Bidiyon sojar da ta sheƙa wa ƴar NYSC ruwan datti ya janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya

Asalin hoton, OTHERS
Wani hoton bidiyo da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ya nuna wata soja mace tana ɗebo ruwa mai datti daga wani bokiti tana kwara wa wata mace da ke durƙushe kan guiwowinta tana sanye da kayan masu yi wa ƙasa hidima a Najeriya, ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar.
Rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwa kuma ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a birnin Calabar na jihar Cross River, sannan ta yi Alla-wadai da ɗabi'ar sojar wadda rundunar ta ce ta saɓa wa dokokinta na kyawawan dabi'u.
Haka kuma rundunar ta ce ta ƙaddamar da bincike kan lamarin kuma an ɗauki mataki kan sojar sannan za a hukunta ta yadda ya dace.
Sannan ta bai wa matar mai yi wa ƙasa hidimar haƙuri kan tozarta ta da aka yi.
Tuni dai lamarin ya dauki hankalin masu amfani da shafuka sada zumunta, sannan suka fara muhawara kan rashin dacewar dabi'ar sojan.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1

Karshen labarin da aka sa a X, 2
Wani mai amfani da shafin Twitter ya bayyana cewa a ganinsa kama sojan bai wadatar ba saboda "al'adar rundunar soja ce haka kuma haka aka koya mata.
Matsalar daga mutanen da ke sama ne," a cewarsa.

Asalin hoton, FACEBOOK/Icon Nixon Chukwuka Odimbu
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Ita ma wannan mai amfani da shafin Twitter mai suna @doctorfolu ta ce "ko me zai sa mace ta yi wa wani ɗan Adam irin haka."
Ta ce lokaci ya yi da za a san abin da ake ciki kan al'adar amfani da karfin iko a Najeriya.
Ta kuma ce ya kamata mu gyara halinmu a Najeriya.
Babu karin bayanai
Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.Karshen labarin da aka sa a Facebook, 1
Johnvianney Chinedu na shafin Facebook kuwa cewa ya yi ɓacin ransa shi ne da alama sojar da mai yi wa kasar hidima sun fito ne daga yanki guda, idan aka yi la'akari da sunayensu.
Ma'ana bai dace sojar ta wulaƙanta matar ba tunda a iya cewa ɓangarensu ɗaya.
Babu karin bayanai
Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.Karshen labarin da aka sa a Facebook, 2
Haka shi ma Abdullahi Jampeck Muhammed a shafin Facebook ya ce "mace ce maƙiyar mace."
"A Najeriya muna da wuce gona da iri wurin amfani da ikon da muke da shi.
"Da zarar mutane sun samu wani ɗan iko sai su yi amfani da shi don biyan buƙatar kansu."
Wasu rahotanni na cewa tuni aka kama sojar kafin a kammala bincike kuma hukumomi sun ɗauke matar da aka ci zarafi daga sansanin da ke birnin na Calabar.
Ƴan Najeriya da dama dai na ta kira da a bi wa matar haƙƙinta kuma a biya ta diyyar tozarcin da aka yi mata.