Liverpool za ta dauki Asensio, Barca na son daukar Sterling

Liverpool na duba yadda za ta iya dauakar Marco Asensio mai shekara 25, wanda ake jin baya jin dadin zama a Real Madrid. (Mirror)
Wadanda suka sayi Newcastle United sun ce za su mayar da kungiyar tamkar Manchester City da kuma Paris St-Germain, wadanda attajiran gabas ta tskiya suka mallaka. (Times - subscription required)
Tsohon kocin Chelsea, Frank Lampard da na Rangers, Steven Gerrard suna daga cikin wadanda ake cewar za sum aye gurbin mai horar da Newcastle, Steve Bruce, wanda ya ce yana fargabar zai rasa aikinsa. (Telegraph - subscription required)
A shirye Manchester City ta fara tattaunawa da Raheem Sterling, mai shekara 26, kan batun tsawaita kwantiraginsa, wand aba ta kaunar ya bar Etihad, wanda saura kasa da kaka daya da rabi yarjejeniyarsa ya kare. (Sun)
Ana alkanta cewar Barcelona na son daukar Sterling ita kuma Manchester City na yin a yi mata musaya da dan kwallon tawagar Faransa Ousmane Dembele. (El Nacional - in Spanish)
Juventus ta gindaya fam miliyan 25.4 kudin dan wasan tawagar Amurka Weston McKennie, mai shekara 23, ga duk wadda ke son daukarsa, bayan da ake cewa Tottenham na bibiyar dan kwallon. (Calcio Mercato - in Italian)
Liverpool ta yi wa Barcelona tayin Divock Origi idan tana bukatar dauka a watan Janairu. Mai shekara 26 dan kwallon tawagar Belgium wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar bana, baya buga wasanni sosai karkashin koci Jurgen Klopp. (The Sun)
Tatakila dan wasan tawagar Ingila, Harry Winks, mai shekara 25, zai koma taka leda Everton daga Tottenham a watan Janairu ko zai ke samun buga wasa akai-akai. (CaughtOffside)
Kungiyar Juventus da ta Inter na son daukar dan wasan Leicester, mai shekara 25, dan kwallon tawagar Belgium, Timothy Castagne. (Le Derniere Heure - in French)
AC Milan na son daukar dan kwallon tawagar Faransa, Samuel Umtiti, mai shekara 27, daga Barcelona a watan Janairu. (Calcio Mercato - in Italian)
Watakila dan kwallon tawagar Italiya mai taka leda a Torino, Andrea Belotti, mai shekara 27, ya bar kungiyar da ke buga gasar Serie A a bana, wanda kwantiraginsa zai kare a lokacin. (Fabrizio Romano)
Dan wasan Serbia, Dusan Vlahovic, mai shekara 21 da ke taka leda a Fiorentina da kuma dan wasan Paris St-Germain dan kasar Argentina, Mauro Icardi, mai shekara 28, suna daga cikin 'yan wasan da Juventu ke sa ido a kai. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Manchester United da kuma Chelsea na son daukar dan wasan Stoke City, Emre Tezgel, mai shekara 16. Itama Manchester City an ce za ta yi zawarcin matashin dan wasan. (Star)









