Angela Merkel: Rayuwarta cikin hotuna

An wallafa

Angela Merkel na shirin sauka daga muƙaminta na shugabar gwamnatin Jamus bayan shekara 16 a mulki, kuma wannan ya kawo ƙarshen rayuwarta ta siyasa wadda ta kwashi tsawon shekaru 30.

Rayuwa ce da aka adana hotunanta a kowace gaɓa: daga kai wa masunta ziyara a farko-farkon kamfe ɗinta zuwa tattaunawa da Fadar White House da sauransu.

A nan, mun tattaro kaɗan daga cikin dubban hotunan matar wadda ta ɗaɗe a fagen siyasar Jamus.

Angela Merkel (CDU), German Chancellor, feeds Australian lorises at Marlow Bird Park and gets bitten, 23 September 2021, Mecklenburg-Western Pomerania, Marlow

Asalin hoton, DPA/Alamy

Bayanan hoto, 23 Satumba 2021: Wa'adin Misis Merkel ta fuskanci faɗi tashi amma za a tuna yadda ta fuskanci matsaloli cikin dabara
A photo taken in 1989 in the northern Polish city of Bachotek shows (from L) now quantum chemistry professor Malgorzata Jeziorska, Joachim Sauer, the husband of German Chancellor Angela Merkel, and the German leader during summer school at a university for chemistry students.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Bazarar 1989: Misis Merkel (a can dama) da Malgorzata Jeziorska da mijin da ta aura Joachim Sauer a wata jami'a a Poland
Election campaign, visiting a fisherman's hut in Lobbe on the island of Ruegen, Mecklenburg-Vorpommern in November 1990

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nuwamba 1990: Zuwa shekarar da ta biyo baya, ta fara kamfe a babban zaɓen Jamus na farko da aka gudanar tun bayan da ƙasar ta koma cikakkiya
Merkel, Angela - Politician, CDU, Germany, Federal Minister for the Environment, Germany - ironing wrapping paper - 1994

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Janairu 1994: An naɗa Misis Merkel Ministar Muhalli
Angela MERKEL , CDU , Minister for the Environment , and Horst SEEHOFER , CSU , Minister for Public Health , during a cabinet meeting in March 1995

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Maris 1995: Misis Merkel na dariya tare da Minista Horst Seehofer a yayin wani taron ministoci
Angela Merkel sits a covered seat on the beach

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Maris 2000: An zaɓi Misis Merkel ta jagoranci jam'iyyar Christian Democrats (CDU) a 2000
Angela Merkel, head of the opposition Christian Democrats, the CDU, speaks at the Lower Saxony Christian Democratic Party's annual general meeting on July 9, 2005 in Emden, Germany

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yuli 2005: Bayan shekara biyar, ta koma kamfe - wanda zai kai ta ga nasarar zama mace ta farko da za ta zama Shugabar Gwamnatin Jamus
Italian Prime minister Romano Prodi, French President Nicolas Sarkozy (hidden), US President George W. Bush, German Chancellor Angela Merkel, Russian President Vladimir Putin and British Prime Minister Tony Blair share a laugh as they take position for a family picture with other G8 leaders,

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yuni 2007: Duk da cewa ƙarni na 21 ne, maza ne suka mamaye fagen siyasa, don haka Misis Merkel - a wannan hoton da Firai Ministan Italiya Romano Prodi da Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, shugaban Amurka George W Bush da shugaban Rasha Vladimir Putin da Firai Ministan Burtaniya Tony Blair- sau da yawa ita kaɗai ce mace a cikinsu
German Chancellor Angela Merkel (L) and Peter Mueller, federal prime minister of the Saar region and top candidate of the of the conservative Christian Democratic Union party (CDU) for the upcoming Saarland state election, hold glasses of beer during an election campaign rally in Bosen near Saarbruecken August 15, 2009

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Afrilu 2009: Misis Merkel ta zama wata alama ta tattalin kuɗin gwamnati a shekarun da suka biyo bayan matsin tattalin arziƙi
US Secretary of State Hillary Clinton (L) and German Chancellor Angela Merkel address the press after a meeting at the Federal Chancellery in Berlin, on April 14, 2011.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Afrilu 2011: Hillary Clinton, lokacin tana Sakatariyar Harkokin ƙasashen wajen Amurka da Misis Merkel a Berlin
Angela Merkel spreads her arms wide while talking to then US President Barack Obama in June 2015, against a dramatic mountain backdrop in southern Germany.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yuni 2015: Misis Merkel tare da shugaban Amurka na wancan lokacin Barack Obama, bayan wani taron ƙoli na G7 a kudancin Jamus. "Ka zama amintaccen abokina tun hawana mulki - fiye da duk wani shugaban duniya," ta shaida wa shugaban na Amurka bayan shekara guda
A migrant girl holds a poster of German Chancellor Angela Merkel as migrants walk in Budapest downtown after leaving the transit zone of the main train station, on September 4, 2015

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, September 2015: The chancellor's decision to open Germany's borders to refugees in 2015 divided the country. Pictured: Refugees making their way through Hungary
U.S. President Donald Trump (R) and German Chancellor Angela Merkel (L) participate in a joint news conference at the East Room of the White House

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Afrilun 2018: Matakin ya sa sun raba gari da shugaban Amurka Donald Trump
In this photo provided by the German Government Press Office (BPA), German Chancellor Angela Merkel deliberates with US president Donald Trump on the sidelines of the official agenda on the second day of the G7 summit on June 9, 2018 in Charlevoix, Canada, looked on by other leaders.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yunin 2018: Ba batun 'yan gudun hijira ne kawai ya janyo matsala ba. Koriya Ta Arewa da Iran da cinikayya na cikin batutuwan da suka janyo ire-iren wannan yanayin a wannan taron na G7 a Canada
Ugur Sahin, founder and CEO of the biotechnology company BioNTech shows German Chancellor Angela Merkel dummy ampoules of the BioNTech/Pfizer COVID-19 vaccine during her visit to the BioNTech Vaccine Production Plant on August 19, 2021 in Marburg, Germany.

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, 2020/21: A dai-dai lokacin da annobar korona ke ci gaba da ya yaɗuwa a faɗin duniya, Misis Merkel ta sha yabo kan yadda ta tafi da annobar: wasu sun ce iliminta na kimiyya ya taimaka

Duka hotunan, ban da waɗanda aka alamta na AFP ne ko na Getty Images