Matar da ta ceto dubban mata daga cin zarafi a gidan aure

Asalin hoton, AGNES SITHOLE
- Marubuci, Daga Sandrine Lungumbu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
Agnes Sithole ta zama wata jaruma ga dubban mata baƙaƙen fata a Afrika Ta Kudu. Tana da shekara 72, ta kai mijinta ƙara a kotu don a hana shi sayar da gidansu ba da izininta ba - kuma ana cikin haka ta ƙalubalanci tsoffin dokokin wariyar launin fata ta yi nasarar hana sayar da gidansu.
'Da ban ƙalubalance shi ba sai dai na ƙare a titi'
Tun daga farko, Agnes ta san rayuwar aurenta za ta yi wahala. Ta auri Gideon, saurayinta tun suna makarantar sakandire a 1972, amma ba a jima ba ta tsinci kanta tana kawar da kai kan neman mata masu zaman kansu da yake yi tsawon shekaru.
"Kullum yana cikin tarayya da wasu matan kuma abin bai taɓa shafa ta ba sai tsakanin shekarun 2016 da 2017 lokacin da ya nemi sayar da kadararmu," a cewarta.
"Kullum maganarsa ɗaya ce - wai gidansa ne, dukiyarsa ce, kuma ni ba ni da komai."
Da ta fuskanci za ta rasa muhallinta, a shekarar 2019 Agnes ta yanke shawarar yin shari'a da mijinta a kotun Afrika Ta Kudu, wani mataki da ba a cika ganin mata baƙar fata masu shekarunta suna dauka ba.
"Shekaruna 72 a lokacin - ina zan je kuma ta ina zan fara? Don haka ba ni da wani zaɓi illa na yaƙe shi ko kuma na ƙare a kan titi da shekarun nan nawa.
"Ina tunanin rashin wani zaɓin ne ya ba ni ƙwarin gwuiwa. Da ina da wani zaɓi da ba zan yi haka ba. Dole na na zamo wata da za ta ce a'a, ba zai yiwu ba."
'Mace ba ta da zaɓi'

Asalin hoton, AGNES SITHOLE
Agnes ta yi aure a lokacin da mata baƙar fata a Afrika ta Kudu ke aure ƙarƙashin tsarin da ake kira "out of community property" wanda ke bai wa maza ƴancin mallakar duk wata dukiya a gidan a matsayinsa na shugaban ahalin.
"A baya, mata ba su da zaɓi - ko dai ta yi aure ƙarƙashin wannan tsarin ko kuma kada ta yi auren gaba ɗaya," a cewar Agnes.
Wata kwaskwarima da aka yi wa dokar aure a 1988 ta bai wa mata da miji baƙar fata damar sauya tsarin aurensu inda za su samu daidaito a ƴncin mallakar dukiya.
Sai dai ba haka kawai take aiki ba - dole ne mata baƙar fata su samu amincewar mazajensu sannan su biya kuɗin shigar da neman dama kuma su shigar da neman damar duk cikin shekara biyu.
"Mun san cewa dokar ta sauya," a cewar Agnes. "Daga baya da na fahimci dokar da yaudare ni sai na fahimci dole na yaƙe ta."

Asalin hoton, AGNES SITHOLE
An haifi Agnes a Vryheid, wani ƙaramin gari da ake haƙar kwal a arewacin KwaZulu-Natal.
A faɗin ƙasar, akwai rashin daidaito a fannin tattalin arziƙi tsakanin farar fata da baƙar fata a shekarun 1940 kuma mahaifinta mai sharar jiragen ƙasa ne a kamfanin jiragen ƙasa na Afrika Ta Kudu sannan yana haɗa wa shugabannin kamfanin farare shayi a ofis, yayin da mahaifiyarta kuma tana wanke-wanke da shara da girki a gidan fararen fata masu arziƙi.
"An haife ni cikin matsanancin talauci, iyayena leburori ne. Sun yi mana tarbiyya mai kyau kuma na yi koyi da halayyarsu," in ji Agnes.
"Muna zuwa coci duk ƙarshen mako. Lokacin da nake girma, ba a bari ƴan Katolika su yi sakin aure, ko da kuwa zaman ba daɗi.
"Ba na so na yi wani auren ko kuma yarana su girma ba tare da duka iyayensu biyu tare ba."
'Ni mai neman na kaina ce'

