Ƴansanda sun kama mutum 6 da ake zargi da garkuwa da mutane a Kaduna

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar Ƴansandan Jihar Kaduna ta ce ta kama mutum shida da ake zargi da garkuwa da mutane, tare da lalata maboyarsu a kauyen Dogon Pako da ke ƙaramar hukumar Ikara.
Rundunar ta ce an kama mutanen ne ranar Talata bayan wani da ake zargin an yi garkuwa da shi ya tsere daga hannun masu garkuwa da shi, sannan ya ba ƴansanda bayanai kan inda aka tsare shi.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan ya fitar, ya ce wanda abin ya shafa ya yi wa ƴansandan cikakken bayanin gidan wani Ja’e Samalu mai shekara 65, inda aka ce an tsare shi.
Bayan samun bayanan, jami’an ƴansanda tare da haɗin gwiwar jami’an sa-kai sun kai samame gidan, inda suka kama Ja’e Samalu, Abdul-Aziz Musa mai shekara 35 wanda aka fi sani da “Kire”, Jafar Isah mai shekara 25, Yunusa Musa mai shekara 22, Shu’aibu Musa mai shekara 20 da Rakiya Samalu mai shekara 50.
Rundunar ta ce ana zargin Rakiya mahaifiyar wasu daga cikin waɗanda aka kama kuma ita ke kula da wanda aka yi garkuwa da shi.
Ƴansandan sun ce waɗanda ake zargin suna hannunsu yayin da ake ci gaba da bincike domin gano irin rawar da kowannensu ya taka da kuma kamo sauran waɗanda ake zargin suna cikin tawagar.




























