Najeriya. Hakan zai taimaka sosai a ayyukan tsaronmu a dukkan sassan ƙasar."

10. Shugaban ƙasar ya yi amfani da damar da ya kira ta ranar haɗin kan ƙasar, ya nemi ƴan Najeriyar su dinga bin hanyoyin sasanci na zaman lafiya don warware rigingimunsu.

"Kamar yadda yake a sashe na 14(2)(b) na kundin mulki, tsaro da walwalar ƴan Najeriya za su ci gaba da kasancewa muhimman al'amuran gwamnati.

"Don haka a matsayinmu na gwamnati, a shirye muke mu gurfunar da dukkan masu son haddasa rikici a baki ko a aikace. Muradinmu na samar da dunƙulalliyar ƙasa ba zai tashi a banza ba.

"Fatanmu ba shi ne mu yi yaƙi don samar da zaman lafiya ba. Ko yaushe muna iya warware rigingimunmu cikin lumana ba tare da zubar da jini ba."

Buhari

Asalin hoton, BBC/Buhari Sallau

11. Buhari ya ce Najeriya ta kowa ce kuma ba za su bari a wargaza haɗin kanta ba.

"Za mu ci gaba da amfani da matakan sasanci don warware matsalolin. Amma a shirye muke don ɗaukar matakai a kan masu fafutukar ɓallewa da masu ɗaukar nauyinsu da ke yi wa tsaron ƙasarmu barazana.

"Kama Nnamdi Kanu da Sunday Adeyemo a kwanan nan da kuma binciken da muke yi, ya gano wasu mutane da ke ɗaukar nauyin hakan. Muna nan muna bin diddigin masu ɗaukar nauyin, ciki har da wani ɗan majalisar dokokin ƙasar mai ci a yanzu.

"Ya ku ƴan Najeriya, wannan na nuni da yadda mutane ke yin watsi da muƙamansu na shugabanci don son kai. Maimakon yin kira ga haɗin kai, sai suke ɗaukar nauyi da sa matasanmu a hanyar da ba ta dace ba, da a wasu lokutan ke jawo asarar rayuka da ta dukiyoyi.

"A yayin da masu kiran kansu shugabannin fafutukar ke guduwa Turai su ɓuya, a nan kuma ana zuga matasanmu suna kashe kawunansu a kan tituna kan shirme.

"Don haka gwamnati za ta ci gaba da haɗa kai da abokan hulɗarmu na ƙasa da ƙasa wajen inganta tsaro, da kuma daina bai wa miyagu mafakar da za su dinga zama don ɗaukar nauyin ta'addanci.

Nigeria at 61

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

12. Shugaban ya kuma yi magana kan dokar yi wa ɓangaren man fetir garanbawul inda har ya yaba wa majalisar dokoki kan rawar da ta taka, har ya yi magana kan gina manya da kananan matatun man fetur a jihohin Imo da Edo da Akwa-Ibom da kuma Legas.

13. Ya taɓo batun harkar noma a matsayin ƙoƙarin faɗaɗa bunƙasar tattalin arziƙi, inda ya ce an samu zuba jari a kusan dukkan harkokin noma.

"Sai dai kash, a yayin da samar da abincinmu ya ƙaru, farashin kayayyakin abinci kuma sai ya tashi saboda ƙarancin abincin da wasu suka ƙirƙira da gangan, waɗanda suke ɓoye shi.

"Don magance wannan matsala, a yanzu ina bai wa Ma'aikatar Noma da Raya Karkara umarnin gyara Hukumar Kula da Rumbunan Abinci ta ƙasa su kuma yi aiki da hukumomin tsaro, da Majalisar Dokoku don gano mafita ta dindindin kan ayyukan waɗannan marasa kishin ƙasar.

14. Shugaba Buhari ya taɓo batutuwan samar da kayayyakin more rayuwa kamar gyaran manyan tituna da ake yi a ƙasar da samar da ingantaccen ruwan sha da samar da fasahar 5G da ciyar da ƴan makaranta da ayyukan N-Power.

Nigeria at 61

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

15. Kan batun shafukan sada zumunta ma Buhari ya bayyana yadda miliyoyin ƴan Najeriya ke amfani da su don zumunci da danginsu da abokan arziki da harkokin kasuwanci da samun bayanai kan abubuwa da labarai.

Amma ya ce wasu na amfani da su wajen aikata miyagun laifuka da yaɗa labaran ƙarya da ta da rikicin addini da ƙabilanci. Shugaban ya ce a don haka ne ma ya dakatar da amfani da tuwita a ƙasar a watan Yunin 2021.

"Daga baya Tuwita ya tuntuɓe mu don warware taƙddamar. Ni kuma na kafa kwamitin shugaban ƙasa don tattauna wa da kamfanin. Kwamitin ya tattauna da tuwita kan batutuwa kamar:

a. Tsaron ƙasa da haɗin kaion;

b. Yin rijista da buɗe ofishi da sanya wakilci;

c. Ta biya haraji;

d. Ta dinga warware taƙaddama.

e. Mutanen ƙasa su dinga amfana da ita.

16. Buhari ya sha alwashin bai wa matasa damar a dama da su a siyasa da damawa da su a sauran ɓangarori na ci gaban ƙasar.

17. Ya taɓo batun cin zarafi da fyaɗe da aka yi ta samun ƙaruwarsa a baya-bayan nan.

"A yanzu haka muna samar da Kotuna na musamman don a dinga gaggauta yin shari'ar da ta shafi fyaɗe da cin zarafi don tabbatar da adalci.

A ƙarshe shugaban ƙasar ya ce a yayin da Najeriya ke cika shekara 61, akwai buƙatar ƴan ƙasar su yi taka tsan-tsan cewar ba komai da ya shafi ƙasar ne ya dogara kacokan a kan gwamnatin tarayya ba.

"Wannan ƙasar akwai gagarumin haɗa hannu daga gwamnatoci a kowane mataki da kuma masu ruwa da tsaki da ƴan ƙsar kowa na da rawar da zai taka."