Asalin hoton, AGNES SITHOLE
Duk da waɗannan ƙalubale, Agnes ta ga iyayenta sun zauna tare kuma sun yi fafutuka tare sai ta sa wa ranta ita ma za ta gina rayuwa mai kyau.
Ta koyi aikin jinya kafin ta auri Gideon, sannan daga baya ta fara sayar da tufafi daga gida kuma ta yi wasu ayyukan duk don a samu na sa wa a bakin salati.
"Nan da nan na fahimci ba ni da kowa, saboda mijina yau yana nan gobe baya nan," a cewar Agnes wadda ta haifa masa yara huɗu.
"Zan dawo gida daga wurin aiki, in fara ɗinki da sayar da kaya. Na riƙa yin abubuwa da dama a lokaci guda saboda na ƙudiri aniyar ƴaƴana za su makaranta.
"Ni mai neman na kaina ce dama. Tun da nake ina da neman na kaina. Na san cewa ba sai na dogara kan namiji ba saboda na gane cewa ba ni da kowa don haka maimakon faɗa da wani don ya yi min abubuwa na gwammaci in yi da kain."

Asalin hoton, AGNES SITHOLE
Ga Agnes, aurensu ya zo gangara ne shekaru tara da suka gabata. Bayan ta dawo daga wurin aiki a wani yammaci, ta samu Gideon ya tattara kayansa ya koma wani ɗaki na daban ba tare da yi mata bayani ba kuma bai sake komawa ɗakin barcinsu ba.
Sun ci gaba da zama a gida ɗaya amma kowa na gudanar da rayuwarsa daban.
"Za mu gamu da juna a cikin gida ko a kan bene ko a wurin ajiye mota kuma babu wanda zai ce uffan," a cewarta.
Agnes ta ce Gideon bai taɓa yi mata maganar shirinsa na sayar da gidansu ba kuma "abin mamaki sai kawai mutane suka riƙa afkowa cikin gidana wai sun zo ganin gida".
Da ta fahimci tana iya ƙarewa bisa titi, a farkon 2019 ta shiga da ƙara a kotu inda ta ce ta bayar da gudumuwa daidai da nasa a cikin iyalinsu don haka arziƙin nasu ne daidai wa daida.
Babu nadama

Asalin hoton, AGNES SITHOLE
Bayan shekarar biyu - a Afrilun 2021- Kotun Afrika Ta Kudu ta yanke hukuncin cewa dokokin da ake da su sun nuna wariya kan baƙaken fata musamman ma mata.
Ta yanke hukuncin cewa za a sauya duka aurarrakin da aka yi kafin 1988.
Agnes da ƴar autarta sun kalli yanke hukuncin ta intanet. Da farko ba ta fahimci cewa ta yi nasara a kotu ba sai da lauyanta ya kira ta.
"Ba mu fahimci abin da ke faruwa ba saboda kalaman shari'a masu wahalar ganewa," ta ce. "Don haka mun kasance a cikin duhu. Cikina ya ƙulle, na tsorata amma na yi imani.
"Na yi kukan farin ciki. A nan na fahimci na ceto dubban mata kamar ni daga aurensu."
Agnes ta ce tana da jajircewa ne duba da manyan ƙalubalen da ta fuskanta ita kaɗai.
"Halina ne da kuma yadda nake yin abubuwa, Ina son cin gashin kaina a ko wane fanni," ta ce. "Lallai ne ba a saba ganin haka ba a al'adarmu kuma daga mata masu shekaruna.
"A ganina, wannan nasarar na ɗaya daga cikin abubuwan farin ciki da suka taɓa faruwa da ni saboda nasarata na nufin nasarar kowa da kowa.
"Ban taɓa yin tantama kan matakina ba, na gaya wa kaina, "Zan tabbatar na jajirce kan wannan lamari ko na yi nasara ko ban yi ba'."
Yafiya

Asalin hoton, AGNES SITHOLE
Agnes ta yafe wa Gideon, wanda ya rasu dalilin cutar korona lokacin da ake shari'ar.
Kwanaki biyu kafin rasuwarsa, ya bai wa matarsa da ƴaƴansa mata haƙuri kan yadda abubuwa suka gudana.
Daga baya Agnes ta gano ashe bai sa ta a wasiyyarsa ba kuma ya bar wasiyyar a bau wa wani daban gadon gidansu. Sai dai hukuncin kotu a soke duka wadannan bukatun nasa.
"Na san cewa abin ba dadi amma wani lokaci yadda abubuwa ke zuwa karshe ya fi yadda suka kasance muhimmanci, a cewar Agnes. Na ceto dubban mata daga irin aurena'
"Mun yafe masa kuma yanzu na samu natsuwa. Bana nadamar komai kuma na tsaya tsayin daka kan aurena har karshensa.
"Babu wani abu nasa da nake so amma shi ya so ya kwace komai, ciki har da abinda na mallaka da gumina kuma wannan shi ne abin da raina bai amince da shi ba."











