Taliban ta sanar da kafa sabuwar gwamnati a Afghanistan

Asalin hoton, Alamy
Taliban ta sanar da kafa gwamnatin rikn kwarya a Afghanistan, sannan a ayyana kasar a matsayin "Daular Musulunci".
Mullah Mohammad Hassan Akhund, wanda yana daya daga cikin mutanen da suka kafa kungiya, shi ne zai jagoranci gwamnatin.
Shugaban kungiyar Haqqani wanda hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI take nema ruwa a jallo shi ne ministan harkokin cikin gida.
Taliban ta kwace ikon kasar fiye da mako uku da suka gabata, inda suka kori gwamnatin da aka zaba.
Sanar da majalisar zartarwar ta rikon kwarya wani babban bangare ne na kafa gwamnatin Taliban.
"Mun san cewa 'yan kasarmu sun dade sun jiran sabuwar gwamnati," a cewar mai magana da yawun gwamnatin Zabihullah Mujahid, yana mai cewa kungiyar ta amsa kiran jama'arta.
Sarajuddin Haqqani, sabon ministan riko na harkokin gida, shi ne shugaban kungiyar 'yan bindiga ta Haqqani wadda ke da alaka da Taliban kuma shi ne ya kitsa wasu daga cikin hare-hare mafiya muni da aka kwashe fiye da shekaru 20 ana kai wa a kasar.
Amurka ta ayyana Haqqani a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Sauran nade-naden da aka yi sun hada da Mullah Yaqoob a matsayin ministan tsaro na riko, Amir Khan Muttaqi a matsayin ministan harkokin waje na riko, da kuma wasu daga cikin wadanda suka kafa Taliban Mullah Abdul Ghani Baradar da Mullah Abdul Salam Hanafi a matsayin mataimaka biyu.
Yaqoob ɗa ne ga mutumin da ya kafa Taliban kuma shugabanta Mullah Omar. A baya Baradar ya taba riko ofishin harkokin siyasar Taliban, kuma a shekarar da ta gabata shi ne ya jagoranci kulla yarjejeniyar janyewar dakarun Amurka daga kasar.
Da aka tambaye shi abin da ya sa ba a saka mata a cikin gwamnati ba, Ahmadullah Wasiq, daga Hukumar Kula Da Al'adu ta Taliban, ya shaida wa dan jaridar BBC Secunder Kermani cewa ba a gama sanar da sunayen ministocin ba.










