Har yanzu Jadon Sancho bai nuna kansa a Premier ba

Asalin hoton, Reuters
Jadon Sancho bai nuna kansa a kakar bana ba kawo yanzu, bayan da ya koma taka leda Manchester United daga Borussia Dortmund.
Bayan da dan wasan tawagar Ingila ya taka rawar gani a Dortmund, an dauka zai nuna kwarewar da ya samu a gasar Bundesliga, sai dai kawo yanzu bai nuna kansa cikin fitattun 'yan wasan da ke fara buga wa United fafatawa ba.
Duk da cewar Marcus Rashford na jinya ba a fara wasannin bana da shi ba, Ole Gunnar Solskjaer na fara karawa da Sancho, tare kuma da Paul Pogba.
Rashin kokarinsa ya sa wasa biyu kacal aka fara yi da shi a Premier League kawo yanzu, kuma bai ci kwallo ba a matakinsa na dan wasan Manchester United.
A cewar masana darajar dan kwallon mai shekara 21 ta yi kasa daga Yuro miliyan 100 zuwa Yuro miliyan 90, tun bayan da ya koma Old Trafford.
Wasan da dan kwallon ya taka rawar gani shine wanda Manchester United ta doke Villareal 2-1 a Champions League, inda Solskjaer ya kara nanata cewar dan wasan na bukatar karin lokaci domin gasar Premier da ban take da ta Jamus.
Duk da cewar tawagar Ingila ta kira Sancho wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za ta fafata da Andorra da kuma Hungary a cikin watan Oktoba, Gareth Southgate ya ce dan wasan bai cancanci shiga tawagar ba, bayan da baya kan ganiyarsa a United.
Kocin ya ce dalilin da ya gayyaci dan kwallon United din, saboda yana cikin tsarin matasan Ingila da za su ja ragama nan gaba.









