Cacar baki ta barke tsakanin shugabannin Taliban a fadar gwamnati

Abdul Ghani

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Wata gagarumar cacar-baki ta barke a tsakanin shugabannin Taliban, kwanaki kadan bayan da suka kafa sabuwar gwamnati a Afghanistan, kamar yadda wasu manyan jami'ai suka shaida wa BBC.

Magoya bayan bangarorin biyu masu fada da juna sun bai wa hammata iska a cikin fadar shugaban kasa a Kabul, babban birnin kasar.

Cacar bakin ta kaure ne a kan batun wanda ya fi taka rawa wajen samun nasarar dawo da gwamnatin Taliban da yin nasara a kan Amurka, da kuma yadda karfin mulki ke raba kan majalisar zartarwar gwamnatin.

Amma Taliban ta yi watsi da rahotanni a hukumance.

Kungiyar ta kwace iko da Afghanistan ne a watan da ya gabata, kuma tun a sannan ta ayyana kasar a matsayin "Daular Musulunci".

Sabuwar gwamnatin ta maza ce zalla kuma ta hada da manyan 'yan Tliban din, wadanda wasun su sun yi kaurin suna kan hare-haren da suka kai wa dakarun Amurka cikin shekara 20 da suka gabata.

Rikicin ya samo asali ne bayan wani jigo a Taliban Mullah Abdul Ghani Baradar, ya bace daga shii=ga hidimar gwamnatin tsawon kwanaki.

Wata majiya ta shaida wa BBC Pashto cewa Mr Baradar da Khalil ur-Rahman Haqqani - minsitan 'yan gudun hijira kuma wani jigo a rundunar Haqqani - sun yi musayar yawu a yayin da magoya bayansu suka bai wa hammata iska a kusa da wajen.

Wani babban jami'i na Taliban da ke zaune a Qatar kuma mutumin da ke da alaka da wadanda lamarin ya shafa ya tabbatar da cewa an yi wata 'yar hatsaniya a makon da ya gabata.

Majiyoyin sun ce rikicin ya barke ne saboda Mista Baradar, sabon mataimakin firaiminista, bai ji dadin yadda aka tsara shugabancin gwamnatin rikon kwaryar ba.

Sannan kuma wasu rahotanni sun ce an samu sabanin ra'ayi kan wa za a jinjina wa a Taliban kan nasarar da aka samu ta kwace mulki a Afghanistan.

Rahotanni sun ce Mr Baradar ya yi amannar cewa shi ya kamata a dinga yabawa kan dabarun diflomasiyya da ya bi, yayin da mambobin rundunar Haqqani - suka ce an samu nasarar ne ta hanyar yakin da suka jagoranta.

Mr Baradar ne shugaban Taliban na farko da ya yi magana kai tsaye da shugaban kasar Amurka, lokacin da ya yi waya da Donald Trump a shekarar 2020. Kafin sannan, ya sanya hannu kan yarjejeniyar janye dakarun Amurka a madadin Taliban.

Taswirar shugabancin Taliban

Rundunar Haqqani dai ana alakanta ta da hare-hare mafi muni da aka taba kai wa a Afghanistan kan dakarun gwamnatin kasar na baya da kuma na kawayensu kasashen yamma a shekarun baya-bayan nan. Amurka ta ayyana rundunar a matsayin kungiyar ta'addanci.

Shugaban rundunar Sirajuddin Haqqani, shi ne ministan harkokin cikin gida na sabuwar gwamnatin.

Tun a makon da ya gabata ake yada jita-jitar, bayan da aka kwana biyu ba a ji duriyar Mista Baradar ba. An yi ta rade-radi a shafukan sada zumunta cewa watakila ya mutu.

Majiyoyin na Taliban sun shaida wa BBC cewa Mista Baradar ya bar Kabul ya je birnin Kandahar bayan cacar bakin.

A wani sakon murya da aka nada da cewa ta Mista Baradar ce a ranar Litnin, an ji jigon na Taliban yana cewa ya yi wani bulaguro ne.

"Muna nan lafiya a duk inda nake a wannan lokacin," in ji shi.

Sai dai BBC ta kasa tabbatar da sakon muryar, wanda aka wallafa a shafukan intanet na Taliban da dama.