Al'ummar Yemen na fuskantar barazanar yunwa

Al'ummar Yemen
An wallafa

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gaggauta taimakawa miliyoyin al'ummar kasar Yemen wadanda ke fuskantar barazanar yunwa.

Shugaban shirin, David Beasley, ya bayyana halin da ake ciki a Yemen bayan shafe fiye da shekara shida ana yaki a matsayin mummuna.

Daga nan ya yi gargadin cewa irin kayayyakin da suke taimakawa kasashe da su sun kusa karewa.

Kudaden tallafin da kasashen duniya suka hadawa Yemen a yanzu bai kai abin da aka yi hasashen tarawa ba domin dala biliyan biyu da miliyan dari biyar ne kadai aka iya tarawa.

Yaki tsakanin dakarun Saudiya da ke goyon bayan gwamnatin kasar da kuma 'yan tawayen Houthi wadanda ke da alaka da Iran ya dai-dai ta kasar.

Mr Davida ya ce, mun sani cewa idan aka dai na shigar da kaya, tattalin arzikin kasa kan tabu haka kuma farashin kaya ma na tashi, ya ce, a yanzu farashin kayan abinci da na man fetir sun tashi a Yemen.

A don haka dole ne 'yan kasar da damansu su fukanci barazanar yunwa.

Shirin samar da abincin ya ce a yanzu ana bukatar goyon bayan al'ummar Yemen da kuma tallafi daga kasashen duniya domin taimakawa mutanen da ba su ji ba su gani ba da yaki ya rutsa dasu a Yemen.