'Yan Super Eagles da suka sha kashi a hannun Jamhuriyar Afirka

Ahmed Musa

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Super Eagles ta yi rashin nasara a hannun Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da ci 1-0 a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da suka buga ranar Alhamis a Legas.

Wannan shine wasan farko da Najeriya ta yi rashin nasara a karawar rukuni na ukun, amma duk da haka ta ci gaba da jan ragama mai maki shida, bayan doke Liberia da Cape Verde.

Sai dai itama Cape Verde ta je ta ci Liberia 2-1 a daya fafatawar rukuni na uku a wasa na uku ranar ta Alhamis.

Najeriya za ta ziyarci Jamhuriyar Afirka ta tsakiya a wasa na biyu a tsakaninsu kuma na hudu a cikin rukuni na uku ranar 10 ga watan Oktoba, a kuma ranar ce Cape Verde za ta yi wa Liberia masauki.

Ita dai Jamhuriyar Afirka ta tsakiya na buga wasanninta a Kamaru a matsayin gida.

Cape Verde ce ta biyu mai maki hudu, itama Jamhuriyar Afirka ta tsakiya maki hudun ne da ita, sannan Liberia mai maki uku.

Cikin watan Maris za a ci gaba da jadawalin wasannin karshe domin fitar da wadanda za su wakilci Afirka a gasar kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci a 2022.

Tun kan wasan kocin Najeriya ya bayyana sunan kyaftin Ahmed Musa da mataimakinsa, Wlliam Ekong cikin wadanda za su kara a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2021.

Tawagar 'yan wasan Nigeria:

Masu tsaron raga: Francis Uzoho (AC Omonia, Cyprus); Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs, South Africa); Maduka Okoye (Sparta Rotterdam, The Netherlands)

Masu tsaron baya: Chidozie Awaziem (Alanyaspor FC, Turkey); Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Leon Balogun (Glasgow Rangers, Scotland); William Ekong (Watford FC, England); Olaoluwa Aina (Torino FC, Italy); Jamilu Collins (SC Padeborn 07, Germany); Abdullahi Shehu (AC Omonia, Cyprus); Calvin Ughelumba (Glasgow Rangers, Scotland); Kevin Akpoguma (TSG Hoffenheim, Germany)

Masu buga tsakiya: Frank Onyeka (Brentford FC, England); Joseph Ayodele-Aribo (Galsgow Rangers, Scotland); Innocent Bonke (Malmo FF, Sweden); Alex Iwobi (Everton FC, England); Kelechi Iheanacho (Leicester City, England)

Masu cin kwallo: Ahmed Musa (Fatih Karagumruk, Turkey); Samuel Kalu (FC Bordeaux, France); Victor Osimhen (Napoli FC, Italy); Moses Simon (FC Nantes, France); Paul Onuachu (KRC Genk, Belgium); Chidera Ejuke (CSKA Moscow, Russia)