Luka Modric na kan ganiya a kwallon kafa duk da cika shekara 36

Asalin hoton, Getty Images
A watan jiya Luka Modric ya cika shekara 36 da haihuwa, sai dai dan wasan na ci gaba da jan zare a wasannin da yake yi wa Real Madrid.
Dan kwallon tawagar Crotia ya shiga cikin fitattun 'yan wasan da ke buga babbar gasar Sifaniya da suka yi karawa da dama duk da yawan shekarunsu.
Tun bayan da ya yi bikin cika shekara 35, 'yan kwallo biyar ne ke gabansa da suka buga wasa sama da 55, bayan da Modric ya cika shekara 35 cikin watan Satumbar 2020.
Mai buga wasannin tsakiya ya hau kan Amancio na Espanyol mai karawa 54, kuma wadanda ke gabansa sun hada da Gento mai wasa 69 da Miguel Angel mai fafatawa 93 da Alfredo Di Stefano mai gumurzu 99 da Ferenc Puskas mai wasa 120 da kuma Paco Buyo mai fafatawa 160.
Modric ya ci gaba da jan zarensa a Real Madrid wadda yake buga wa wasanni sosai a wannan lokacin duk da yawan shekarunsa.
Haka kuma a tawagar Croatia, Modric kashin bayan tawagar ne a kokarin da kasar ke yi na kai wa gasar cin kofin duniya a Qatar a 2022 a lokacin dan wasan zai cika shekara 37 da haihuwa.
Sai dai wasu na hangen da kyar ne idan jikin dan wasan zai iya jure wahalar tamaula zuwa babbar gasar kwallon kafa ta duniya.





